Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 10/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 10 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Abin da ya sa na koma APC - Gwamnan Zamfara

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma shari’o’in da suka dabaibaye tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne babban dalilan da suka sa ya fice daga jam'iyyar zuwa APC.

    A ranar Litinin ne gwamnan ya sanar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC a hukumance bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

    A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ficewar gwamnan zuwa APC ya zama dole saboda muradun al’ummar Zamfara.

    Sanarwar ta ce gwamnan ya ɗauki matakin komawa APC ne bayan shawarar masu ruwa da tsaki a jihar, musamman duba da matsalolin shari’a da jam'iyyar PDP ke fuskanta a halin yanzu.

    Gwamna Dauda Lawal ya ce ya yi baƙin ƙoƙarinsa don ganin ya sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin jam’iyyar domin tabbatar da haɗin kai da kuma damar tsayar da ƴan takara a zaɓuka masu zuwa.

    “Amma ƙoƙarin samar da zaman lafiya da sasanci ta hanyar sulhu bai yi nasara ba, lamarin da ya haifar da jerin shari’o’i da ka iya yin tasiri ga ‘yan siyasar da za su nemi takara a zaɓen shekarar 2027.” in ji sanarwar.

    Ficewar Dauda Lawan daga PDP na zuwa ne mako guda byan ficewar gwamnan Adamawa daga PDP zuwa APC, inda a yanzu jam'iyyar na da gwamnoni 2 kacal, inda APC ke da 31.

  2. Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasarta kan yiwuwar hari a Najeriya

    Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da sanarwar tsaro inda ya gargaɗi ‘yan kasarsa kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyinta da kuma makarantu masu alaka da ƙasar a fadin Najeriya.

    A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar Amurka ko kuma cibiyoyin da ke da alaka da kasar.

    Sanarwar ta ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Legas, inda aka buƙaci ‘yan kasar su kasance cikin lura tare da ɗaukar ƙarin matakan tsaro idan za su je waɗannan wurare.

    Ofishin jakadancin ya ce "yana da muhimmanci mutane su riƙa canza hanyoyin tafiya da lokutan da suke fita, su guji yin abu iri daya a kai a kai, tare da kasancewa masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallinsu domin rage haɗarin da ka iya tasowa."

    Sanarwar ta ce: “Ya kamata ‘yan Amurka su ɗauki ƙarin matakan tsaro idan suna tafiya zuwa ofishin jakadancin ƙasar da ke Abuja, ko ƙaramin ofishin jakadancin ƙasar da ke Legas, da kuma makarantu masu alaka da Amurka.”

    Haka kuma sanarwar ta shawarci ƴan ƙasar da su guji cunkoson jama’a ko zanga-zanga, sannan su sake duba tsare-tsaren tsaron kansu tare da iyalansu.

    Sauran matakan kariya da ofishin ya bayar sun haɗa da tabbatar da cewa wayoyin hannu suna da caji idan wani lamarin gaggawa ta taso, da kuma sanin hanyoyin fita na gaggawa idan aka shiga wani gini.

  3. Kasuwannin mai sun fara farfaɗowa bayan kalaman Trump na kawo ƙarshen yaƙin Iran

    Kasuwannin mai da hannayen jari sun yi armashi sakamakon tabbacin da Trump ya bayar na kawo karshen yankin Iran nan kusa.

    Farashin gangar ɗanyen man fetur ya fadi zuwa dala casa'in.

    Hannun jari a kasuwannin Asiya sun farfaɗo, idan aka kwatanta da irin asarar da aka tafka a ranar Litinin.

    Sai dai har kawo yanzu babu wani abu a kƙasa da ya sauya, domin har yanzu jiragen ruwa ba sa iya ratsa mashigin Hormuz.

    Trump ya ce taɓarɓarewar farashin mai da kuma faɗuwar kasuwar hannun jarin bata kai yadda ake ta faman zuzutawa ba.

    Sai dai ya sake tsokaci kan yadda hakan ya janyo tashin farashin kayayakin masarufi a cikin gida.

    Trumo ya yi alƙawarin sassauta takunkumin cinikayyar da ya sanya wa wasu kasashe don wadata yan kasar da abubuwan da suke bukata.

  4. Trump ya nuna damuwa kan ci gaba da rufe mashigin Hormuz da Iran ke yi

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana takaicinsa game da ci gaba da rufe mashigin Hormuz da Iran ke yi.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya yi barazanar kai wa Iran hari mafi muni idan ba ta buɗe mashigin ba.

    A baya ya ce hare-haren Amurka da Isra'ila ke kai wa basu shafi kayayyakin more rayuwa na Iran kamar wutar lantarki da cibiyoyin man fetur ba, amma hakan na iya sauyawa.

  5. Iran na ci gaba da luguden wuta kan Isra'ila da sansanonin Amurka

    Iran na ci gaba da yin luguden wuta kan Isra'ila da sansanonin Amurka da kuma wasu ƙasashen gabas ta tsakiya, a wani martani ga hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata.

    A Bahrain, mahukunta sun ce wuta na ci gaba da ci a babbar matatar man ƙasar, lamarin da ya sa kamfanin man ƙasar ya ayyana wata doka ta yarjejeniyar ƙin daukar asara tsakaninsa da abokan hulda, a yayin da aka shiga wani yanayi na bala'i.

    A Isra'ila, an tabbatar da mutuwar mutum guda, da jikkatar wasu da dama sakamakon makamai masu linzamin da Iran din ke ci gaba da harbawa.

    Shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Leo ya roki a kai zuciya nesa, yana cewa galibi tasirin yakin na karewa ne a kan 'yan ba ruwana.

  6. Iran ta yi watsi da ƙudirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin ƙasar

    Rundunar juyin juya halin Iran ta yi watsi da kalaman Shugaba Trump na cewa yakin da Amurka da Isra'ilar suka kaddamar kan Iran din ya kusa zuwa karshe.

    Kalaman na zuwa ne a yayin da shugaba Trump ya shaidawa mahalarta wani taro a Florida cewa Amurka ta samu gagarumar nasara a yaƙin, don haka akwai yiwuwar kawo karshensa nan kusa.

    Da yake jaddada dalilin kai harin, shugaban na Amurka ya ce Iran tana shirin kai hari kan Amurka, ba tare da ya bayar da wata kwakkwarar shaida ba.

    Ya ƙara da cewa Iran ɗin ta yi ta ƙoƙarin sake farfado da shirinta na Nukuliya.

    Da yake amsa tambaya a kan ko Amurka za ta kai hari kan sabon jagoran adddinin kasar Ayatollah Mojtaba Khamenei, Trump ya ce ba abu ne da ya kamata ya furta ba, ko da yake ya bayyana rashin jin dadinda kan zabin na sa.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.