Zaben Amurka na 2020: Ana zargin Trump da batanci ga sojojin Amurka

An yi wa shugaba Trump na Amurka rufdugu sakamakon wasu kalaman batanci da aka rawaito ya yi a kan dakarun sojin kasar da suka mutu a fagen daga, da ya kira ''asararru''.
Abokin hamayyarsa a zaben kasar na watan Nuwamba Joe Biden, ya bayyana kalaman a matsayin abin kyama, yana kira ga shugaban ya nemi gafara.
Suma wasu manyan shugabannin sojin kasar sun yi Alawadarai da subul da bakan Mista Trump,. wanda tuni ya musanta cewa ya furta kalaman.
Jaridar The Atlantic ce ta rawaito labarin, wanda tuni sauran kafofin watsa labarai suka tabbatar da shi, ciki har da Fox, da ake kallo a matsayin 'yar gani kashenin shugaban.
Wadannan kalamai na shugaban na zuwa ne yayin da Amurkawa ke shirin jefa kuri'a a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba, wato nan da watanni biyu masu zuwa.
Sai dai ya sha furta irin wadannan kalamai na subul da baka, wadanda daga baya ke yawan janyo ce-ce-ku-ce.
Kalaman baya-bayan nan da ya yi shine kiran masu zabe a muhimmiyar jihar da ake kai ruwa rana a zaben shugaban kasar wato North Carolina da su kada kuri'a sau biyu yayin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.
A hukumance, yin irin wannan zabe tamkar magudin zabe ne.
Yayin wata ziyara da ya kai jihar, Mista Trump ya ce bai gamsu da yadda yawancin al'ummar jihar suka amince su yi zabe ta hanyar aika kuri'unsu ta akwatun gidan waya ba.
A don haka ne ya bukaci masu zabe a jihar su kada kuri'a a ta hanyar da aka saba wato bin layin jefa kuri'a, ko da kuwa sun aika kuri'unsu ta akwatun aikawa da sakonnin gidan waya.











