Coronavirus a duniya: Ƙasashe 10 da annobar ba ta ɓulla ba har yanzu. Shin sun tsira?

    • Marubuci, Daga Owen Amos
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Cutar korona kusan ta bulla a duk kasashen duniya - ban da guda 10. Ya aka yi hakan ya faru? Kuma me kasashe suka yi?

Otel din Palau fitaccen wuri ne, tun da aka bude shi a 1982 aka sanya masa wannan sunan. Shi kadai ke dauke da wannan sunan.

Tun daga lokaci, wannan 'yar ƙaramar kasa kewaye take da shuɗin sararin samaniya a Tekun Pacific, ta kan karɓi cikowar baki da ke zuwa yawon buɗe ido.

A 2019, masu yawon bude ido 90,000 sun ziyarci Palau, adadin ya ninka al'ummar kasar sau biyar. A 2017, alkaluman IMF ya nuna cewa baƙi ke samar da kashi 40 cikin 100 na kudin shigar ƙasar.

Wannan alƙaluma kafin zuwan korona ake ganin sa.

Tun karshen watan Maris aka rufe iyakokin Palau. Tana cikin kasashen duniya 10 da ba a samu mutum guda da ya kamu da cutar ba (Idan aka ware Koriya ta Arewa da Turkmenistan).

Duk da cewa babu mutum ko guda da ya kamu da cutar a kasar, tasirin annobar ya nuna sosai a kasar.

Otel din Palau ya kasance rufe tun a watan Maris, kuma ba shi kadai ba ne. Kantunan cin abinci sun kasance babu kowa, haka zalika shagunan sayar da kayan tsaraba, sannan bakin da suke cikin Otel din sun kasance suna keɓe kansu.

Ƙasashen da ba a samu bular korona ba

  • Palau
  • Micronesia
  • Marshall Islands
  • Nauru
  • Kiribati
  • Solomon Islands
  • Tuvalu
  • Samoa
  • Vanuatu
  • Tonga

''Yanayin teku a wannan wuri ya sha bamban da wanda aka saba gani a ko ina a duniya,'' a cewar Brian Lee, manaja kuma daya daga cikin masu Otel din Palau.

Wannan teku ya sa Brain kullum a cikin hidima. Kafin bullar Covid, dakunansa 54 na samun mutane kashi 70 zuwa 80 cikin 100. Amma ana rufe iyakoki sai yanayin ya sauya.

''Karamar kasa ce, don haka mutanen yankin ba za su zauna a Palau ba,'' a cewar Brian.

Yana da ma'aikata kusan 20, kuma duk sun cigaba da zama da shi, ko da yake ya rage mu su lokacin aiki. ''Na yi kokarin nema masu aiki - sa ido, gyararraki da sauransu,'' a cewarsa.

Brain bai zargi gwamnati ba, wadda ke taimakawa mazauna yankin da kudade, kuma a ko da yaushe ba ya sako annobar a matsayin hujja ko uzuri.

''Ina ganin sun yi aiki mai kyau,'' a cewarsa. Kuma idan otel din Palau zai rayu, dole a samu sauyi nan kusa.

Shugaban kasa ya sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Satumba hada-hadar jirage zasu soma dawo wa. Sannan a soma duba yiwuwar barin baki daga Taiwan shiga kasar don yawon shakatawa.

Otel din Robert Reimers na kan wani tsibiri da ke Majuro. Kafin barkewar annobar korona kashi 75 zuwa 88 cikin 100 na baki da ke ziyartar yankin akasari daga Asia da yankin Pacific ko Amurka na zama ne a dakunan otel din 37.

Tun rufe iyakoki a farkon watan Maris, aka samu koma baya inda kashi 3 zuwa 5 cikin 100 ake gani na baki.

''Yan kalilan muke samu da ke shigowa daga wasu tsibirai,'' a cewar Sophia Fowler, wacce ke aiki a otel din. ''Amma dai ba sosai ba.''

Mutane 700 aka yi hasashe za su rasa ayyukansu a yankin, kaso mafi girma tun 1997. Kuma 258 za su kasance masu aikin Otel da wurin cin abinci.

Amma yayin da rufe iyakoki ya sanya kasashen da cutar ba ta bulla ba ke talaucewa, ba kowa ke son ganin an sake bude iyakokin ba.

