Paul Auster: Dimokraɗiyyar Amurka na fuskantar barazana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Gerardo Lissardy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
"Kwashe wasu shekara hudu nan gaba cikin wannan yanayi, ina ga zamu wayi gari wata rana ba mu tsira da komai ba. Ina nufin komai," a cewar Paul Auster.
"Za mu kasance kasar da ake yi wa mulkin kama karya."
Marubuncin litattafai kamar 'The New York Trilogy da Moon Palace da na baya-bayan nan 4321', ya tattauna da BBC Mundo a gidansa da ke Brooklyn shi da matarsa Siri Hustvedt, wanda kuma rubuce-rubucensa suka shahara.
Yana kallon shugabanci Donald Trump na Amurka a matsayin barazana ga dimokraɗiyyar Amurka sannan yana gangamin adawa da sake zaɓarsa a wa'adi na biyu.
"Muna da rarrabuwar kawuna a matsayin ƙasa, zuciyarmu cike da ƙiyayyar juna," a cewar marubucin.
"Mun kasaftu gida biyu: akwai masu son Trump da waɗanda ba sa son sa."
Ga bayanan tattaunawar wayar tarho da aka yi da shi ƙunshe da jajircewa da sahihan bayanai da kuma batun annobar korona da ayyukansa.

Asalin hoton, Getty Images
Kana yawan maganar New York a litattafanka. Ya kake ganin birnin da kuma sauyin da kake ganin an samu tun bayan ɓullar wannan annobar da ta shafe shi sosai?
New York ya fuskanci manyan matsaloli a tarihinsa.
Mun sha ganin annobobi da iftila'i kala-kala; rikicin yaƙin basasa, kisan kiyashi, da harin 9/11....da murar 1918.
Wannan dai ya kasance daya daga cikin munanan yanayi da birnin ke tsintar kansa. A ɗan wani lokaci, New York ya kasance inda wannan annoba ta fi ɓarna a duniya. Amma an yi nasarar tunkararta da kyau, ina iya cewa haka, sama da abin da muka gani a wasu sassan duniya.
Kuma sannu a hankali, New York ya sake farfadowa, zuwa wani mataki.
Abu mafi muni shi ne wanda ya faru a ƙasar.
Babbar matsalar ita ce wanda muke da shi a matsayin shugaban ƙasa, da mutane da ke cikin jam'iyyarsa masu goya masa baya ya ƙalubalanci matsalolin kasa ba tare da wani tsari ba.
Shi ya haifar da mutuwar mutum sama da dubu 170 zuwa yanzu. Da miliyoyin mutanen da suka kamu da annobar.
Abin kunya ne.
Kuma zaɓe na tafe, abubuwa da dama ba su daidaita ba, akwai rashin tabbas, wa ya san abin da zai faru nan gaba?
Wannan shi ne abin da ya dame ni, sama da birnin da na fito.
Kana nufin annobar da abubuwan da ta haifar sun zarce abin da duniya ta shaida a harin 9/11 na New York?
Ƙwarai kuwa! 9/11 rana guda ce, sannan ya ɗauke mu watan kafin mu farfado. Hakan bai sake faruwa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Amma idan ka samu 9/11 na faruwa a kullum, to kana cikin matsala. Kuma abin da ya faru kenan a nan.
A lokacin da aka kai ƙololowa a Afrilu, ana samun aƙalla mutum 700 zuwa 900 da ke mutuwa a kullum a New York. Adadin akwai yawa.
Alƙaluma a hukumance kan yawan mutanen da suka kamu da cutar bai kai gaskiyar abin da aka sani a zahiri ba.
A litattafanka kana yawan maganar sauyi, abubuwan da suka faru da kamanceceniya...kamar kana ƙoƙarin fadamana cewa muna rayuwa cikin yanayi da bamu da iko a kai.
Abin da nake ƙoƙarin cewa tsawon wadannan shekaru shi ne komai zai iya faruwa ga kowa a kowanne lokaci.
Idan muka ci gaba da tafiya a hakan kuma, to mu shirya karbar abin da ke iya samu mu ba tare da mun yi zato ba.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wani abu a ran dan adam da ke neman daidaito da aminci, sannan, akasarin mutane na faɗawa cikin mumunan yanayi idan wani abu kwatsam ya auku ko wanda ba a saba gani ba.
Amma idan muka yi amfani da hikima da aikata abin da ya dace, muna iya nasara.
Kawai akwai mutane da yawa da ke bijire wa gaskiya, da kuma kin yarda da hujojjin kimiya.
Idan ba ka amince da abin da masana kimiya ke faɗamu ku ba, kuma kana ganin shan sinadarin wanke datti zai kawo ma sauki, ko duk abubuwan shirme da shugaba Trump ke cewa watannin shida da suka gabata..to, ka kasance cikin ƙasa da kowanne mutum na buga nasa shirmen.

