Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya yaƙin Iran zai cutar da ƙasashen Yamma ya kuma tallafi Rasha?
- Marubuci, الکسی کالمیکوف، بیبیسی
- Lokacin karatu: Minti 4
Yaƙin Isra'ila da Amurka da kuma Iran ya jima yana barazanar rufe zirin Hormuz; wata muhimmiyar hanya ga tattalin arzikin duniya - wadda kashi 20 cikin 100 na man fetur da gas ɗin da ke fita daga ƙasashen yankin Gulf ke bi.
Samun kowane irin tsaiko a wannan hanya zai haifar da matsala ga ƙasashen Turai, da Amurka da ma Shugaba Trump kansa.
To sai dai a gefe guda hakan zai taimaka wa Rasha, saboda zai ba ta damar ƙara ywana man da take fitarwa don samun biliyoyin dalolin da za ta ci gaba da yaƙin Ukraine.
Ƙasar Iran ce ke da iko da arewacin mashigar, kuma ta sha yin barazanar rufe hanyar a matsayin martani ga hare-haren Amurka da Isra'ila, amma har zuwa yanzu ba ta aiwatar da barazanar ba, duk kuwa da kashe manyan jagororin ƙasar.
To amma duk da rashin rufe hanyar, an ɗan samu tsaikon jigilar man ta mashigar, inda kamfanonin jigilar man ke fargabar ɗaukar kasadar wucewa ta wurin.
lamarin da wasu masana ke ganin kawai dai hanyar na buɗe ne a ganin ido, amma a aikata tamkar a rufe take.
Ta yaya yaƙin zai taimaki Rasha?
"Wannan yaƙi zai yi matuƙar ƙarfafa matsayin Rasha a kasuwar ɗanyen mai ta duniya. Samun tsaiko a man ƙasashen Gabas ta Tsakiya zai sa ƙasashen Indiya da China su koma sayen man Rasha'', a cewar kamfanin Kepler mai kula da jigilar man fetur da iskar gas.
A watannin baya-bayan nan waɗannan ƙasashe biyu, wadanda su ne manyan masayan mai a duniya sun rage sayen man Rasha saboda matsin lambar ƙasashen yamma, lamarin da ya tilasta wa Rasha rage farashin manta tare da rage yawan fitar da shi.
Duk da waɗannan matgakan da Rasha ta ɗauka, bai saka ta rika sayar da duka man nata ba, inda miliyoyin ganguna suka ci gaba da kasancewa a cikin teku suna jiran masu saye.
Idan aka rufe mashigar Hormuz, duniya za ta rasa man ƙasashen Gabas ta Tsakiya, da suka haɗa da Saudiyya da UAE da Kuwait da Iraƙi da ma man Iran wanda tuni ke da takunkumi.
Kasancewar Amurka ta hana fitar da man Venezuela, Rasha za ta kasance ƙasar da za ta riƙa sayar da manta da araha, kuma yayin da farashin man zai tashi ba makawa, hakan zai bai wa Rasha damar sayar da dubban tankokinta da ke maƙale a cikin teku.
"Vladimir Putin zai amfana da yaƙin, saboda farashin mai zai tashi sannan a samu ƙaruwar buƙatar man rasha, kuma idan Amurka ta yi wasa, Indiya za ta riƙa sayen wannan man,'' a cewar Javier Blas masanin makamashi na Bloomberg.
Tuni dai Mista bTrump ya bai wa Indiya damar sayen man Rasha da ke cikin teku.
Yayin da zaɓen rabin wa'adi na watan Nuwamban ke matsowa, saukar farashin man a Amurka shi ne babban abin da Trump zai fi bai wa fifiko.
Samun tsaikon fitar da mai, zai bai wa Kremlin damar ci gaba da mafani da bututunta wajen fitar da mai zuwa Turai, kodayake akwai wasu matsaloli biyu.
Na farko, Tarayyar Turai na shirin sanya cikakken takunkumi kan Rasha cikin watan Afrilu. To amma game da man fetur, wannan ba shi ne lokacin da ya dace ta yi hakan ba.
Na biyu, ƙasashen Hungary da Slovakia, waɗanda suka fi sayen man Rasha a Turai kuma ƙawayen Kremlin, ba su samu man ta bututun ba fiye da wata guda, saboda lalacewar bututun a Ukraine sakamakon harin Rasha.
Sakamakon haka, waɗannan ƙasashe biyu sun ƙi amincewa da sabbin takunkuman da aka ƙaƙaba wa Kremlin domin tallafa wa Ukraine.
Tarayyar Turai ta bayar da shawarar cewa ƙasashen biyu su riƙa samun mai daga wani bututun tekun Croation maimakon man na Rasha.
Ta yaya yaƙin zai cutar da Ƙasashen Yamma?
Mr. Trump ya alƙawarta cewa farashin mai zai ci gaba da kasancewa bai tashi ba, sannan za a riƙa sayar da gas da araha. Sai dai tsadar man a duniya ya saɓa da alƙawarin nasa.
Amurka ce ƙasar da ta fi samar da man fetur da iskar gas a duniya, ,kuma ba za ta fuskanci ƙarancin man acikinta ba.
Haka kuma ƙasar na da rumbunan ajiyar man da za ta iya fitar da shi zuwa kasuwannin duniya domin daidaita farashinsa.
To amma ba haka batun yake ba a Turai. Bayan yanke alaƙa da man Rasha - wadda ke shigar musu da iskar gas ta bututu kan wata daɗaɗɗiyar yarjejeniya, ƙasashen na Turai a yanzu na sayen mai daga kasuwar mai ta duniya, wanda farashinsa ke hawa da sauka.
Bunƙasar tattalin arzikin Turai, saɓanin Amurka na tafiyar hawainiya, don haka samun tsaiko da fannin makamashi ka iya haifar da matsalar tattalin arziki da na siyasa.
An fara yaƙin ranar Asabar, amma bayan kwana biyu sai da farashin gas ya tashi da kashi 20 cikin 100.
Idan har ana rufe mashigar Hormuz, Amurka ba za ta iya magance matsalar ba. Mista Trump ya sha alkawarta magance ƙananan matsaloli, kamar rufe jigila ta Tekun Maliya da ƙungiyar ƴantawayen Houthi suka yi, amma hanyar jigilar mai tsakanin Turai da Asiya ta ci gaba da zama a rufe.