Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 09/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 9 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Hare-haren Iran sun yi ajalin mutum ɗaya tare da jikkata wani a Isra'ila

    Hukumar bayar da gajin gaggawa ta Isra'ila ta ce wani mutum ya mutu, yayin da wasu biyu kuma suka jikkata a tsakiyar kasar, a yayin da Iran ke ci gaba da kai hari a yankin.

    Sojojin Ira'ila sun zargi Tehran da amfani da bama-bamai masu ƴaƴa. Wakiliyar BBC ta ce wannan ne karon farko da aka samu wani hari mai muni da Iran ta kai Isra'ila cikin kusan mako guda.

    Na'urorin kare sararin samaniya na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato da ke gabashin tekun Mediterrian sun kakkabo wasu makamai masu linzami na Iran waɗanda suka shiga sararin samaniyar Turkiyya a karo na biyu.

    Hukumomi a Bahrain sun ce aƙalla mutum talatin da biyu ne suka jikkata a wani harin da Iran ta kai a kudancin babban birnin ƙasar Manamah.

    Qatar ma ta ce ta harbo wani makami mai linzami na Iran.

  2. Mayaƙan Kurɗawa: Dabar da mata zalla ke jagoranta a asirce

    Yayin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai, a Iran ana ci gaba da raɗe-raɗin cewa ƙungiyoyin Kurɗawan Iran masu ɗauke da makamai da ke zaune a Iraƙi za su tsallaka ƙasar domin shiga yaƙin da Jamhuriyar Musulunci.

    A matsayin martani, Iran ta ƙaddamar da hare-hare masu yawa kan ƙungiyoyin Kurɗawan, ciki har da na makami mai linzami wanda ya kashe wani mayaƙin kungiyar ɗaya.

    Sai dai a wani jawabi da ya yi ranar Asabar, Shugaba Trump ya ce ba ya son Kurɗawan su shiga cikin yaƙin.

  3. Rufe mashigar Hormuz ya fara tasiri a ƙasashen Afirka

    Ƙasashen Afirka da dama, musamman waɗanda ke dogaro da shigar da mai daga ƙasashen wajen, sun soma jin tasirin tsaikon da aka samu na fitar da mai ta mashigar Hormuz.

    Wakiliyar BBC ta ce darajar kuɗaɗen Afirka ta Kudu da Masar sun faɗi a kwanakin baya bayan nan, a yayin da ake fargabar samun hauhawar farashin kayayyaki.

    Gwamnatoci a yankin Asiya na ci gaba da kokarin ganin sun rage tasirin yakin kan tattalin arzikinsu da ƴan kasar. Bangladesh ta rufe dukkanin jami'ointa daga yau Litinin, a wani mataki na rage amfani da lantarki da man fetir.

    A ƙasar Philippines kuwa, gwamnatin ƙasar ta sanar da rage kwanakin aiki zuwa kwanaki huɗu kacal a mako.

  4. Ministocin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki sun yi taro kan yaƙin Iran

    Ministocin kuɗi na ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ta G7 suna gudanar da wani taron gaggawa, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar taɓarɓarewar tattalin arzikin sakamakon yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran.

    Ana sa ran za su tattauna fitar da man fetir ɗin da aka adana a rumbunan ajiyarsu cikin haɗin gwiwa, a yayin da farashin gangar mai ya haura ɗala ɗari a karon farko tun bayan mamayar Rasha a Ukraine.

    Kasuwannin hannayen jarin Turai sun faɗi sosai a yau. Ita ma kasuwar hannun jarin Asiya ta faɗi da kusan kashi biyar. A jiya Lahadi shugaba Trump ya ce tashin farashin man fetir na ɗan jageren lokaci da aka samu, ba wani abu ba ne idan aka kwantanta da samun abin da ya kira zaman lafiya a duniya.

  5. Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya koma Jam'iyyar APC

    Gwamna jihar Zamfara Lawal Dauda ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Nuhu Salihu Anka ya fitar, inda ya ce ya yanke shawara ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa.

    Gwamna Lawal ya ƙara da cewa ya yi la'akari ne da irin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matakin ƙasa da jiha, wanda a cewarsa ke haifar da ruɗani da kawo tsaiko wajen tafiyar da mulki a jihar.

