Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed, Rabiatu Kabir Runka
Rufewa
Masu bibiyar wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Trump ya buƙaci Opec ta rage farashin man fetur
Asalin hoton, EPA
Shugaban maurka Donald Trump ya buƙaci ƙasar Saudiyya da sauran ƙasashen mambobin Opec ta masu arzikin man fetur su rage farashin man, inda ya nanata bazaranar ƙara haraji kan man.
Cikin jawabin da ya gabatar a taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a birnin Davos, shugaban na Amurka ya ce ya yi mamaki yadda ƙungiyar Opec ta kasa rage farashin man fetur tun kafin zaɓensa.
"A yanzu haka wannan farashi ya yi yawa ta yadda yake bayar da damar ci gaba da yaƙin Ukraine'', in ji shi, yana mai cewa ƙarin kuɗin man zai iya taimaka ci gaba da yaƙin daga ɓangaren Rasha, wadda ke gaba-gaba a masu arzikin man fetur a duniya.
"Ya kamata a rage farashin man domin kawo ƙarshen yaƙin, tabbas hakan zai kawo ƙarshen yaƙin,'' in ji shi.
Jawabin sabon shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan zantawarsa da Yariman Saudiyya Muhamad bin Salman ta waya.
Kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun ce Yarima bin salman ya alƙawarta zuba jarin dala biliyan 600 a Amurka cikin shekara huɗu masu zuwa, kodayake sanarwar da fadar White House ta fitar bayan zantawar shugabannin biyu ba ta ambaci waɗannan alƙaluma ba.
'Boko Haram ta ƙara kashe masunta a Borno'
Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla masunta 20 ne ake zargin wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun hallaka a harin da suka kai kan wani ƙauye da ke jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda jami'ai daga yankin suka tabbatar.
Borno na daga cikin jihohin Najeriya da suka fi shan wahala a rikicin Boko Haram da ISWAP, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama da ɗaiɗaita al'umma.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami'i na rundunar ƴan sa-kai ta Civilian Task Force, Modu Ari, na cewa ƴan bindigar sun far wa ƙauyen Gidan Gari ne a jiya Laraba da misalin ƙarfe 11 na safe, inda suka buɗe wuta nan take, lamarin da ya yi ajalin aƙalla masunta 20.
Wani mazaunin yankin, Mustapha Kachallah, ya ce ɗansa na daga cikin mutanen da aka kashe, kuma tuni aka yi jana'izar sama da mutum 15.
Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba kan batun.
Hare-haren mayaƙan Boko Haram masu sari-ka-noƙe na ƙara yawa a baya-bayan nan, duk kuwa da matakan da sojojin Najeriya ke ɗauka a ƙoƙarin daƙile hakan.
A shekarun da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta ayyana yin nasara a kan ƙungiyar.
An yanke wa matar da ta buge jaririya da mota ɗaurin shekara huɗu
Asalin hoton, Hoton da aka samu daga wurin iyalin Mabli
Bayanan hoto, Mabli Cariad Hall ta rasu ne bayan kwana huɗu da buge ta da mota
An yanke wa wata
mata hukuncin ɗaurin shekara huɗu a gidan yari bayan kama ta da laifin buge
wata jaririya ƴar wata takwas da mota, lamarin da ya yi ajalin jaririyar.
Matar mai suna
Bridget Curtis, mai shekara 71 a duniya ta amsa laifin cewa ita ce ta yi sanadin
mutuwar jaririya Mabli Cariad Hall sanadiyyar tuƙin ganganci a yankin
Pembrokeshire na Birtaniya a shekarar 2023.
Jaririya Mabli na
cikin keken jarirai a kusa da mahaifinta ne a wajen wani asibiti, a lokacin da
Curtis ta buge ta da wata mota ƙirar BMW.
A yau Alhamis,
wata kotu da ke yankin Swansea ta yanke wa Curtis ɗaurin shekara huɗu sannan
aka haramta mata yin tuƙi na tsawon shekara takwas.
