Nyanya: SSS ta kama wasu matasa

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, SSS ta ce ta kama wasu mutane biyar da take zargi da kitsa kai harin Nyanya a Abuja.
Harin na ranar 14 ga watan Aprilun da ya gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 70, tare da jikkata wasu da dama.
Hukumar ta SSS ta kuma ce tana neman wani Rufai Abubakar Tsiga da aka fi sani da Dr Tsiga da kuma Aminu Sadiq Ogwuche, ruwa a jallo game da harin.
SSS ta ce zata bayar da tukwicin naira miliyan 25 ga duk wanda ke da bayani a kan mutanen biyu.