    Ya ce komawa APC za ta taimaka masa wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnatin tarayya domin tabbatar da tsaro da ci gaban jihar baki ɗaya.

  6. Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama - Ma'aikatar tsaro

    Ma’aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce mambobi biyu na rundunar sojin ƙasar sun mutu bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari sakamakon tangarɗar na'ura.

    Har yanzu ba a tabbatar ko lamarin yana da alaƙa da rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran ba.

    Ma’aikatar tsaron ta ce mutanen biyu da suka mutu suna “cikin aiwatar da aikin ƙasa ne” a lokacin da hatsarin ya faru ranar Litinin.

    Ta kuma bayyana cewa tana miƙa ta’aziyya da jaje ga iyalan waɗanda ta kira shahidai.

  7. An kai wa gidan mawaƙiya Rihanna hari - Ƴansanda

    Ƴansanda a Los Angeles sun tabbatar da cewa an kai wa gidan tauraruwa shahararriyar mawaƙiyar nan Rihanna dake Beverly Hills hari da bindiga a ranar Lahadi.

    ‘Yansandan sun ce sun amsa kiran rahoton harin ne da karfe 1:15 inda suka kuma ce an gano wacce ake zargi tare da kama ta

    Wani jami’in ‘yan sanda ya shaida CBS News an samu harsasai na bindigar a gidan tauraruwar inda ya ce babu wanda ya ji rauni sakamakon harin.

    Wata majiyar jami’an tsaro ta ce Rihanna na cikin gidan a lokacin da aka kai harin.

    ‘Yansanda sun ce wacce ake zargin, mace ce mai shekaru 30 zuwa 39 inda ake kyautata zaton ta tsaya a cikin mota a wajen gidan ta harba harsasai bakwai kafin ta tsere.

    An gano motarta a kusan kilomita 12 daga gidan mawaƙiyar, inda aka kama ta.

    Har yanzu ba a bayyana sunanta ga jama’a ba.

    BBC ta tuntubi wakilan Rihanna domin samun ƙarin bayani.

  8. Idan an kai wa Cyprus hari, to Turai aka kai wa hari - Shugaban Faransa

    Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, na ziyarar aiki a ƙasar Cyprus inda yake ganawa da shugabannin ƙasashen Girka da Cyprus domin nuna goyon bayansa, bayan da aka kai wani hari da jirgi mara matuƙi kan sansanin sojin Birtaniya da ke kudancin tsibirin.

    Da yake jawabi a wani taron manema labarai a birnin Paphos, Macron ya ce: “Idan aka kai wa Cyprus hari, to Turai aka kai wa hari.”

    Shugaban na Faransa ya kuma bayyana cewa ƙasarsa za ta tura jiragen ruwan yaƙi guda biyu, wato a matsayin wani ɓangare na aikin rundunar ruwa ta Tarayyar Turai domin kare jiragen kasuwanci da ke wucewa ta yankin tekun maliya.

    Ya ce ana kan shirye-shiryen kafa wata rundunar tsaro ta ruwa wadda aikinta zai kasance kare jiragen ruwa da kuma yi musu rakiya ne kawai.

    "Wannan aiki dole ne a shirya shi tare da haɗin gwiwar ƙasashen Turai da kuma wasu ƙasashe da ba na Turai ba,” in ji Macron.

  9. Croatia ta ƙayyade farashin man fetur a ƙasar

    Gwamnatin ƙasar Croatia ta sanar da ƙayyade farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai.

    Matakin zai fara aiki daga gobe kuma zai ci gaba da kasancewa na aƙalla makonni biyu.

    Firaministan ƙasar, Andrej Plenković, ya ce an kayyade farashin litar man fetur kan euro 1.50, yayin da na man dizel zai kasance euro 1.55.

    Ya ƙara da cewa da ba a ɗauki wannan mataki ba, farashin fetur zai kai euro 1.55 a kowace lita, yayin da na dizel zai iya tashi zuwa euro 1.72.

    Tun da farko dai Croatia ta taɓa ƙayyade farashin mai bayan harin da Rasha ta kai wa Ukraine a shekarar 2022, amma ta dakatar da wannan tsari a watan Yulin bara.