Jaririya Mabli, wadda
aka haifa a ranar 27 ga watan Satumban 2022 ta ce ga garinku nan a asibitin
yara na Bristol Royal Hospital bayan samun buguwa a ƙwaƙwalwa sanadiyyar buge
ta da mota da aka yi.
Wane hali ake ciki a asibitocin Abuja bayan yajin aikin likitoci ?
Asalin hoton, Abuja National Hospital
An shiga rana ta biyu da fara yajin aikin gargaɗi da likitoci masu neman ƙwarewa suka tsunduma a asibitocin gwamnatin tarayya da ke
Abuja babban birnin Najeriya.
Likitocin sun tsunduma yajin aikin gargaɗin ne kan
rashin biyansu albashi da wasu alawus-alawus da wasu buƙatunsu.
Yajin
aikin ya janyo tsayawar lamura a wasu asibitocin, yayin da wasu kuma ake
gudanar da ayyukan ba yabo ba fallasa.
BBC ta ziyarci asibitocin Asokoro da Wuse, inda wasu jami'an lafiyar da ba su buƙaci a sakaya sunansu sun wa BBc cewa marasa lafiya da dama da kan je asibitin ba sa samun kulawar likitoci, sai dai su tafi asibitoci masu zaman kansu.
To amma an karɓi wasu masu
buƙatar kulawar gaggawa sannan waɗanda ke ɗakuna na musamman wato ICU da
waɗanda suke asibitin tun kafin yajin aikin gargaɗin sun ci gaba da karɓar
magani.
A asibitin Maitama, akwai likitoci da ma’aikatan jinya da
Ungozoma duk a bakin aiki, babu wanda zai fahimci ana yajin aiki a asibitin.
Kuma sun ce lamuran na gudana musamman a yau
Alhamis idan aka kwatanta da ranar farko ta yajin aikin.
Ba wannan ne karon farko da likitoci masu
neman ƙwarewa ke tsunduma yajin aiki a Najeriya ba, yawancin yajin aikin na
kiran gwamnati ta biya musu buƙatunsu musamman tarin bashin albashi da suke bin
gwamnatin, da alawus-alawus, da kyautata walwalarsu da rage aikin da ake
jibgawa likitoci ƙalilan amma suna kula da ɗaruruwan marassa lafiya.
Rasha ta ce a shirye take ta tattauna da Amurka kan yaƙin Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta ce a shirye
take a tattauna da ita ko samun fahimtar juna cikin mutuntawa.
Tana martani ne kan
barazanar takunkumai da Shugaba Donald Trump ke shirin kakaba mata muddin taki
yanjewa da kawo karshen yaki da Ukraine.
Kakakin gwamnatin Putin,
Dmitry Peskov, ya ce suna jira su ga yadda abubuwa za su kasance, sai dai kuma
ba boyayye abu ba ne cewa ba sa tsoron Amurka, kuma babu wani abu sabo a
barazanar takunkumi da Trump ya yi musu.
Wanna na zuwa ne bayan
shi ma mataimakin jakadan Rasha a MDD, Dmitry Polyanskiy, ya ce Kremlin za ta
bukaci sanin abin da Trump ke so kafin ta yanke hukuncin kawo karshen yakin.
Kamfanin Meta ya musanta zargin tilasta wa mutune bibiyar shafin Trump
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Meta ya musanta
bayanan da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ya sa mutane na bibbiyar
shafukan manyan jami’ai a gwamnatin Trump.
Masu amfani da shafin
Facebook da Instagram sun yi ta korafin cewa sun ga suna bin Donald Trump a
ranar Litinnin, haka zalika an tilasta musu bibbiyar shafukan mataimakin
shugaban kasa, JD Vance da matar shugaban kasa, Melania Trump.
