Kullen Coronavirus: Shugabannin duniya 10 da suka karya dokokin coronavirus

    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Akwai kakanni da suka gaza rungumar jikokinsu; waɗanda aka yi wa rasuwa amma suka kasa zuwa jana'iza; abin baƙin ciki annobar korona ta raba masoya da abokai da dama.

Dokokin kulle da zummar daƙile yaɗuwar annobar sun jawo sadaukarwa mai yawa daga ɓangaren mutanen gari.

Kazalika waɗanda suka zabi su karya dokar sun fuskanci tara iri-iri kuma mai yawa a wasu ƙasashe.

Sai dai an ga wasu shugabannin siyasa da masana harkar lafiya da masu bayar da shawara suna karya dokokin.

Mun duba mafiya shahara daga ckinsu kamar haka:

Mutuwar babban jami'in gwamnati a Najeriya

A Najeriya, annobar korona ta shiga har fadar Gwamnatin Tarayya.

Abba Kyari wanda shi ne Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati da kuma Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da ke arewa maso gabashin ƙasar, duka an bayyana sun kamu da cutar ranar 26 ga watan Maris.

Rahotanni sun nuna Abba Kyari mai shekara kusan 70, ya dawo daga Jamus, inda kuma ya halarci taron jam'iyyar APC mai mulki - wanda Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da gwamnoni 16 suka halarta.

'Yan makonni bayan nan Malam Abba Kyari ya rasu a ranar 17 ga watan Afrilu. Shi ne babban jami'in gwamnati da cutar ta yi ajali a Najeriya.

Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa an karya dokokin da aka tanada yayin jana'izarsa, abin da har sai da ya kai ga hana wasu manyan jami'ai da suka je jana'izar- ciki har da ministoci - shiga Fadar Shugaba Buhari ta Aso Rock Villa.

Donald Trump

Amurka kaɗai tana da kashi 30% na waɗansda suka rasa rayukansu sakamakon annobar korona a duniya baki ɗaya.

Tun a makon farko na watan Afrilu hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Amurka (CDC) ta bayar da shawarar cewa ya kamata Amurkawa su saka takunkumi a bainar jama'a domin rage yaɗuwar cutar.

Donald Trump bai yi aiki da wannan shawara ba. "Ba na son saka shi ni kaina," in ji shi, yana mai cewa zai yi mamaki idan ya gan shi da takunkumi zaune a kan kujerar ofis ɗinsa yayin da yake gaisawa da sauran shugabannin duniya.

A ranar 21 ga watan Mayu, Trump ya ziyarci Jihar Michigan - inda saka takunkumi wajibi ne a bainar jama'a - don ganin yadda aikin ƙera na'urar taimaka wa numfashi ke tafiya.

Shugabannin kamfanin da ke yin aikin kowannensu na sanye da takunkumin amma shi ya ƙi sakawa.

Da 'yan jarida suka mata matsa masa da tambaya sai ya ce ya saka a lokacin da ba su gani ba. "Ba na son 'yan jarida su gani ne," in ji shi.

Amma matarsa Melania Trump ta wallafa wani bidiyo a shafukan zumunta tana jaddada shawarar CDC ta saka takunkumi a bainar jama'a kuma ta nuna kanta sanye da shi.

Jumullar waɗanda suka mutu a Amurka sakamakon korona sun zarta dubu 100.

Vladimir Putin

Shugaban Rasha, Vladmir Putin ya yi ta ƙoƙarin nuna jajircewarsa game da yaƙi da cutar korona a idon 'yan ƙasar.

Ranar 24 ga watan Maris - lokacin da cutar ke kan ganiyarta - ya kai ziyara wani asibiti a birnin Moscow domin duba yadda aiki ke tafiya.

Shugaban ya sanya kwat ƙirar hazmat (mai bayar da kariya) yayin ziyarar amma bai saka wasu kayan kariya na likitoci ba.

Wannan ɗabi'a na da haɗari sosai musamman yadda ya gaisa da jagoran daktocin, Denis Protsenko wanda ya kamu da cutar 'yan kwanaki bayan haka.

Daga lokacin ne Putin ya fara ja da baya, inda ya fara jagorantar taruka daga gida kuma ya rage fitowa bainar jama'a.

Ya zuwa 2 ga watan Yuni, Rasha na da waɗanda suka kamu da cutar 423,186 - ƙasa ta uku mafi yawan masu cutar a duniya bayan Amurka da Brazil - da kuma waɗanda suka mutu fiye da 5,000.

Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Ƙasa Reuven Rivlin sun sha suka bayan sun haɗa wata liyafar cin abinci da manyan 'ƴa'ƴansu kwanaki kaɗan bayan sun gargaɗi 'ƴan ƙasar kada su yi hakan.

