Iran ta kawo cikas a taron OPEC

Asalin hoton, AP

Rahotanni na cewa an shiga rikici a wani taro da ake na kasashen dake fitar da man fetur a Qatar da nufin amincewa a dakatar da samar da man, sakamakon rawar da Iran ta taka a kasuwar man.

Saudi Arabia da kuma wasu kasashen na fatan dakatar da yawan man da ake samarwa zai sa farashin man ya tashi, wanda ya yi kasa tun tsakiyar shekarar 2014.

Amma Iraniyawa ba sa shirin amincewa da daina samar da man, kuma ba sa halartar Taron.

Akwai alamu a baya cewa Saudi Arabia ba za ta dakatar da samar da man ta ba har sai Iran ita ma ta yi hakan, kuma wannan batu a yanzu rahotanni sun ce shi ne ya ke kawo cikas a tattauwar da ake yi a Qatar