Zanga-zanga ta barke a Hong Kong

Asalin hoton, AP
'Yan sanda a Hong Kong sun yi amfani da kulake da hayaki mai sa hawaye a lokacin wata arangama da masu zanga-zanga, bayan da jami'an suka yi yunkurin hana ciniki a bakin hanya a yankin Mong Kok.
Masu zanga-zangar sun yi ta jifan 'yan sandan da duwatsu da sauran tarkace tare da banka wuta a kan tituna.
Rundunar 'yan sanda ta ce ta cafke mutane ashirin da hudu, yayin da aka jikkata jami'anta 48.
Zanga-zangar ta hada da masu fafutuka daga kungiyoyi daban-daban, inda suke bukatar kara samun 'yanci daga gwamnatin kasar.







