Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Hare-hare 6 da Iswap ta kai wa sansanonin soji a Borno cikin mako ɗaya'
Ƙungiyar ISWAP ta masu tayar da ƙayar baya a Najeriya ta ɗauki alhakin kai jerin hare-hare kan sansanonin sojin Najeriya a jihar Borno cikin mako guda, tare da kashe sojoji da dama.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta hannun kamfanin dillancin labarai na Amaq mai alaƙa da Iswap ɗim, ta ce ta ƙaddamar da hare-haren a cikin makon da ya gabata.
Wasu kafofin yaɗa labaran Najeriya sun bayar da rahoton wasu daga cikin waɗannan hare-hare, kodayake alƙaluman sojojin da suka mutun ya sha bamban da iƙirarin ƙungiyar ta ISWAP.
Sai dai a wani salo da ba a saba gani ba ƙungiyar ta bayar da rahoton mutuwar mayaƙanta da dama a gumurzu da jami'an tsaro a lokacin hare-haren
Ƙungiyar ta yi iƙirarin kai hari sansanonin soji har guda huɗu a cikin dare ɗaya, lamarin da ta ce ya yi sanadin mutuwar sojoji.
Sai dai wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato sojojin ƙasar na cewa sun samu nasarar daƙile hare-haren mayaƙan na Iswap a wasu sansanonin da ke jihar ta Borno.
Hotunan da Amaq ta fitar tare da sanarwar sun nuna yadda gine-gine da motocin soji ke ƙonewa da suka yi iƙirarin ƙwata a harin Marte.
Hare-haren da ƙungiyar ta yi iƙirarin kaiwa
Konduga
Amaq ta ruwaito cewa ISWAP ta ƙaddamar da "jerin hare-hare" kan sansanonin soji da ƙungiyar JTF mai aiki da sojoji, inda ta kai hari gidan kwamandan ƙungiyar da ke garin na Konduga.
A hari kan sansanin sojin da ke Konduga, ƙungiyar ta Iswap ta yi iƙirin kashe wani babban jami'in soji da wasu ƙananan sojoji biyu, tare da ƙona sansanin da wasu motocin soji 11, sannan ta yi iƙirarin ƙwace babaru 68 a sansanin.
Haka ma ƙungiyar ta yi iƙirarin ƙona wani ofishin ƴansanda da ke garin tare da kashe jami'ai huɗu.
Mai bincike kan ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya, Zagazola Makama.
Marte
Kamfanin dillancin labaran na Amaq ya kuma ce mayaan Iswap sun addamar da hari kan sansanin soji da ke Marte tare da wace iko da wasu sassan sansanin.
A nan ma ungiyar ta yi iirarin kashe jami'an soji uku tare da raunata wasu, da kuma ƙona motocinsu na yaƙi.
Amaq ya kuma ambato ƙungiyar na cewa ta ƙwace makamai masu yawa da motocin soji biyu daga sansanin.
Sai dai a harin na Marte ƙungiyar ta ce an kashe mayaƙanta da dama sakamakon mayar da martanin sojojin sama.
Jakana
Ƙungiyar ta kuma yi iƙirarin kai wasu jerin hare-hare a ranar 5 ga watan Maris ciki har da garin Jakana.
Iswap ɗin ta ce a garin na jakana ta ƙona sansanin soji tare da kashe sojoji uku.
Garin Jakana na yankin ƙaramar hukumar Konduga na kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu zuwa Kano.
Mainok
Haka ma ƙungiyar ta yi iƙirarin kai wa sansanonin soji da ke gari Mainok hari tare da kashe wasu sojoji.
Iswap ta ce ta kwashi makamai masu yawa a sansanin sojin lokacin harin.
Garin Mainok na yankin ƙaramar hukumar Kaga, kuma garin na kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Kawuri
A sanarwar ta Iswap din ta fitar ta kuma yi iƙirarin kai hari kan sansanin soji da ke garin Kawuri.