Asalin hoton, Getty Images
Kusan rabin ƴan kasar basa sanya takunkumi, suna ganin wani tauye musu haƙƙi ne. To, mene ne? Yancin mutuwa? Na rasa gane abin da suke nufi...
Muna rayuwa cikin al'ummar da suka dogara da junansu.
Yadda mutane suke nuna son-kai da rashin tunani da ganin kamar suna da kariya kan abin da ke faruwa tsakanin mutanen da ke kusa da su, wani ɓangare ne na haukar siyasar da ya zauna a zukatan mutane.
Amurka na cikin wani yanayi a yanzu: annoba, zanga-zangar wariya, matsalar tattalin arziki da shugabancin Trump. Duk wadanan sun sauya matsayar marubuta da tunanin masu sharhi a cikin al'umma?
Kwarai kuwa! Sirri da ni a yanzu na cikin wata ƙungiya da kuma hada na "marubuta a kan Trump" (writersagainsttrump.org).
Muradin mu shi ne kwaɗaita matasa, wayanda suka zaɓi kauracewa zaɓe, domin sauya ra'ayinsu su je kaɗa kuri'a.
Aikin mu shi ne yin duk abubuwan da zamu iya, ko mu marubuta ne ko A'a, domin tabbatar da cewa ba a sake zaɓen Trump ba.
Bayan 3 ga watan Nuwamba, (lokacin da ake dakon kirga zabe) za a yi wata guda zuwa biyu da zai yi barazana haddasa rikici saboda komai na iya faruwa irinsa na farko tun yakin basasar Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Na yi tunanin dimbin labarai kan abubuwan da ka iya faruwa, daga madaidaici zuwa wanda ke iya wuce tunani. Amma babu wani abin kirki da zai faru a wannan lokaci.
Ga Trump, idan ya sha kaye, zai fuskanci shekaru yana ziriyar kotu kan laifukan da ya aikita.
Yana iya kare rayuwarsa a furuson, ba wai kan laifin da ya aikata a kasa ba, sai dai kan laifukan da ya aikata a jihar New York, kauracewa haraji, damfara da sauran abubuwan da yeke daban-daban a tsawon shekaru.
Don haka ya zaku ya cigaba da zaman mulki, kuma zai iya komai, komai, domin tabbatar da hakan.
Kana ganin kamar dimokraɗiyyar Amurka na cikin haɗari a yanzu?
Sosai kuwa cikin haɗari! Shekaru sama da hudu da suka gabata, Trump da gwamnatin Republican abin da suka aikata shi ne kokarin tarwatsa gwamnatin Amurka baki daya.
Duk wata ma'aikata ko kungiya da ya kamata ta tafiyar da kasar an tarwatsa su.
Hukumar kare muhalli ta janye tsare-tsarenta da dokoki, saboda gurbata muhalli ya kasance abin da gwamnati ke assasawa.
Muna da sakataren ilimi wanda bai yarda da makaratun gwamnati ba.
Muna da sakataren ƙwadago wanda ke adawa da ayyukan mutane.
Muna da sakataren ketare da rigakadi a fadin duniya, kasashen da bamu da wakilai kuma.
Muna da ma'aikatar shari'a da ke take dokokin da zama abin karan farautar da Trump da Republican ke amfani da shi.
Wannan bai taɓa faruwa a Amurka ba sai yanzu. Tabbas, dimokraɗiyya na cikin barazana.

Asalin hoton, AFP
Trump na kokarin murkushe zaɓen. Yana kokarin rufe ayyukan akwatin gidan waya; a daidai lokacin da ake son ya kasance aikinsa ya inganta, yana kokarin dakusar da shi saboda masu kada kuri'a ta wannan hanya ya kasance sakonninsu ba su iso kan lokaci ba, don haka ba za su shiga lissafi ba.
Shekaru hudu gaba kan wannan, sannan ina gani zai kasance babu abin da ya rage. Kusan babu komai.
Za mu kasance kasar da ake mulkin kama karya, abin da babu wanda ya taɓa tunanin zai faru shekaru hudu baya. Amma muna kan hanya, cikin gaggawa.
Amma masana siyasa da shari'a sun ce ma'aikatun Amurka, kamar ta shari'a da majalisa, sun nuna suna kan aiki....
Ba sosai ba, suna aiki amma ba wani aiki suke sosai ba.
Wani matakin ban mamaki ne a ce ka tarwatsa komai, cikin gaggawa
Kuma muna da majalisar mai rabuwar kawuna, mutane da ba wai masu tsattsauran ra'ayi ba ne amma sun kasance mahaukata masu mugunta kuma ba su da niyyar taimakawa kowa sai kansu...
Ina neman Afuwan kalamai na amma ina iya shaida ma mumunan yanayi da hadari da muke ciki a yanzu. Ban taba ganin abu irin wannan ba a rayuwata, kuma na kasance matashi a shekarun 1960.

Asalin hoton, Bettmann
Mene ne alaƙarka da sociyal midiya: makami ne ko matsala?
Ba ni da alaka da shi. Ba ni da Komfuta, Ba ni da wayar hannu. Ba na hawa intanet. Ba na son kasance cikin su.
Nasan intanet ya aikata abubuwan ban mamaki, kuma yana da tasiri ko sauyi wajen yadda ake sadarwa a yanzu.
Sai dai kuma yana da hadari. Yana da hadari sosai, yana yaɗa karya sama da kowanne kafa a tarihin rayuwar dan adam a duniya.
Ba ya tantacewa, kuma yana bude kofa ga maƙaryata.











