Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
George Floyd: Me ya sa ba a cika hukunta 'yan sandan Amurka ba?
- Marubuci, Daga Pablo Uchoa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
An yi kiyasin cewa 'yan sanda na kashe kusan mutum 1,200 a duk shekara a Amurka, kuma kashi 99 cikin 100 na kisan da suke yi, ba a kama 'yan sandan da wani laifi.
Sakamakon wutar da aka huro ta hanyar zanga-zanga da tayar da zaune tsaye bayan kashe George Floyd, a halin yanzu an gurfanar da 'yan sandan da ake zargi da kisan.
Ɗaya daga cikin 'yan sandan da ake zargi Derek Chauvin na fuskantar tuhume-tuhume da suka danganci kisa. Ya murƙushe Floyd har ƙasa idan ya danne masa wuya da gwiwarsa na kusan mintuna tara kafin Floyd ya mutu a garin Minneapolis a ranar 25 ga watan Mayu.
Sauran 'yan sandan da ke wurin da lamarin ya faru su ma ana tuhumar su da laifin taimaka wa wajen aiwatar da kisa. Akwai yiwuwar duka 'yan sandan huɗu su yi zaman gidan yari na shekaru 40.
Masu zanga-zangar na da yaƙinin cewa mutuwar Floyd za ta kawo sauyi matuƙa kan yadda ake shari'ar 'yan sanda da suke kashe mutane da sunan suna kan aiki.
Amma a ƙarkashin dokar Amurka, 'yan sanda a Amurka na samun rangwame idan aka zo yi musu shari'a.
Kama 'yan sanda da laifi 'na da wuya'
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa 'yan sanda sun kashe mutum 7,666 a Amurka tsakanin 2013 zuwa 2019.
Cikin kashi 99 cikin 100, kashi ɗaya ne kawai daga cikin laifukan kisan da 'yan sandan suka yi aka yanke musu hukunci, binciken ya nuna cewa 'yan sanda 25 ne kaɗai aka same su da laifi.
Clark Neily, wanda shi ne mataimakin shugaban cibiyar hukunta laifuka da ke birnin Washington DC ya shaida wa BBC cewa abu ne mai wuya ga masu tuhuma su kai ƙarar 'yan sanda kotu, kamar yadda hakan ta faru kan batun Floyd.
Neily ya bayyana cewa masu tuhuma da kuma 'yan sanda dukansu jami'ai ne da ke tabbatar da doka - suna aiki tare da juna - masu tuhuma na dogara da 'yan sanda domin neman hujjoji da bayanai.
Wannan na nufin wannan amfani da ƙarfi ga 'yan sanda na ɗaya daga cikin aikinsu kuma yana cikin doka - misali a ƙoƙarin kare kai daga jin rauni ko kuma kisa.
Kare su daga fuskantar shari'a
Iyalan waɗanda aka kashe ba su da wani zaɓi illa su kai 'yan sandan kotu, amma Neily ya bayyana cewa a kullum kotuna ba su cika sauraren irin waɗannan ƙararrakin ba sakamakon wata ƙa'ida da ake da ita ta "rigar kariya".
Hakan na kare manyan ma'aikata daga fuskanatar shari'a ko da sun take haƙƙin wani, sai dai idan akwai wasu ƙwararan hujjoji.
A 2014, wani lamari ya taɓa faruwa a gidan Amy Corbitt inda 'yan sanda suka faɗa cikin gidanta yayin da suke bin wani mai laifi. Ko da 'yan sandan suka shiga gidan, sai suka buƙaci yaranta shida waɗanda ke wasa da su kwanta a ƙasa.
Kwatsam sai ga wani kare na Amy ya fito, sai ɗaya daga cikin 'yan sandan ya harbi karen duk da cewa karen bai nuna wata alamar barazana ba ga 'yan sandan kamar yadda takardun kotu suka nuna.
Ko da ɗan sandan ya harbi karen, sai harsashin ya kauce inda ya samu yaron Amy mai shekaru 10, Dakota. Yaron bai mutu ba amma ya samu munanan raunuka a ƙafa.
A ƙarshe kotu ta yi watsi da buƙatarta bayan ta kai ƙara inda ta ke neman a kama 'yan sandan da laifi.
Adalci ga Floyd
Neily ya bayyana cewa rigar kariya da 'yan sanda ke da ita a Amurka zai iya sa wa da wahala iyalen Floyd su samu abin da suke so ta bangaren adalci.
"Idan baza su iya samo wani lamari makamancin wannan ba da kotu ta yanke hukuncin cewa bai cikin tsarin mulki a murƙushe wuyan mutum na minti tara, to wannan batun na rigar kariya na nufin ba za a iya gurfanar da 'yan sandan ba, sakamakon babu makamancin haka a rubuce."
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Ƙungiyar 'yan sanda ta Amurka amma ta ƙi amincewa ta tofa albarkacin bakinta.
Shugaban ƙungiyar Michael McHale a baya ya yi magana kan batun kisan Floyd, inda ya ce: "Abin da ya faru da George Floyd abu ne mai muni. Babu wata hujja a doka, ko kuma dokar kare kai da za ta sa ɗan sandan ya aikata abin da ya yi."
Irin wannan abin da Michael ya faɗa, 'yan siyasa da dama a ƙasar suna faɗin irin haka.
Wutar da mutane suka huro ta taka muhimmiyar rawa wajen yadda aka bai wa kisan Floyd muhimmanci, amma akwai buƙatu na ƙara yin wasu sauye-sauye.
Masana da kuma wasu rahotanni daga kafofin yaɗa labarai sun bayar da shawarwari kan cewa Kotun Kolin ƙasar ta sake bitar batun rigar kariya da ake ganin cewa 'yan sanda a ƙasar suna da ita.
Masu fafutuka a ƙasar kuma sun yi kira da a kafa wata doka da za ta hana jami'an tsaro amfani da mugun ƙarfi har sai abin ya zama tilas, kuma za su iya amfani da ƙarfin ne kawai idan babu duk wata hanya sai ta amfani da ƙarfin.
Wasu daga cikin 'yan majalisa a ƙasar sun goyi bayan kafa wata doka da za ta hana kai makaman sojoji zuwa ga 'yan sanda. Akwai sauran ƙudurori masu kama da wannan da ke kan hanya.