An kai tagwayen hare-hare a Borno

Asalin hoton, AFP
A Najeriya wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wasu tagwayen hare-hare a Jihar Borno.
An kashe akalla mutane 38 an kuma kone gidaje dama a hare-haren ne wadanda aka kai a garin N'Goshe-Sama da kuma Kaigamari ranakun Asabar da Lahadi.
Wani mazaunin garin N'Goshe-Saman, wanda ya tsira daga harin, ya sheda wa BBC cewa 'yan bindigar sun rika bi gida-gida, suna kashe mutane, suna kuma cinna wa gidajen wuta.
Ga cewarsa, kimanin mutane 30 ne aka kashe a N'Goshe-Sama.
Ya ce an fara harbe harbe ne tun karfe goma na daren Asabar har zuwa ran Lahadi da safe.
Ya kuma ce babu wani dauki da jami'an tsaro su ka kaima masu.
An kai harin na biyu ne a kauyen Kaigamari inda aka kashe kimanin mutane takwas, ga cewa wani mazaunin wurin.
Ya ce mutane na zaman fargaba sosai yanzu a kauyen.










