Zaɓen Amurka na 2020: Ko Trump ya cika alƙawarin da ya yi wa sojoji?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Christopher Giles
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
Shgaban Amurka Donald Trump ya sha kare yadda yake kashe kuɗaɗe kan rundunar soji tare da shan alwashin fitar da Amurka daga shiga sha'anin yaƙe-yaƙen ƙasashen duniya.
A shekarar 2017 ya ce zai sake inganta rundunar sojin ƙasar ''wacce yawan dakarunta ya ragu''. Ya kuma yi kira ga a rage yawan dakarun Amurka da ke aiki a wasu ƙasashen.
A wannan maƙala, BBC ta yi duba kan ayyukan shugaban a harkar soji.

A baya-bayan nan ɗan shugaba Trump, Donald Jr ya wallafa saƙo a Tuwita cewa: "Trump yana kashe wa rundunar sojin ƙasarmu kuɗi yadda ya kamata bayan da Obama da Biden suka gaza yin hakan."
Taswira ta nuna yadda kuɗaɗen da ake kashe wa rundunar sojin suka dinga ƙaruwa tun bayan hawan Shugaba Trump mulki a watan Janairun 2017.
Sai dai duk da haka kashe kuɗaɗen bai kai na wa'adin farko na mulkin Obama ba,
To sai dai, kudaden da aka kashe a wa'adin farko na mulkin Obama ba su da yawa, idan aka yi amfani da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki.
"Kuɗaɗen da ake kashewa a harkar tsaro ya ƙaru sosai a ƙarƙashin mulkin Trump har zuwa yau. ''Sai dai ba zan iya cewa ƙaruwar irin wacce ba a taɓa samu ba ce,'' in ji Michael O'Hanlon, wani masanin harkar tsaro a Cibiyar Brookings.
"Shugaba Trump zai iya da'awar cewa an ya kara kudaden da ake kashewa a lokacinsa, duk da cewa a lokacin Obama ma abinda ake kashewa din sun wadatar, inda kasafin kiudin bangaren tsaro yake da gwabi idan aka dubi tarihi - fiye da dala biliyan 100 da ake ringa kashewa duk shekara lokacin Yakin Cacar Baka, idan aka duba shi da yadda farashin kayayyaki ke sauya," a cewar O'Hanlon.

Asalin hoton, Getty Images
Idan aka yi duba da kuɗaɗen da aka kashe a shekaru 30 da suka gabata, sannan aka kwatanta da girman tattalin arzikin Amurka, za mu ga cewa yawan kuɗaɗen da ake kashewa a yanzu bai ko kama ƙafar wanda aka taɓa samu ba a tarihi.
Kuɗaɗen da ake kashe wa ayyukan soji sun yi ƙaruwar ban mamaki tun daga shekarar 2002 a yayin da Amurka ta shiga yaƙin Iraƙi da Afghanistan.
Ya kai ƙololuwa a 2010 irin ɗagawar da kason ma'aunin tattalin arziki kan dukkan kayayyakin ƙasar - inda daga nan Amurka ta fara janyewa daga shiga harkokin Gabas Ta Tsakiya da yankin Tsakiyar Asiya.
Ko babu dakarun Amurka da yawa a ƙasashen waje?
Shugaba Trump ya daɗe yana kira ga dakaru su koma gida, ya kuma soki shiga tsakanin da rundunar sojin Amurka ke yi da ke jawowa ƙasar kashe ɗumbin kuɗaɗe amma kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu ba.
Mr O'Hanlon ya ce: "Mr Trump ya matuƙar rage kaka-gidan da Amurka ta yi a Afghanistan da Iraƙi da Syria ba kamar yadda ya samu ba.''
A wannan shekarar shugaban ya rage yawan dakarun Amurka da ke Afghanistan zuwa 8,600 daga 13,000 da kuma shirin sake rage yawansu kafin zaɓen 3 ga watan Nuwamba.
Ammam Mr O'Hanlon ya ce: "Ya samar da dan wani sauyi ne kawai dangane da aikin soji a kasashen duniya da kuma dakarun da ake turawa kasashen waje, domin kuwa muna nan a duk inda muke a lokacin da ya hau mulki ranar 20 ga watan Janairu, 2017.

An fi rage yawan dakarun a lokacin Shugaba Obama, tun da a zamanin mulkinsa ne aka kawo ƙarshen dakatar da aike dakaaru masu matuƙar yawa Iraƙi da Syria.














