Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Bahrain da Isra'ila

Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu and Bahrain's Crown Prince Salman bin Hamad al-Khalifa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Yarima mai jiran gadon Bahrain Salman bin Hamad al-Khalifa
Lokacin karatu: Minti 1

Isra'ila da Bahrain sun cimma gagarumar yarjejeniya ta gyara huldar da ke tsakaninsu, a cewar Shugaban Amurka Donald Trump.

" Ita ce kasar Larabawa ta biyu da take neman zaman lafiya da Isra'ila a cikin kwana 30," in ji Mr Trump a sakon da ya wallafa a Twitter.

Galibin kasashen Larabawa sun kwashe shekara da shekaru suna janye jiki daga Isra'ila, suna masu cewa za su kulla dangantaka da ita ne kawai idan ta yi sulhu da Falasdinawa.

Sai dai a watan jiya Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Da ma dai an yi hasashen cewa Bahrain za ta biyo baya.

Mr Trump, wanda ya gabatar da shirinsa na zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya a watan Janairu wanda ke da zummar sulhunta Isra'ila da Falasdinu, ya shige gaba wajen kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu da Isra'ila.

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana "farin ciki" da cimma "wata yarjejeniyar zaman lafiyar" da wata kasar Larabawan.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

"Yau an sake kafa tarihi!" a cewar Mr Trump, inda ya kara da cewa: "Manyan abokanmu biyu Isra'ila da Bahrain sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya."

Bahrain ta zama kasar Larabawa ta hudu a Gabas Ta Tsakiya da ta amince da Isra'ila tun kafuwarta a 1948. Sauran kasashen su ne Masar da Jordan.

1px transparent line