Daliban Kano sun yi hatsari a Lagos

A Najeriya, daliban makarantar Sakandare shida 'yan jihar Kano tare da jagoransu da kuma direba sun rasu ranar Laraba sakamakon hatsarin mota a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.
Daliban na kan hanyarsu ta zuwa Lagos ne domin wakiltar jihar Kano a gasar kacici-kacici ta kasa baki daya.
Uku daga cikin daliban 'yan makarantar Unity ne yayin da ragowar guda ukun 'yan makarantar Kano Capital ne.
Ana sa ran za a kai gawarwakinsu Kano ranar Alhamis.