Mai Magana a madadin
kamfanin Meta, Andy Stone, ya ce fadar White House ke kula da shafukan mutanen,
kuma sun sabunta su ne domin nuna sabbin mukamansu.
Kuma a cewarsa haka abin
yake a duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati.
Darakta hulda da jama’a
na Meta, Nkechi Nneji, ta fadawa tashar CBS cewa ba sa tilastawa kowanne mutum
bin wasu shafukan mutane.
Netanyahu na fuskantar barazana a gwamnatinsa
Asalin hoton, AFP
Yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza ta jefa firaminista Benjamin
Netanyahu a cikin yanayi na tsaka mai wuya – idan yake tababa kan zabin mutunta
alkawarin zaman lafiya da ya yi wa sabon shugaban Amurka ko kuma buƙatar abokan
haɗakar gwamnatinsa masu tsattsauran ra’ayi da ke son a cigaba da yaƙi.
Bayanai na nuna cewa Netanyahu na fuskantar barazana a
gwamnatinsa, mukarraban nasa dai na ganin kamar an fifita Hamas a yarjejeniyar
don haka suka buƙaci ya cigaba da yaƙi duk da gargadin Donald Trump na ganin an
dawo da zaman lafiya Gabas ta Tsakiya da taimaka wa Isra’ilar wajen faɗaɗa
harkokinta na diflomasiyya.
Ɗaya daga cikin jami’an gwamnatin haɗakar Netanyahu ya yi murabus,
sannan akwai masu barazanar ajiye aikinsu muddin ba a cigaba da wannan yaƙi ba.
Nan da ‘yan kwanaki ake sa ran Isra’ila da Hamas za su koma
tattauna shirya yadda mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar za ta kasance.
Tanzaniya ta tabbatar da sake ɓullar cutar marburg a ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Cibiyar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta Afirka ta ce tana hasashen gwamnatin Tanzaniya za ta nemi allurar riga-kafin cutar a hukumance domin shawo kan matsalar.
Cibiyar ta ce an yi gwaji 31 zuwa yanzu. Mutum gua ne aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon cutar,cikin mutane tara da hukumar lafiya ta duniya, WHO ta bayyana a matsayin waɗanda ake zargin cutar ta kashe.
Shugaban cibiyar ta CDC ya bayyana wa manema labarai cewa, "Dole ne mu amince da sakamakon da muka samu daga Tanzania."
"An gudanar da binciken ne a babban dakin gwaje-gwaje na ƙasar dake Dar es Salaam, wuri mafi aminci a ƙasar"
A ranar 21 ga watan Janairun, 2025, gwamnatin Tanzania ta shawarci matafiya da su dauki matakan ba da cikakken bayani kan lafiyarsu musamman waɗanda suka fito daga arewa maso yamma na yankin Kagera.
IMF zai ba Nijar bashin sama da dala miliyan 51
Hukumomin ƙasar Nijar sun bayyana cewa kwamitin
gudanarwa na asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya amince da rahoton kwamitin da suka aika domin nazari tare da tsara yadda za a gudanar da shirye-shiryen asusun a Nijar.
Wannan dai na zuwa ne bayan amincewa da bayanan da rahoton binciken farko ya yi.
Abubuwan da rahoto na IMF ya ƙunsa sun haɗa da yadda ƙasar ta
Nijar ta samu ci gaba a fanin tattalin arziki da ƙoƙarin hukumomin ƙasar na ɗaukar matakan gyara a fanin domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Hakan ya sa asunsun
ya amince ya samar da wasu kuɗaɗe da jimilarsu ya haura dala miliyan 51
ga ƙasar ta Nijar.
Ukraine ta yi maraba da saƙon Trump ga Putin na kawo ƙarshen yaƙi
Ministan harkokin wajen Ukraine ya ce ƙasarsa na maraba da saƙon Shugaban Ƙasa Donald Trump, inda ya yi barazanar ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumi da riɓanya haraji idan har Putin bai kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar ta Ukraine ba.
