Ambaliya ta yi barna a jihar Gombe

Wani yanki da ambaliyar ruwa ta afkawa a Najeriya
Bayanan hoto, Wani yanki da ambaliyar ruwa ta afkawa a Najeriya

Rahotanni daga jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a garuruwan Gombe da kuma Bajoga.

Rahotannin sun ce ambaliyar ruwan ta lalata daruruwan gidaje da gonaki, kuma al'amarin ya fi muni a garin Bajoga.

Lamarin ya faru ne sakamakon ruwan da aka tafka kamar da bakin kwarya a ranar Laraba.

A baya-bayan nan hukumomin Kamaru suka yi gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu sassa na Najeriya sakamakon bude madatsar ruwa na Lagdo.