Yadda rashin lantarki ya jefa sassan Abuja cikin duhu

Asalin hoton, Getty Images
A daidai lokacin da aka cika mako ɗaya da wasu sassan birnin Abuja ke fama da matsalar rashin wutar lantarki, wasu al'umomin yankunan da matsalar ta shafa na kokawa kan halin da matsalar ya jefa su ciki.
A makon da ya gabata ne kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya, TCN ya ce za a fuskanci matsalar rashin wutar a wasu sassan Abuja, babban birnin ƙasar, sakamakon lalata wasu manyan wayoyin taransifoma da wasu ɓata-gari suka yi.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar 17 ga watan Janairu ya ce an lalata wayoyoin ƙarƙashin ƙasa da ke kai wuta zuwa unguwar tsakiyar ƙwaryar Abuja da kewaye, lamarin ya yi sanadiyyar katsewar wutar a wasu unguwannin yankin.
Sanarwar kamfanin ta zayyano unguwannin da lamarin ya shafa da suka haɗa da Maitama da da Wuse da Jabi da Life Camp da Asokoro da Utako da Mabushi da wasu sassan fadar shugaban ƙasa da ke Villa.
Sai dai kamfanin ya ce tuni injiniyoyinsa suka duƙufa don ganin sun gyara matsalar.
Lamarin ya ja hankalin mutane, musamman na cikin Abuja da wasu jihohin, inda wasu suke mamakin yadda babban birnin ƙasar ya faɗa cikin duhu, har ya ɗauki tsawon lokaci ba tare da an magance ba.
'Halin da muka shiga'

Asalin hoton, Getty Images
Mazauna wasu unguwannin da BBC ta zanta da su, sun koka kan irin asarar da suka ce suna yi sakamakon rashin wutar, har na tsawon mako guda.
Wata mazauniyar unguwar Maitama, wadda BBC ta zanta da ita, ta ce lamarin rashin wutar ya jefa su cikin tasku da taƙaici.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce a cikin mako guda da ya gabata, ranar Lahadin da ta gabata ne kawai suka samu wutar lantarki, ita ma a cewarta, ba ta wuce sa'a guda ba aka ɗauke, sannan tun daga lokacin har yanzu ba su sake ganin lantarkin ba.
''Yanzu sai dai mu tayar da inji, jifa-jifa. Mukan kunna shi da safe domin tafasa ruwan yi wa yara wanka, idan sun tafi makaranta a kashe, sai kuma da yamma wajen ƙarfe 6:30pm a sake kunnawa zuwa 12:00 na dare sannan a kashe."
Matar - wadda ta buƙaci kada a ambaci sunanta - ta ce sukan saya man dizel lita 200, amma da ƙyar yake yi musu kwana uku.
''Muna kunnawa da safe, sannan mu kunna da dare. Idan mun yi hakan ne lita 200 na man dizel ɗin zai yi mana kwana uku."
Haka kuma gidaje da dama sun koka kan yadda kayan miya da sauran abubuwan - da suke taskancewa a firinji - ke lalacewa sakamakon rashin lantarkin.
A nasa ɓangaren, Abubakar mai wanki da guga wanda yake sana'arsa a yankin Jabi da ke Abuja, ya ce lamarin ya jawo masa asara, sannan ya sa aikinsa na ƙara wahala.
A cewarsa, "idan akwai wuta, nakan iya goge kaya tsakanin 30 zuwa 40 a rana bayan na yi wanki da safe. Amma yanzu aboda rashin wutar nan, dole da dutsen guga na gawayi nake amfani, inda kuma da ƙyar nake iya haɗa kaya 15 zuwa 20," in ji shi.
Abubakar ya ƙara da cewa bayana asarar kuɗi, amfani da gawayin ba daɗi, sannan yana jawo musu cunkso saboda ba sa iya kammala aikin cikin sauri.
NLC ta buƙaci ministan makamashi ya sauka

Asalin hoton, NLC
A nata ɓangaren, ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, ta yi kira ga Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu da ya sauka saboda yawaitar katsewar babban layin lantarki na ƙasa.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya fitar, ya ce ƙungiyar na takaicin yadda ɓangaren lantarkin Najeriya ya ƙi gyaruwa.
Ajaero ya ce, "idan har akwai ma'aikata ƙwararru waɗanda suka san makaman aiki a ma'aikatar makamashi, to lallai za a iya kiyaye yawaitar abin kunyar nan da ake fuskanta na yawaitar katsewar layin lantarki a Najeriya. Magance matsalar ya kamata ministan ya yi, ba tiƙa maganar cewa za su magance ta ba.
"Mun yi amannar cewa wannan na nuna rashin ƙwarewa da gazawar ma'aikatar makamashin, wanda hakan ya sa muke mamakin me ya sa wanda ke jagorantar ma'aikatar ba zai sauka cikin mutunci ba."
Ajaero ya kuma caccaki ministan bisa kasafta kashe naira biliyan 8 a kasafin kuɗin 2025 domin "wayar da kan ƴan Najeriya muhimmancin biyan kuɗin lantarki."
Yawan faɗuwar babban layin lantarki

Asalin hoton, Getty Images
Babban layin wutar lantarki na Najeriya yana yawan fuskanci matsalar lallacewa, inda a shekarar da ta gabata ya faɗi har sau 12, wani abu da ya haifar da ƙorafi da koke daga 'yan ƙasar da ƙungiyoyin fararen hula.
Rashin wutar lantarki a Najeriya, matsala ce da ta jima tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda gwamnatocin ƙasar da dama suka sha alwashin magance matsalar, amma har yanzu ta gagari kundila.
Batun samar da wutar lantarki ya kasance babban maudu'i ko manufofin yaƙin neman zaɓen ƴan siyasa a Najeriya, inda suke alƙawarin kawo ƙarshen matsalar amma har yanzu jiya-i-yau.
Ko a farkon makon da muke ciki ma, sai da kamfanin Sunrise Power ya shigar da tsoffin gwamnatocin Najeriya ƙasa a wata kotu da ke birnin Paris na ƙasar Faransa kan zargin rashin cika yarjejeniyar kwangilar da ya shiga da Najeriya kan samar da wutar lantarki daga tashar Mambila.