"Lallai muna maraba da wannan saƙon na Shugaba Trump," in ji Andriy Sybiha, a lokacin da yake jawabi a taron tattalin arziki na duniya da ake yi a birnin Davos.
"Mun yi amannar cewa Trump zai samu nasaea," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa yana fata Ukraine za ta "kawo sauyi a yanayin amfani da diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin tare da tsara hanyoyin samar da zaman lafiya mai ɗorewa."
Tun da farko, ƙasar Ukraine ta yaba wa Trump, sannan ta ce, "mun shirya shiga tattaunawa domin samar da matsaya mai kyau."
Hotunan yadda Mexico ke gina masauki ga baƙin haure da Trump zai koro daga Amurka
Domin tarbar baƙin haure da Shugaban Amurka Donald Trump zai kora, mahukunta ƙasar Mexico sun fara shirye-shiryen gina gidajen wucin-gadi a kusa da bakin iyakar ƙasar da Amurka.
Daga cikin abubuwan da Trump ya yi yaƙin zaɓe da su akwai yaƙi da kwararar baƙi, musamman masu shigowa ta bakin iyakar Amurka da Mexico, da ma alƙawarin da ya yi na korar baƙi mafi girma a tarihi.
Wannan ya sa ƙasar ta fara gina gidajen domin ba waɗanda aka koro daga Amurka masauki na wucin-gadi da zarar an kore su daga Amurka.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, A birnin Ciudad Juárez da ke jihar Chihuahua, an ga ma'aikata suna aikin gina rumfunan tanti domin tarbar baƙi
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Hoton da aka ɗauka da jirgi mara matuƙi wanda ke nuna yadda ake aiki a Ciudad Juárez da ke birnin El Paso da ke bakin iyakar ƙasashen biyu
'Lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su fara gani a ƙasa'
Asalin hoton, Getty Images
Ministan kula da dabbobi na Najeriya, Alhajij Idi Mukhtar Maiha, ya ce ya kamata ƴan Najeriya su fara gajiya da maganar cewa ƙasar na da damarmaki, inda a cewarsa, lokaci ya yi za ya kamata su fara a gani a ƙasa.
Maiha ya bayyana haka a taron tattaunawa wanda jaridar Daily Trust ta shirya na bana, wanda shi ne karo na 22, inda ya ce ya kamata tsare-tsaren harkokin noma su kawo hanyoyin da za a kawo sauyi kan yadda manoma suke noma kawai domin su ci, sai kaɗan suke sayarwa.
Ya ce akwai buƙatar a canja yadda ake kallon harkokin noma da kiwo a ƙasar, sannan ya ƙara da cewa ma'aikatarsa za ta inganta harkokin kiwo.
Sai dai ya ce matsalar rashin tsaro ta shafi harkokin samar da abinci a ƙasar, sannan ya yi kira da rumgumi harkokin noma a damuna da rani, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai magance ƙarancin abincin, sannan ya rage farashinsa.
A ƙarshe ya yi kira da a magance matsalar rikice-rikicen manoma da makiyaya, inda ya ce ma'aikatansa na aiki tuƙuru domin magance matsalar.
Tun da farko, shugaban kamfanin Media Trust, Malam Kabiru Yusuf ya ce alƙaluma suna nuna cewa akwai damuwa a ɓangaren samar da abinci a ƙasar.
A jawabinsa a wurin taron mai taken: Samar da abinci: Samar da shi da farashi, ya ce "me ya sa ƴan Najeriya suke shan wahalar samun isasshen abinci? dole mu duba batun nan, muna jira mu ji me masana za su ce game da samar da abincin da farashinsa."
An fara kwashe mutane a Los Angeles bayan wata gobara ta kunno kai
Asalin hoton, Getty Images
Wata gobara mai ƙarfi ta sake tasowa a yankin Los Angeles, wanda ta sa aka fara kwashe dubban mutane daga yankin zuwa wani wurin daban.
