Shin wanene Musulmi ?

A wannan makon 'yan siyasa sun yi wadansu kalamai kan Musulmi da kuma wani martani da aka yi kan harin da aka kai a tashar jirgin kasa a London.

BBC ta tambayi wani ma'aikantanta 11 a kan shin ko su waye Musulmi ana su fahimtar ?

Wanda ke kan gaba a neman tsayawa takarar shugaban Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Republican, Donald Trump a wannan makon ya bukaci a haramta wa Musulmi shiga Amurka, bayan da aka kai hari a California.

Wasu ma'aurata Musulmi ne wadanda aka hurewa kunne suka kashe mutane 14 a cibiyar lafiya ta San Bernardino.

'Yan jam'iyyar Republican da na Democrats da shugabannin Musulmi da majalisar dinkin duniya sun yi Allah wadai da wannan kira da suka ce yana da hadari sosai.

Mr Trump ya ce Musulmi na barazana ga Amurka, amma kuma abin tambaya shin ko duka Musulmai ne ke da hadari ?

Ga ra'ayoyin wasu ma'aikatan BBC wadanda suma Musulmai ne.