Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ƙananan yara ke yin mura a kai-akai?
- Marubuci, Aisha Salisu Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Yawan mura a cikin ƙananan yara na ɗaya daga cikin matsalolin da ke damun iyaye musamman a lokacin damina ko canjin yanayi.
Duk da cewa mura ba cuta mai tsanani ba ce a mafi yawan lokuta, rashin kulawa na iya haifar da matsaloli kamar rashin cin abinci da bushewar hanci, ko matsalolin numfashi.
A tattaunawar da BBC ta yi da Dr. Hadiza Musa, ƙwararriyar likitar yara a Kano, ta ce akwai dalilai daban-daban da ke sa yara ƙanana su na yin mura akai-akai.
"Ƙananan yara musamman waɗanda ba su wuce shekaru biyu ba, suna da tsarin garkuwar jiki da ba shi da cikakken ƙarfin kare kansu daga ƙwayoyin cuta. Wannan yasa suka fi saurin kamuwa da mura idan aka kwatanta da manya yara."
Dalilan yawan mura a ƙananan Yara
Dr. Hadiza ta bayyana wasu daga cikin dalilan da ke sa yara su na yawan yi mura kamar haka;
- Rashin cikakken garkuwar jiki
Yara ƙanana ba su da cikakken tsarin garkuwar jiki, musamman idan ba a yi musu allurar rigakafi gabaɗaya ba.
- Rashin tsafta
Yara ƙasa da shekara biyu suna da yawan saka hannunsu a baki da kuma tsintar abubuwa a ƙasa suna sakawa a baki, wannan shine babban dalilin da ke haifar da mura a ƙananan yara, akwai kuma rashin wanke hannu da tsaftar muhalli wanda suma ke haifar da yawan mura a yara saboda haka, yana da matuƙar muhimmanci a riƙa wanke wa yaro hannu kuma a koya musu wanke hannayensu in ji Dr. Hadiza.
- Sauyin yanayi
Sauye-sauyen yanayi musamman daga sanyi zuwa zafi ko daga ruwan sama zuwa iska mai sanyi na iya haifar da mura.
- Hulɗa da mutane da yawa
Yara da ke zuwa wurin taro ko makaranta suna fuskantar ƙarin haɗarin kamuwa da mura saboda hulɗa da yara da yawa.
- Fitar haƙori
Yawanci iyaye suna yawan alƙanta yawan mura a yara da fitowar haƙori a al'adance shiyasa na ba da wannan dalilin. Lokacin da wasu yara ke fara fitowa da hakori, gumi da majina na ƙaruwa, wanda ke sa hanci ya toshe sai kuma su fara mura. Wasu kuma in ji likitar, duk lokacin da haƙori zai fito, ana ganewa ne ta muran da suka yi.
- Yanayin abinci
Likitar ta ce yara da ake bai wai abinci mai ɗumi sosai ko mai sanyi sosai ko ruwa mai sanyi, ko lemun yara mai sanyi da dai sauransu na iya janyo mura.
Hanyoyin magance yawan mura
Likitar ta ce yayin da yara suka fara mura, akwai hanyoyi da iyaye za su bi wajen rageta ko magance ta.
Hanyoyin sun haɗa da;
- Shan ruwa da yawa
Liktar ta ce ruwa na taimakawa wajen sauƙaka kumburin a maƙogwaro da toshewar hanci da hana bushewa.
- Ganin likita da shan magungunan da likita ya bayar
Kada iyaye su yi amfani da magungunan mura na manya ga yara ƙanana kamar yadda iyaye mata ballantana hausawanmu suka saba in ji Dr. Hadiza.
Tsaftace muhalli
Liktar ta ce a dage wajen yawan wanke wa yara hannu kuma a koya musu yadda za su wanke hannu a kai- a kai musamman kafin cin abinci da bayan dawowa daga waje.
- Barin yara su huta
Kula da hutun yara da ƙarancin damuwa yana taimakawa wajen warkar da mura in ji likitar.
- Sakawa yara kayan da suka dace
Tabbatar da cewa yara suna sanye da kayan da suka dace da yanayi.
- Rigakafi
Bibiya da kai yara a yi musu allurar rigakafi kamar yadda ake ba da shawara a asibitoci na da matuƙar muhimmanci in ji likitar.
- Bai wa yara abinci mai gina jiki da ruwa
Dr. Hadiza ta ce ba yara abinci mai gina jiki da isasshen ruwa don karfafa garkuwar jiki na da muhimmanci sosai.
Matsalar yawaita bai wa yara maganin mura
Dr. Hadiza ta yi gargadi kan yadda wasu iyaye ke yawan bai wa yara maganin mura ba tare da izinin likita ba.
"Muna ganin yadda wasu iyaye idan suka lura yaransu sun fara mura, sai su je su siya maganin mura a kanti ko a shago, su durawa yaron ba tare da sanin ko ya dace ba.
Wannan ba kawai ba ya magance mura ba, har ma zai iya haifar da matsaloli ga yara kamar rashin narkewar abinci da matsalolin ciki, ko tsananta yanayin mura.
"Magungunan mura da aka tsara ga yara manya ba su dace da yara ƙanana" in ji ta.
Dr. Hadiza ta shawarci iyaye da su kasance masu hakuri, su lura da alamu, kuma idan mura ta wuce kwanaki biyu zuwa uku ko ta haɗu da zazzabi mai tsanani, sai a nemi likita:
"Iyaye su sani cewa mura na iya kama yaro akai-akai amma mafi yawan lokuta ba cuta mai tsanani ba ce.
Dr. Hadiza ta ce abin da ya fi muhimmanci shine lura da alamu kamar zazzaɓi mai tsanani, wahalar numfashi, ko rashin cin abinci, domin waɗannan na iya nuna matsala mai tsanani.