Gobarar ta taso ne daga kimanin tafiyar mil 45 wato kilomita 72 ta arewa maso yammacin birnin na Los Angeles a ranar Laraba, a kusa da tafkin Castaic mai tsaunuka da dama, kuma akwai gidajen mutane da makarantu a kusa.
Tuni wutar ta faɗaɗa zuwa faɗin murabba'in ƙasa 10,000 a ranar Laraba saboda yanayin iska da buji da ake ciki, duk da cewa har yanzu ba ta kai ga cinye wani gida ko wurin kasuwanci ba, sannan mahukunta na cewa sun yi amannar kashe ta kafin ta munana.
Yankin ya sake faɗawa cikin shirin kar ta kwana ne saboda ganin yadda waccan wutar dajin ta ɗaiɗaita jihar.
Aƙalla mutum 31,000 ne aka ce tilas su bar yankin, sannan an yi wa wasu mutum 23,000 gargaɗin cewa akwai buƙatar su tashi daga yankin na Los Angeles, ciki har da fursunoni 500 da suma aka kwashe aka sauya musu wuri, kamar yadda wani jami'in tsaron, Robert Luna ya bayyana.
Shugaban hukumar kashe gobara ta Los Angeles, Anthony Marrone ya ce ma'aikatansa suna aiki tuƙuru domin shawo kan gobarar, inda ya ce, "mun kashe kusan kashi 15 na wutar zuwa safiyar Alhamis."
Hukumomi a jihar na cewa wannan wutar ta bambanta da na'ukan wutar dajin da aka fuskanta kwanakin baya, inda aƙalla mutum 28 suka rasu, sannan sama da gidaje 10,000 suka lalace.
Ƙara kuɗin kira da na data rashin adalci ne- NLC
Asalin hoton, NLC
Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi kira ga ƴan Najeriya su fara shirye-shiryen dakatar da amfani da kamfanoninin sadarwa domin nuna adawarsu ga amincewa da ƙarin kashi 50 na kuɗin kira da data da gwamnatin tarayya ta yi.
A wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, ta ce ƙarin kuɗin rashin adalci ne ga ƴan ƙasar, waɗanda a yanzu haka suke fuskantar ƙalubale saboda matsin tattalin arziki.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana damuwarsa kan ƙarin, inda ya ce, "wannan matakin, wanda ya zo a daidai lokacin da ma'aikata da sauran ƴan ƙasa suke fama da matsin tattalin arziki, tamkar ba kamfanonin sadarwar wuƙa da nama su yi yadda suke su da ƴan ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
"Harkokin sadarwa na cikin abubuwa masu muhimmanci domin sadarwa da neman labarai. Kuma ko a yanzu ma ƙaramin ma'aikacin Najeriya yakan kashe kusan kashi 10 na albashinsa wajen sayan katin waya da data. Misali ma'aikacin da ke karɓar albashin naira 70,000, idan yana kashe naira 7,000 ne, yanzu zai fara kashe kusan naira 10,500 ne a waya."
Ya kuma caccaki gwamnatin bisa yadda ta amince da ƙarin cikin gaggawa, amma ta ɗauki dogon lokaci kafin ta amince da mafi ƙarancin albashi.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a yankin Jenin
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce ta kashe ƴanbindiga biyu da take zargi da kashe ƴan Isra'ilawa uku a gabar yamma da tekun Jordan a farkon wannan watan da muke ciki.
Ta ce dakatunta sun Qutaiba Shalabi da Mohammed Nazzal ne bayan musayar wuta da su a daren ranar Laraba a Burqin da ke arewacin gaɓar yamma da tekun Jordan.
Ma'aikatar lafiyar mutanen yankin Falasɗinu ta ce sojojin Isra'ila sun tafi gawarwakin mutane, sannan sun rushe gidan da suka zama.