'Ƴan kwanaki kafin a fara bikin da suke kira Passover, Netanyahu ya saka dokar hana fita a ƙasa baki ɗaya sannan ya umarci mutane da su guji yin taruka da zummar daƙile yaduwar korona.

Sai dai kwanaki kaɗan bayan haka sai ga shi an gan shi yana cin abinci tare da ɗansa a ranar bikin na Passover.

Muƙarraban shugaban sun kare abin da ya aikata suna masu cewa ɗan nasa mai suna Avner ya shafe sa'o'i a gidan mahaifinsa sannan kuma yana zaune ne a kusa da gidan.

Amma 'ƴan jarida sun soki ingancin wannan bayani na jami'an gwamnatin.

Siyasar addini

Firaministan Indiya ya saka dokar kulle mafi girma a duniya ranar 24 ga watan Maris, wadda ta shafi mutum biliyan 1.35. An rufe wuraren ibada ma.

Miliyoyin ƴan ci-rani sun shiga tasku, yayin da dubbansu suka yi tafiyar ƙasa ta tsawon ɗaruruwan kilomitoci.

Sai dai wani babban ɗan siyasa mai suna Yogi Adityanath ya karya dokar a ranar farko da ta fara aiki.

Babban Ministan Uttar Pradesh - jiha mai al'umma mutum miliyan 230 - ya wallafa hotunansa a intanet ana damawa da shi a wani taron addini, inda ake sake ƙoƙarin gina wani wurin ibada a Ayodhya mai cike da ce-ce-ku-ce.

Wata ɗaya bayan mahaifinsa ya mutu, Yogi ya shawarci mahaifiyarsa da ƴan uwansa da "su bi dokokin bayar da tazara yayin jana'iza" amma shi kansa bai je jana'izar ba.

An hukunta minista a bainar jama'a

Ministar Sadarwa ta Afirka ta Kudu Stella Ndabeni-Abrahams ta fuskanci dakatarwa ta tsawon wata biyu sannan aka tilasta mata bai wa jama'a haƙuri bayan ta karya dokar hana fita.

Hotunan da aka wallafa sun nuna ministar ta ci abincin rana da wasu mutum biyar a gidan wani tsohon minista.

Minsitar ta nemi afuwa bayan ta sha suka. "na yi nadamar abin da na aikata kuma ina neman afuwa," in ji ta.

An ci tarar ministan lafiya

An ci tarar mataimakin ministan lafiya na Malaysia sakamakon karya dokar kulle a ƙsar.

Noor Azmi Ghazali ya biya tarar dala 325 bayan wani hoto da aka saka a shafukan zumunta ya nuna shi yana cin abinci a wata makarantar Islamiyya.

Shawarwari masu cin karo da juna

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya tsira daga cutar korona da ta kama shi bayan ya shafe kwanaki a asibiti.

Kwanaki kaɗan kafin ya kwanta a asibiti, Johnson ya saka tsauraran dokokin kulle.

Farfesa Neil Ferguson - wanda shawararsa ta janyo saka dokar kullen - ya sauka daga muƙaminsa na kwamitin kwararru mai bai wa firaminista shawara kan harkokin gaggawa saboda "kuskuren yanke hukunci".

Wannan ya biyo bayan wani rahoto a wata jarida cewa budurwarsa ta ziyarce shi a gidansa yayin dokar kulle.

Ferguson ya ce ya yi nadamar rashin ɗaukar abubuwan da aka riƙa bayyanawa a shafukan zumunta da muhimmanci.

An samu rahoton ne a ranar da Birtaniya ta zarta Italiya a yawan waɗanda suka mutu sakamakon cutar korona.

Ita ma Babbar Ministar Scotland ta sauka daga muƙaminta bayan ta sha suka biyo bayan wani balaguro da ta yi yayin dokar.

Dr Catherine Calderwood ta so ta ci gaba da zama a muƙamin nata bayan ta nemi afuwa, sai dai ta ji matsi sai ta haƙura.

Lokacin da labari ya ɓulla cewa amintaccen mai bayar da shawara ga Firaminista Boris Johnson ya yi balaguron na mil 260 daga gidansa na Landan zuwa Durham da ke arewacin Ingila yayin dokar kulle, Johnson ya sha caccaka.

Cummings ya haƙiƙance cewa shi bai karya kowacce doka ba.

Ƴan sanda sun ce aikin nasa zai iya kasancewa ya karya dokar kaɗan, sai dai da alama Cummings ya samu goyon bayan mai gidansa kuma zai ci gaba da zama a muƙaminsa.

Har yanzu Birtaniya ce ƙasa ta biyu da ta fi fama da annobar korona, inda mutum kusan 40,000 suka mutu.