EFCC ta damke Godswill Akpabio

Asalin hoton, BBC World Service
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta damke Mr Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan kasar.
Bayanai sun ce da yammacin ranar Juma'a ne jami'an EFCC din suka damke tsohon gwamnan.
Ana zarginsa ne da wawure dukiyar al'umma a zamanin mulkinsa a jihar ta Akwa Ibom.
Wata majiya a hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ana yi wa Mr Akpabio tambayoyi a ofishin hukumar da ke Abuja.
Sai dai kuma wasu rahotanni na cewa tun a daren ranar Juma'ar ne hukumar ta saki mista Akpabion ya koma zuwa gidansa.
Mr Godswill Akpabio shi ne gwamnan jihar Akwa Ibom daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A yanzu haka dai EFCC na binciken wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni a Nigeria ciki har da Alhaji Sule Lamido na Jigawa da Murtala Nyako na Adamawa da Gabriel Suswan na Benue da kuma Ikedi Ohakim na jihar Imo.







