Otedola ya yi asarar dala miliyan 400

Mujallar Forbes da ke Amurka ta ce hamshakin attajirin nan dan Najeriya, mai kamfanin mai na Forte, Femi Otedola, ya yi asarar $400m a makonni tara da suka wuce bayan hannayen jarin kamfaninsa sun fadi da kashi 43 cikin 100 a kasuwar hannayen jari.
Mujallar Forbes da ke Amurka ta ce hamshakin attajirin nan dan Najeriya, mai kamfanin mai na Forte, Femi Otedola, ya yi asarar dala miliyan 400 a makonni tara da suka wuce bayan hannayen jarin kamfaninsa sun fadi da kashi 43 cikin 100 a kasuwar hannayen jari.
Mujallar ta ce kowanne hannun jarin kamfanin ya fadi zuwa N193 daga N342 a karshen watan Fabrairu.
Ta ambato wata majiya a kamfanin mai na Forte na alakanta faduwar hannayen jarin da janye jarin da wasu masu hannayen jari a kamfanin suka yi.
A watan Maris ne dai mujallar ta yi kiyasin cewa kudin da Mista Otedola yake da su sun kai $1.6bn, amma yanzu yana da $1.2bn.







