Yaran Syria masu gudun hijira a Lebanon

A karshen watan Maris kimanin mutanen Syria miliyan daya da dari shida ne ke gudun hijira a makotan kasashe, kuma kusan rabinsu yara ne.

Yaran Syria a cikin wani tanti a Bekaa na Lebanon
Bayanan hoto, Tun fara yakin Syria shekaru biyu da suka wuce, mutane kimanin miliyan daya da dari shida ne suke gudun hijira a kasashen Jordan daTurkiyya da Iraqi da Masar da kuma Lebanon. Kuma yawansu na ci gaba da karuwa kullum. Mai daukar hoto na Magnum, Moises Saman ya hadu da wadannan yara da suka tsere wa rikicin tare da iyalansu.
Haytham da Wassim a cikin tanti
Bayanan hoto, Haytham dan shekaru 7 da kaninsa Wassim dan shekaru 5 na zaune a wani tanti a kwarin Bekaa dake Lebanon.
Wata yarinya 'yar Syria a matsugunin wucin gadi na iyayenta
Bayanan hoto, Wasu iyalan kuma sun samu wasu gine-gine ne wadanda ba a kammala ba, wadanda suke amfani da su a matsayin matsuguni na wucin gadi.
Abd El Rahman dan shekaru 10
Bayanan hoto, Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an yi rajistar kimanin 'yan Syria 400,000 ko kuma suna jiran a yi musu rajista a matsayin 'yan gudun hijira a Lebanon
Wata yarinya 'yar Syria
Bayanan hoto, Gudun hijirar ta dora wani gagarumin nauyi a kan kasar mai hamada kuma yana tasiri a rayuwar yau da kullum da tattalin arzikin al'ummarta.
Wani jariri dan Syria yana barci a tantin iyayensa
Bayanan hoto, Ministan cikin gida na Lebanon Marwan Charbel ya ce hakikanin yawan 'yan gudun hijirar Syria a Lebanon ya kusan miliyan daya. An kiyasta cewa yawan 'yan Lebanon bai fi miliyan hudu ba.
Faysal dan shekaru 6
Bayanan hoto, Hukumomin ba da agaji na Majlisar Dinkin Duniya sun kaddamar da neman taimako mafi girma a tarihin Majalisar--ta nemi tara kudi domin taimakawa da kayan agaji ga Syria da makwabtanta.
Aziz mai shekaru takwas
Bayanan hoto, Majalisar na neman karin miliyan dubu hudu a wannan shekarar, yayin da take tsammanin yawan 'yan gudun hijirar da kuma masu neman taimako a Syria zai yi matukar karuwa.