A nata ɓangaren, Hamas ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana cewa waɗanda aka kashe ɗin mayaƙanta.
Isra'ila dai ta zafafa hare-hare a yankin Jenin ne tun daga ranar Talatar da ta gabata, inda zuwa yanzu rahotanni suka nuna an kashe mutanen yankin aƙalla 12, ciki har da Shalabi da Nazzal, sannan an raunata gommai.
Isra'ila ta ce akwai wata ƙungiyar ƴanbindiga da take so ta fatattaka a yankin, domin hana ta kai mata hare-hare.
Sai dai daga cikin waɗanda aka kashe, rahotanni na cewa akwai fararen hula, kamar Ahmed al-Shayeb, wanda mutanen yankin suka sanannen mai shagon sayar da wayar hannu ne, kuma ba mayaƙi ba ne.
Yara dubu 250 a Zamfara na fama da tamowa - Unicef
Asalin hoton, Getty Images
Asusun kula da ilimin ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce akwai yara dubu 250 da ke fama da matsananciyar yunwa daga cikin yara miliyan 1.2 da aka yi nazari a kansu a jihar Zamfara.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa wakiliyar asusun na Unicef, Cristian Munduate ce ta faɗi hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Gusau na jihar ta Zamfara ranar Wednesday.
Misis Munduate ta ce a duk yara 10 da ke jihar ɗaya na fuskantar barazanar mutuwa inda kuma yawan yaran da ke fama da matsalar girma ƴan wata ɗaya zuwa shekaru biyar na ƙaruwa inda suka kai kaso 45.2 cikin 1000.
Ministan tsaron Nijar ya ce dakarun AES sun kusa fara aiki
Asalin hoton, Burkina Faso Presidency
Ministan tsaron ƙasar Janar Salifou Modi ya ce rundunar tsaro na ƙasashen AES sun kusa fara aikin haɗin gwiwa domin tabbatar da tsaron ƙasashensu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da sakamakon
ayyukan tsaro na tsawon wata 18 da suka yi kan ragamar
milkin ƙasar bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum a watan
Yulin 2023.
Kazalika ya ambato wasu matsalolin da suka haɗa da yadda ya ce ƙasar Benin da wasu ƙasashen Turai sun kame wa Nijar wasu motoci da jirage da
sauran kayan yaƙi da Nijar ɗin ta yi sayo daga ƙetare.
Sheikh Sharif Saleh ya buƙaci gwamnati ta yaƙi talauci da rashin tsaro
Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Sharif Ibrahim Saleh ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta yi dokoki tare da ɗaukar matakan da za su magance matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro.
Shehin malamin ya bayyana haka a jiya Laraba a gidansa da ke Abuja, inda ya ce lallai akwai buƙatar gwamnatin ƙasar ta yi ƙoƙarin da za ta yi domin tabbatar da hakan, sannan ya yi kira ga samun haɗin kai tsakanin ƴan ƙasa, wanda ya ce sai da shi ne za a samu ci gaba mai dorewa.
Ya ce dukkan ƴan Najeriya suna da rawar da za su taka domin ciyar da ƙasar gaba.
Shehin malamin ya kuma yi godiya ga Jami'ar ABU da ke Zariya bisa ba shi digirin girmama, inda ya ce, "hakan ya nuna cewa ana girmama gudunmuwar da malaman addinni ke bayarwa wajen gina ƙasa."
Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar masu riƙa madafun iko su riƙa sauraron buƙatar mutane, sannan ya ce Allah ya san dalilin da ya hada mu a matsayin ƴan ƙasa ɗaya a Najeriya.
Ƴan Syria masu komawa gida na fargabar bama-bamai da aka binne a ƙasa
Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.
Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito.
Jami'an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu.
Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau'in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba, sun fi sauƙin sha'ani, sannan ya ce tsakanin Nuwamban bara zuwa 3 ga Janairu sun ctsince aƙalla bama-bamai 822.