An ga watan Zulhijja a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar ya ayyana Laraba, 28 ga watan Mayun 2025 a matsayin ɗaya ga watan Zulhijjan shekara ta 1446 bayan Hijira.
Mai alfarman, wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli ta addinin Musulunci a Najeriya ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, wadda ta samu sa hannun babban mashawarci ga sarkin Musulmin kan harkokin addini, Farfesa Sambo Wali Junaidu.
Wannan sanarwa na nufin za a hau idin babbar sallah a Najeriyar a ranar Juma'a 10 ga watan na Zulhijja, wadda ta yi daidai da shida ga watan Yunin 2025.
Hakan ya zo daidai da ganin watan ƙasar Saudiyya, wadda tun farko ta ayyana Laraba a matsayin ɗaya ga watan na Zulhijja, tare da cewa za a hau Arfa a ranar Alhamis, biyar ga watan Yuni.
Zulhijja shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci kuma an kwaɗaitar da Musulmai wajen yin ibadu a cikinsa domin samun albarka.
A cikin watan ne kuma ɗimbin al'ummar Musulmi daga faɗin duniya ke taruwa a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji, wanda ɗaya ne daga cikin ginshiƙan addinin na Musulunci.


















