Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
George Floyd: Shin Trump zai iya tura sojoji su fatattaki masu zanga-zanga?
- Marubuci, Daga Jake Horton
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Tawagar Binciken Kwaf ta BBC
Yayin da zanga-zanga ke ci gaba da mamaye jihohin Amurka, Shugaba Trump ya yi barazanar tura sojoji domin daƙile ta.
Mista Trump ya ce zai tura dakarun ne idan jihohi da birane suka gaza kawo ƙarshen tarzomar.
Sai dai wasu gwamnoni sun ce Trump ba shi da ikon yin hakan ba tare da amincewar jihohin ba.
Ko shugaban yana da ikon tura dakaru?
A taƙaice, yana da iko bisa wasu dalilai.
Tuni aka tura wasu dakarun daga Rundunar Tsaro ta ƙasa, wadda take a matsayin rundunar ko-ta-kwana.
An tura su kusan jihohi 20 da zummar kawo ƙarshen zanga-zangar, sai dai jihohin ne suka buƙace su da kansu.
Sai dai wata doka da aka ƙiƙira a ƙarni na 19 ta zayyana yadda shugaban Amurka zai iya tura dakakru ba tare da amincewar jihohi ba.
Dokar -- mai laƙabin Insurrection Act -- ta ce ba a buƙatar amincewar gwamnoni idan shugaban ƙasa ya aminta cewa yanayin da ake ciki ya ƙazanta ko kuma idan aka tauye haƙƙin 'yan ƙasa.
An ƙirƙiri dokar ne a shekarar 1878 domin bai wa shugaban ƙasa damar gayyato wata ƙungiya don kare kai daga hare-haren mayaƙa da ake kira Indians.
Daga baya an faɗaɗa ta yadda shugaban ƙasa zai iya amfani da sojoji yayin rikici da kuma kare haƙƙin ƴan ƙasa.
Wata dokar da aka yi a shekarar 1878 ta buƙaci a nemi amincewar majalisar dokoki kafin tura dakaru a cikin Amurka, amma wani masanin shari'a ya faɗa wa BBC cewa Insurrection Act kaɗai ta isa shugaban ƙasa ya dogara da ita.
Robert Chesney, wani malami a Sashen Shari'a na Jami'ar Texas, ya ce abin lura a nan shi ne: "Shugaban ƙasa ne ya kamata ya yanke hukunci; ba lalai sai gwamnoni sun nemi tallafinsa ba."
Ko an taɓa yin amfani da dokar kafin yanzu?
A cewar wani bincike na Majalisar Dokoki, an yi amfani da dokar Insurrection Act sau da yawa a baya, duk da cewa an shafe kusan shekara 30 ba a yi hakan ba.
Rabon da a yi amfani da ita tun shekarar 1992, inda Shugaba George Bush ya yi amfani da ita wurin daƙile zanga-zangar wariyar launin fata a birnin Los Angeles.
An sha yin amfani da ita a shekarun 1950 da kuma 1960 yayin rajin ƙungiyoyin fararen hula - shaugabanni uku ne suka yi amfani da ita.
Shugaba Dwight Eisenhower ya fuskanci tirjiya lokacin da ya yi amfani da dokar a shekarar 1957 da ya tura dakaru zuwa wurin zanga-zanga a wata makaranta a Jihar Arkansas.
Tun bayan shekarun 1960 ba a fiya amfani da dokar ba. Majalisar Dokoki ta yi mata kwaskwarima a 2006 bayan afkuwar Guguwar Katrina domin sauƙaƙa tallafin da sojoji za su bayar, sai dai an dakatar da sauyin bayan gwamnoni sun nuna adawa da shi.