Jonathan ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Jos

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai ranar Lahadi a wata majami'a a Jos, babban birnin jihar Filato.
Mista Jonathan ya bayyana cewa harin bam din a matsayin na ta'addanci kana ya ce za su ga bayan 'yan ta'addan da ke kai hare-hare a kasar.
Ya hori 'yan kasar da kada su karaya sakamakon hare-haren bama-bamai da ake kai wa a sassa daban-daban na Najeriyar, yana mai cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen dakile matsalar ta'addanci a kasar.
Harin da aka kai kan majami'ar Saint Finbar's ta Katolika da ke Unguwar Rayfield dai, ya yi sanadiyar mutuwar mutane takwas ne yayin da wasu matasa kuma suka huce fushinsu a kan musulmi da ke Unguwar mai Adiko da ke kusa.






