An yi jana'izar mutane 4 da suka mutu a dagwalo a Kano

Asalin hoton,
A Najeriya an yi jana'izar wasu mutane hudu da su ka hallaka a cikin wani dagwalon masana'antu, a wata majema a birnin Kano.
Lamarin dai ya faru ne yau da safe, inda wani da ke aikin kwashe dagwalon da majemar ke tarawa ya fada cikinsa.
Sauran mutanen uku sun rasa rayukansu ne yayin da suke kokarin ceto shi.
Tuni dai wasu lauyoyi a Kanon suka yi barazanar gurfanar da kamfanin a gaban kotu, matukar ya gaza biyan iyalan mutanen cikakiyar diyya.