    Hukumomi a ƙasar Koriya ta Kudu ma sun bayyana cewa za su fara saka irin wannan iyaka kan farashin mai, karon farko cikin kusan shekaru 30.

  10. Yadda dubban mutane suka yi murnar naɗin sabon jagoran addinin Iran a Tehran

    Dubban magoya bayan gwamnati a ƙasar Iran sun fito kan titunan babban birnin ƙasar, Tehran, domin murnar naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar.

    Hotuna daga wurin taron jama'a sun nuna mutane suna daga hotunan Mojtaba da na mahaifinsa, Ali Khamenei, wanda aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a makon da ya gabata.

    A wani hoto kuma, an ga wani mutum riƙe da allon da ke nuna kamar mahaifin yana miƙa tutar jagoranci ga ɗansa.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa dubban mutane sun taru a wani babban fili a tsakiyar Tehran da safiyar yau, inda suka nuna mubaya’a ga sabon jagoran ƙasar.

    Sai dai yayin da wasu ke nuna farin ciki a fili, wasu kuma sun shaida wa sashen Farisanci na BBC cewa sabon jagoran “ya fi mahaifinsa tsauri,” tare da bayyana fatan cewa makomarsa za ta kasance irin ta mahaifinsa.

  11. UAE ta ce ta gano makamai masu linzami 15 da jirage marasa matuƙa 18 a yau

    Ma’aikatar tsaron Haɗadɗiyar Daular Larabawa ta ce ta gano makamai masu linzami 15 a yau, inda ta hallaka guda 12, yayin da uku suka faɗi cikin teku.

    Haka kuma, ma’aikatar ta ce ta gano jirage marasa matuƙai 18, inda ta kakkaɓo 17, yayin da ɗaya ya faɗi a cikin ƙasar.

    Tun bayan fara hare-haren Iran, ma’aikatar ta ce ta gano jimillar makamai masu linzami 253 da jirage marasa matuƙa 1,440 inda guda makamai guda 83 suka faɗa cikin ƙasar yayin da aka kakkaɓo sauran in ji ma'aikatar.

    Hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutum 4 da kuma jikkata 117 zuwa yanzu.

  12. Kotu da tabbatar da rushe shugabancin Tanimu Turaki na PDP

    Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta yi watsi da ƙorafin da jam'iyyar PDP ɓangaren Tanimu Turaki ya shigar, inda ya nemi soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta yi ranar 31 ga Oktoba, wanda ya hana hukumar zaɓe ta Inec amincewa da babban taron ƙasa na PDP da aka yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 na Nuwamba, wanda a nan ne aka zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar.

    Tun da farko babbar kotun tarayyar da ke Abuja ta rushe shugabancin Turaki, tana mai cewa an shirya taron da aka zaɓe shi ba bisa ƙa'ida ba.

    Daga nan ne kuma ɓangaren Tanimu Turaki ya garzaya kotun ɗaukaka ƙarar domin ƙalubalabantar hukuncin.

    Sai dai a zamanta na yau kotun ɗaukaka ƙarar - ƙarƙashin jagorancin alƙalan kotun uku - ta yanke shawarar cewa ƙorafin PDP ba shi da tushe, kuma babbar Kotun Tarayya ta yi daidai wajen yanke hukunci da bayar da dukkanin abubuwan da masu ƙorafin suka nema.

    Kotun ta ƙi amincewa da iƙirarin PDP cewa babbar kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraron ƙarar saboda batun ya shafi harkokin cikin gida ne kawai na jam’iyyar.

    Haka kuma, kotun ta tabbatar cewa masu ƙorafin suna da haƙƙin shigar da ƙara domin kare haƙƙinsu a dimokuradiyya, kuma ba a hana jam'iyyar PDP sauraron ƙarar yadda ya kamata ba, kamar yadda ta yi ikirari a ƙorafinta.

    Bugu da ƙari, kotun ta ci tarar naira miliyan biyu ga ɓangaren Turaki kan shigar da ƙara ba bisa ƙa'ida ba.

