Zaɓen Amurka na 2020: Waɗanne abubuwa Trump ya faɗa a kan muhalli?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Christopher Giles
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
A daidai lokacin da wutar daji ta fara ci a wasu ƙasasashen yamma da kuma guguwar ruwa da iska da ta far wa kudancin gaɓar tekun Amurka, Shugaba Trump na Amurka ya jawo ce-ce-ku-ce kan kimiyyar da ke tattare da sauyin yanayi.
A dai lokacin, ya kira kansa wani "babban masanin muhalli," inda ya ce ya samu nasara wurin kula da dazukan Amurka da namun daji da kuma haramta wasu haƙe-haƙe da ake yi a doron ƙasar Amurka.
Mun duba wasu abubuwan da shugaban ya faɗa kuma ya yi kan wasu matsaloli da ke tattare da muhalli.
Trump: 'Za a fara sanyi. Ku tsaya ku gani...ba na tunanin an san haka a kimiyance.'
Mista Trump ya sha caccaka daga masana kimiyya kan wannan lamari.
Dakta Chris Brieley, wanda farfesa ne kan nazarin kimiyar muhalli, ya bayyana cewa duniya na fuskantar zafi, kuma za a ci gaba da fuskantar zafin.
"Ana samun wasu shekaru masu tsananin zafi, haka ma ana samun wasu shekaru masu tsananin sanyi, amma a yanzu abin na ƙaruwa", in ji shi.
Kuma ana samun ƙarin zafi mai tsanani, kuma ayyukan ɗan adam ne ke jawo hakan.
Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka ta bayyana cewa: "Bincike da dama da aka gudanar sun nuna cewa kashi 97 cikin 100 ko kuma sama da haka na masana muhalli kuma marubuta sun yi ittifaƙin cewa wasu abubuwan da bil adama ke yi ne ke kawo wannan sauyin yanayin."
Sai dai shugaban ya nuna halin ko in kula ta ɓangaren shawo kan wannan matsalar, inda ko a shekarar da ta gabata sai da shugaban ya cire Amurka daga wata yarjejeniya da aka cimma a Paris, wadda yarjejeniya ce ta yadda ƙasshe za su shawo kan matsalar ɗumamar yanayi.
Trump: A yanzu, muna da iskar shaƙa mafi tsafta da ba a taɓa samu a ƙasar ba, mu ce sama da shekaru 40.'

Asalin hoton, Getty Images
Amma ko da waɗannan nasarorin sun samo asali ne daga matakan da Trump ke ɗauka ko kuma daɗewar da aka yi da ba a amfani da makamashin gawayi, duka wasu lamura ne da masana ke nuna shakku a kai.
"Matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na samar da iska mai nagarta na nuna aniyarsa ta ƙara gurɓata iskar da ake shaƙa nan gaba," in ji H Christopher Frey, wani farfesa a Jami'ar Carolina.
Trump: Mu ƙanana ne a batun gurɓata muhalli. Su suka fi gurɓata muhalli
Shugaba Trump ya bayyana haka ne a wani martani da ya mayar wa China da India da Rasha a ƙoƙarinsa na nuna cewa Amurka ba ta bayar da wata gudunmawar a zo a gani ta fuskar gurɓata muhalli.

"Babu mai magana kan wannan lamari," in ji shi.
Amma Amurka ce ta fi kowace ƙasa fitar da sinadarin carbon dioxide a duk duniya, bayan China.
Kuma idan kuka duba abin da duk mutum guda ke fitarwa, ya fi na abin da sauran ƙasashen da Trump ya lissafo.
Trump: 'Ina ƙoƙarin ganin cewa Amurka ta samar da ruwa mafi tsafta a duniya.'
An ɗora Amurka a matsayin ta 26 a duniya, ta ɓangaren tsafta da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha, kamar yadda wani bincike da Jami'ar Yale ta wallafa a 2020.
A cikin waɗannan ƙasashe, Finland da Iceland da Netherlands da Norway da Switzerland da Birtaniya su suka fi ruwa mai tsafta.

Asalin hoton, Getty Images
Trump: 'Na sa hannu kan kudirin dokar nan ta kula da dazuka'
Majalisar Tarayya ta Amurka ta amince da dala biliyan 9.5 domin kula da gandun daji a shekaru biyar masu zuwa.
Kudirin, wanda duka 'yan jam'iyyun Democrats da Republican suka sa wa hannu zai ƙaru da dala miliyan 900 na shekara guda domin kula da ruwa da dazuka wanda aka ƙirƙira a 1965.
A baya dai Shugaba Trump ya nuna goyon bayansa wajen rage kashe kudi ta hanyar kula da dazuka, sai dai a sauya ra'ayinsa a wannan karon inda ya sa hannu kan dokar.

Asalin hoton, Getty Images











