Jirgi mai saukar ungulu ya fadi a Adamawa

Jirgin ya fadi ne kusa da sansanin 'yan gudun hijira da ke Girei

Asalin hoton, Adamawa Resident

Bayanan hoto, Jirgin ya fadi ne kusa da sansanin 'yan gudun hijira da ke Girei

Wani jirgi mai saukar ungulu ya fadi a karamar hukumar Girei da ke jihar Adamawa a arewa-maso gabashin Nigeria ranar Litinin.

Wasu 'yan jarida da suka je inda jirgin ya fadi sun shaida wa BBC cewa, mutane hudu da ke cikin jirgin turawa uku da kuma baki daya duka sun tsira.

Haka kuma rahotanni sun kara da cewa akwai yiwuwar jirgin na leken asiri ne, domin bai yi kama da jiragen da ake kai hare-hare da su a yankin ba.

Jami'an sojin Najeriya dai daga bisani sun killace wurin da jirgin ya fadi kuma sun hana 'yan jarida kaiwa inda ya ke.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga hukumomin Nigeria game da faduwar jirgin.