Dr Len Tarivonda shi ne daraktan da ke sa ido kan lafiyar al'umma a Vanuatu, mai al'umma 300,000. Ko da yake yana aiki ne a birnin, Port Vila, ya fito kuma daga Ambae, tsibirin da mutane dubu 10 ke rayuwa.

''Idan ka yi musu magana (a Ambae), galibinsu na cewa sun fi son iyakoki su kasance rufe har zuwa wani lokaci,'' a cewarsa: 'Ba ma son ciwon - amma dai muna cikin mummunan yanayi.''

Kashi 80 cikin 100 na mutanen Vanuatu na rayuwa a wajen garin, a cewar Dr Tarivonda.

''Kuma abin da na lura da shi, shi ne ba sa jin radadin yanayin da ake ciki. Manoma ne na hakika, suna noma abincinsu - sun dogara ne da tattalin arzikin yankin da na al'adu.''

Duk da haka, kasar za ta shiga kangin wahala. Bankin raya yankunan Asiya na hasashen faduwar tattalin arzikinta da kashi 10 cikin 100 - a Vanuatu wannan zai kasance koma baya mafi girma tun samun 'yancin kai a 1980.

A watan Yuli, gwamnati ta sanar da shirin sake bude iyakokinta ga kasashen da ba su da hadari a ranar 1 ga watan Satumba. Samun karuwar masu cutar a Australia da New Zealand shi ya ruguza shirin.

Dr Tarivonda, wanda ke aiki tare da jami'an gwamnati a kan iyakoki ya ce kusan an sake koma wa gidan jiya domin har yanzu babu ranar sake bude iyaka.

Duk da bukatar da ake da ita na sake bude iyakoki, Vanuatu ba za ta yi azarbabin bude iyakarta ba.

Dr Tarivonda ya ba da misali da Papua New Guinea wanda kusan cutar babu ita a kasar amma dai gashi a karshen watan Yuli an sake samun ta'azzararta, tare da nuna damuwa.

''Idan annobar tazo, za ta kasance kamar wutar daji - kuma abin da muke gani a Papua New Guinea gargaɗi ne kan dalilan da suka sa dole mu shiga damuwa,'' a cewarsa.

Akwai wani abu da kasashen da babu korona za su iya yi?

Akwai matakai na gajeren lokaci, kamar biyan albashin ma'aikata da 'yan kasuwa. Sannan akwai matakai na dogon lokaci: jiran riga-kafi.

Kafin wannan lokaci, dawowar balaguro shi kawai ake sa rai. Sai dai kamar yadda Rommel Rabanal na bankin Asiya ke cewa, fadin abin a baki ya fi tabbatarsa sauki.

''Wadannan tsare-tsare sun zama wajibi,'' a cewarsa. ''Tabbatar da tsarin gwaji, bibiyar mutane, da kayayyaki kebe mutane idan an samu barkewar annobar. Ana kan tattaunawa sai dai cigabar da ake samu na tafiyar hawainiya - ko kuma kokarin taka tsan-tsan ne.''

Kuma - kamar yadda muka gani a Vanuatu ''shirinta na Satumba'' - cikowar mutanen da ake son gani na iya tabbata.

''Australia da New Zealand sun sanar da cewa za su kasance kasa ta farko da za a yiwa juna gwaji,'' a cewar Jonathan Pryke, darakta a shirin ci gaban yankin Pacific na cibiyar Lowy.

''Kuma kafin hakan ya faru, akwai bukatar kawar da yaduwar cutar tsakanin al'umma. Don haka ina ganin takaita kwararar matafiya a wannan shekara ita ce mafita.''

Mista Pryke ya ce, yayin da watanni ke wucewa, damuwa na karuwa a kasashen yankunan Pacific.

Ya ce, wadannan kasashen babu shaka ba su da zaɓi sama da kebe kansu daga waɗanda zasu yi kokarin shigowa kasar daga ketare.

''Ko da sun bar iyakokinsu bude, kasuwan bakin da ke zuwa yawon bude ido a Australia da New Zealand zata kasance rufe, yayin da suka rufe iyakokinsu,'' a cewarsa.

''Don haka yanayin zai kasance mai tsananin a kowanne bangare - matsalar tattalin arziki da fanin kiwon lafiya. Za a shafe tsawon shekara da shekaru na nazari kan yanke hukuncin da ya dace.

''Amma idan aka yi waiwaye, babu shaka dokar kulle ta taimakawa yankunan Pacific.''