    Kotun ta ce za ta ci gaba da sauraron sauran hukunci da shawarwari da suka shafi jam’iyyar.

  13. Putin ya taya sabon jagoran addinin Iran murna

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya taya Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin sabon jagoran addinin Iran, tare da tabbatar da goyon bayansa ga ƙasar.

    A cikin saƙon taya murna da aka wallafa a shafin Kremlin, Putin ya ce: "ina miƙa gaisuwa ta ta musamman tare da taya Mojtaba Khamenei murna kan naɗinsa a matsayin jagoran addini ta Iran."

    Shugaban Rasha ya ƙara da cewa yana "yana tabbatar da goyon bayansa ga iran tare da taimaka mata ba tare da shakka ba" sannan ya yi alkawarin "ci gaba da zama abokin ƙasar mai aminci."

    "A wannan lokacin da Iran ke fuskantar hare-hare mai girma, tabbas za su bukaci ƙarfin zuciya da sadaukarwa. Ina da yaƙinin cewa za ka ci gaba daga inda mahiafin ya tsaya cikin girmamawa kuma ka haɗa kan al’ummar Iran a wannan mawuyacin lokaci," in ji shi.

  14. Iyalan sojojin da ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu sun roƙi a sake su

    Iyalan da ‘yan uwan sojojin da aka tsare bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu, sun roƙi shugaban kasar da sojojin Najeriya da su sake su.

    Sun kuma baƙaci a ba su damar ganawa da iyalansu, sannan a tabbatar an yi musu shari’a ta gaskiya da adalci, a kuma duba lafiyarsu kamar yadda sojoji suka yi alƙawari.

    Iyalan sun ce jami’an da a yanzu suka shafe fiye da kwanaki 160 a tsare, ya jefa su cikin wani yanayi mai matuƙar tayar da hankali.

    Masu magana daga cikin iyalan sun ce suna jin tsoro da damuwa kan yadda tsawon lokacin tsarewar ya shafi lafiyar ‘yan uwansu, musamman ganin cewa wasu daga cikin su suna da matsalolin lafiya da ke buƙatar kulawa ta musamman.

    Sun kuma jaddada buƙatar ganin an yi musu adalci cikin hanzari, domin kauce wa ƙarin matsaloli ga rayuwarsu da walwalar iyalansu.

    Ana zargin sojojin ne da hannu a wani yunƙuri na kifar da gwamnatin shugaba Tinubu, zargin da hukumomin tsaro suka ce suna bincike a kai tun bayan kama su.

  15. Dakarun Isra'ila sun yi arangama da mayaƙan Hezbollah a gabashin Lebanon

    Rahotanni na cewa an yi arangama tsakanin dakarun Isra'ila da mayaƙan Hezbollah a iyakar gabashin Lebanon.

    Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasar ya ce sojojin Isra'ila sun zo wajen ne a jirage masu saukar ungulu don yin wani bincike, a nan ne dakarun Hezbollah ɗin suka cim musu harma suka kakkaɓo jirgi guda da ke ƙoƙarin tashi don arcewa.

    A baya baya nan dai ministan harkokin wajen Lebanon ya zargi Hezbollah da sake jefa ƙasar cikin yakin da ba ruwanta a ciki, yana mai jaddada bukatar kungiyar ta ajiye makamanta.

    Kusan mutane ɗari huɗu ne aka kashe a Lebanon tun bayan sake barkewar yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a ranar Litinin da ta gabata.

  16. An ji ƙarar manyan abubuwan fashewa a Tehran - Rahoto

    An ji ƙarar manyan abubuwan fashewa a sassa da dama na birnin Tehran, babban birnin Iran, in ji rahotannin kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Har yanzu ba a fayyace mene ne aka nufa da harin ba, amma ƙarar fashewar sun yi tasiri a fadin birnin.

    Rahotanni na cewa wannan na da alaƙa da sabbabbin hare‑hare da aka kai kan birnin a yayin rikicin da ke ƙara tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.

  17. Harin Iran da makamai masu linzami ya kashe mutum ɗaya a Isra'ila

    Hukumar bayar da gajin gaggawa ta Isra'ila ta ce wani mutum ya mutu, yayin da wasu biyu kuma suka jikkata a tsakiyar kasar, a yayin da Iran ke ci gaba da kai hari a yankin.

