Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasashen duniya 7 da ba su san annobar coronavirus ba
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Zuwa ranar Talata 31 ga watan Maris akwai fiye da mutum 800,000 da ke dauke da coronavirus, inda mutum fiye da 39,000 suka mutu sakamakon cutar a fadin duniya.
Alkaluma na baya-bayan nan daga hukumar da ke dakile yaduwar cututtuka ta Afirka, ACDC, sun tabbatar da cewa kasashe 49 daga cikin 54 a nahiyar Afirka na da mutum fiye da 195,000 da suka kamu da cutar ta coronavirus, al'amarin da ya sa kasashen nahiyar da dama daukar matakan dakile ta, ciki har da dokar hana fita.
Alkaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 172 da suka mutu a nahiyar sakamakon cutar, sannan kuma mutum 387 sun warke daga cutar.
To sai dai hukumar ta ACDC ta ce akwai kasashe guda biyar a nahiyar ta Afirka da har yanzu ba a samu bullar annobar coronavirus a can ba:
- Sao Tome and Principe
- Malawi
- Comoros
- Lesotho
- Sudan Ta Kudu
Sao Tome and Principe: Wannan tsibiri ne da ke yankin Afirka ta tsakiya mai yawan jama'a 201,800. Turawan kasar Portugal ne suka reni wannan tsibiri.
Malawi: Kasa ce da ke yankin kudu maso gabashin nahiyar Afirka, inda ta yi iyaka da Zambia da Tanzania da kuma Mozambique. Tana da yawan jama'ar da suka haura 18,000,000.
Comoros: Wannan kasar ita ma tsibiri ce a yankin kudu maso gabashin Afirka. Kuma tana daya daga cikin kasashen Afirka masu karancin yawan jama'a, inda take da mutum 850,000.
Lesotho: Ta yi iyaka da Afirka Ta Kudu, inda take da yawan jama'a kimanin 2,000,000.
Sudan Ta Kudu : A shekarar 2011 ta samu 'yancin kai daga tarayyar Sudan, inda kuma bayan nan kasar ta tsunduma cikin yakin basasa, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da daidaita 'yan kasar da dama. Sudan ta Kudu na da yawan jama'a da ba su kai milyan 11 ba.
Dangane kuma da kasashen duniya, baya ga wasu kananan tsibirai da ba a kai ga tantance halin da suke ciki ba, har yanzu ba a samu mutum ko daya da ya kamu da cutar coronavirus a Yemen da Koriya Ta Arewa ba.
6. Yemen: Ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO a kasar Yemen ya ce har yanzu babu ko da mutum daya da ya kamu da annobar coronavirus da ake yi wa lakabi da COVID-19.
To sai dai ofishin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa bisa hadin gwiwar ofishin da hukumar lafiya ta Yemen, an samar da cibiyoyin killace jama'a a birnin Aden domin kasancewa a halin ko-ta-kwana.
Kasar Yemen dai ta yi fama da yakin basasa, inda dubban 'yan kasar suka mutu sannan wasu suka daidaita. Yemen na da yawan jama'a fiye da milyan 28.
7. Koriya Ta Arewa: Kasar har kawo yanzu dai ba ta sanar da ko da mutum daya da ta ce ya kamu da cutar coronavirus ba.
To sai dai rahotanni da dama na alakanta halin ki-fadi da rashin gwada jama'ar kasar da rashin bai wa 'yan jarida damar ruwaito abin da ke faruwa a kasar da kuma halin saniyar ware da kasar take fuskanta da dalilan da ya sa ba za a iya fahimtar ko 'yan kasar na da cutar ta coronavirus ko babu.
Koriya ta Arewa dai na fuskantar jerin takunkumi iri-iri daga Amurka da kawayenta kan shirinta na makaman nukiliya.
Yanzu dai abin zura ido a gani shi ne ko wannan annoba za ta kutsa wadannan kasashe ko a'a bisa la'akari da yadda duniya ta dinke wuri guda.
Yawanci dai kasashen Afirka sun samu wannan annoba daga 'yan kasar ne wadanda suka je wasu kasashen waje, inda wasu lokutan ma wasu 'yan kasashen wajen da suka shiga kasashen na Afirka ne suka yada cutar.
Karin labaran da za ku so ku karanta