A lokacin harin ƙungiyar ta yi iƙirarin amfani da manyan makamai wajen lalata wata motar yaƙi ta soji.
Kawuri wani ƙaramin gari ne da ke yankin ƙaramar hukumar Konduga, mai nisan kilomita kimanin 40 daga kusu maso gabashin birnin Maiduguri.
Dalori
Ƙungiyar ta Iswap ta kuma iƙirarin kai hari kan sansanin soji da ke garin Dolari.
Iswap ta yi iƙirarin korar sojojin da ke sansanin kafin cinna masa wuta, kamar yadda Amaq ya ruwaito.
Shi ma dai Dolari wani ƙaramin gari ne a yankin ƙaramar hukumar Konduga, mai tazarar aƙalla kilomkta 15 daga birnin Maiduguri.
'Ba ta ɗauki alhakin harin Ngoshe ba'
Sai dai ƙungiyar ba ta ɗauki alhakin mummunan harin garin Ngoshe ba, wanda ya yi sanadin kisan mutane da dama da yin garkuwa da fiye da 100.
A ranar 4 ga watan Maris ne rahotonni suka ce ƴanbindiga sun kai hari garin na Ngoshe inda suka kashe limamin garin da wasu ƴangudun hijira, tare da ƙwace ilahrin gari.
Kodayake daga baya wani bidiyo ya ɓulla inda mayaƙan Boko Haram suka ɗauki alhakin harin.
Me ne gaskiyar iƙirarin na ISWAP?
Tuni dai kafofin yaɗa labaran Najeriya sun tabbatar da wasu, yayin da su ma sojojin ƙasar suka tabbatar da wasu ta hanyar sanarwar da suke fitarwa.
Haka kuma BBC ta tuntuɓu Dr Kabiru Adamu shugaban Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, mai nazarin tsara a yankin Sahel, wanda kuma ya tabbatar da hare-hare.
''Daga bayanan da muke samu da kuma waɗanda sojojin Najeriya suka fitar, tabbas an kai waɗannan hare-hare'', in ji shi.
Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da iƙirarin yawan sojojin da ƙungiyar ta ce ta kashe ko makaman da ta ƙwace ba.
Me ya sa Iswap ta zafafa hare-haren?
Dr Kabiru Adamu ya ce duk da cewa ƙungiyar ta saba zafafa hare-hare a irin wannan lokaci a baya, amma ya ce ba a samu lokacin da ta zafafa hare-hare kamar yanzu ba.
Masanin harkokin tsaron ya alaƙanta ƙaruwar hare-haren ƙungiyar kan abubuwa guda uku.
''Na farko shi ne sabon gangamin da ƙungiyar ta ƙaddamar a baya-bayan nan mai taken ''ƙona sansanonin soji'' da ta sanya a gaba'', in ji shi.
Abu na biyu a cewar Kabiru Adamu shi ne sanarwar da uwar IS ta fitar a watan Febrairu inda ya taba wa reshen ƙungiyar da ya yi yunƙurin kai hari filin jirgin saman Nijar.
''Wannan ya ƙarfafa wa rassan ƙungiyar da ke ƙasashe daban-daban gwiwa wajen neman samun yabo da taimako da samun ƙarin girma daga uwar ƙungiyar'', kamar yadda ya ce.
Shugaban kamfanin na Beacon Security ya ce abu na uku da ya sa Iswap ta zafafa hare-hare shi ne yadda Najeriya ta shiga ƙawancen tsaro da Amurka.
''Wanann ya ƙara bai wa irin waɗannan ƙungiyoyin ƙarfin gwiwar zafafa hare-hare, saboda ana nuna cewa Shugaba Trump ya shiga yaƙin ne saboda addini, kuma dama su waɗannan ƙungiyoyi suna iƙirarin faɗa domin addini'', in ji shi.
Jihar Borno da ke kudu maso gabashin Najeriya ta shafe shekaru tana fama da hare-haren mayaƙa masu iƙirarin jihadi.