    Sojojin Isra'ila sun zargi Tehran da amfani da bama bamai masu ƴaƴa.

    Wannan ne karon farko da aka samu wani hari mai muni da Iran ta kai Isra'ila cikin kusan mako guda.

    Naurorin kare sararin samaniya na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta Nato da ke gabashin tekun Meditreniya sun kakkaɓo wasu makamai masu linzami na Iran waɗanda suka shiga sararin samaniyar Turkiyya a karo na biyu.

    Hukumomi a Bahrain sun ce aƙalla mutum talatin da biyu ne suka jikkata a wani harin da Iran ta kai a kudancin babban birnin ƙasar Manamah.

    Qatar ma ta ce ta harbo wani makami mai linzami na Iran.

  18. Ƙasashen G7 za su fitar da man da ke rumbunan ajiyarsu - Rahoto

    Wani rahoto daga jaridar Financial Times ta ce ministocin kuɗi na ƙasashen G7 za su yi wani taron gaggawa a ranar Litinin domin tattauna yiwuwar fitar da man fetur daga rumbunan ajiyarsu tare, saboda shawo kan tashin farashin man a kasuwannin duniya.

    Rahoton ya ce wannan mataki na zuwa ne bayan farashin gangar man fetur ya haura dala 100 a karon farko tun shekarar 2022, kafin daga baya ya ɗan sauka kaɗan.

    Rumbunan ajiyar man dai ana sarrafa su ne ƙarƙashin kulawar Hukumar Makamashi ta Duniya inda ƙasashe 32 mambobi ke ajiye man fetur a matsayin wani tsarin gaggawa na bai ɗaya da aka tanada domin magance rikicin farashin mai.

    Rahoton ya ƙara da cewa zuwa yanzu ƙasashe uku na G7, ciki har da Amurka sun nuna goyon bayansu ga yiwuwar fitar da man daga rumbunan ajiyar, a cewar wasu mutane da ke da masaniya kan tattaunawar.

  19. Jakadan China a Gabas ta Tsakiya ya je Saudiyya domin sasanta yaƙin Iran

    Jakadan gwamnatin China na musamman kan harkokin Gabas ta Tsakiya, Zhai Jun, ya kai ziyara Saudiyya a wani yunƙuri na shiga tsakani a yaƙin da ke tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

    Zhai ya ce Beijing a shirye take ta yi aiki tare da Saudiyya domin ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tekun Fasha.

    A yayin ziyarar, jakadan ya gana da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud, da kuma babban sakataren ƙungiyar ƙasashen yankin Gulf, Jasem al-Budaiwi.

    A ganawarsa da Yarima Faisal a ranar Litinin, Zhai ya nuna matuƙar damuwa kan tashin hankalin da ake fuskanta a yankin, yana mai cewa dole ne a mutunta ikon ƙasashe da tsaronsu da kuma yankunansu.

    Ya kuma jaddada cewa ya kamata a yi Allah wadai da duk wani hari da ke jawo wa fararen hula ko wuraren da ba na soja ba illa.

    Haka kuma ya sake nanata kiran Beijing na a dakatar da duk wasu hare-haren soji nan take.

  20. Kawo ƙarshen yaƙin Iran na buƙatar amincewata da Netenyahu - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran zai buƙaci amincewarsa da na firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

    Rahoton jaridar The Times of Israel ya ce Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta waya da aka yi da shi, inda ya ce shi da Netanyahu sun dade suna tattaunawa kan batun, yana mai cewa "zai yanke shawara a lokacin da ya dace”.

    Da aka tambaye shi ko Isra’ila za ta iya ci gaba da yaƙi da Iran idan Amurka ta dakatar da hare-haren da take kai wa, Trump ya cewa: “Ba na ganin hakan zai zama dole.”

    Game da naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin Iran, Trump ya ƙi yin tsokaci, inda ya ce: “Za mu ga abin da zai faru.”

    A baya dai Trump ya nuna adawarsa da naɗin Mojtaba, inda ya ce: “Ɗan Khamenei ba abin da zan amince da shi ba ne.”