Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 21 ga watan Yuli, 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙashen wannan shafi na labaran kai-tsaye na wannan rana. Sai kuma gobe idan Allah kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa Allah ya tashe mu lafiya.

  2. Kotu ta wanke mutum 12 waɗanda ake zargi da dasa bam a jirgin ƙasa A India

    Wata Kotu a Indiya ta wanke mutane goma sha biyu da aka yankewa hukunci sakamakon tashin bama-bamai cikin jirgin kasa a Mumbai.

    Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutum 200, sannan sama da 800 suka jikkata kimanin shekara 20 da suka gabata.

    An yankewa biyar hukuncin kisa sauran kuma an yanke musu hukuncin daurin rai da rai.

    Babbar kotun Bombay ta gano shaidar da aka bayar a shari'ar ba gamsasshiya ba ce, sannan masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da hannun mutanen a al'amarin.

    Shari'ar ta gano kura-kurai a binciken ƴansanda da shaidu.

  3. Malaman jami'o'in Ghana sun ce a daƙile harƙallar haƙo ma'adinai ko su shiga yajin aiki

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Ghana (UTAG) ta yi kira da kakkausar murya ga Shugaba John Dramani Mahama da ya cika alƙawarin da ya ɗauka kafin zaɓe na yaƙi da aikin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

    Lamarin haƙar ma'adinan ba bisa ƙa'ida ba, wanda aka fi sani da galamsey a ƙasar Ghana na cikin matsalolin da ke ci wa ƴan ƙasar tuwo a ƙwarya.

    Ƙungiyar malaman ta kuma yi gargaɗin cewa gazawar daukar mataki cikin gaggawa na iya tunzarasu su tsunduma yajin aiki.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Ghana (UTAG) ta bayyana damuwa matuƙa kan yadda gwamnati ta gaza samar da wani cigaba mai gamsarwa a yaƙin da take da aikin galamsey, duk da ƙananan nasarorin da jami’an tsaro suka samu.

  4. Hare-haren Isra'ila sun lalata gidaje da masallatai a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Mazauna Deir al-Balah a tsakiyar Gaza sun ce tankokin yaƘin Israila sun lalata gidaje da masallatai kuma sun kashe mutane da dama a sabon hari ta Ƙasa.

    Hukumonin agaji sun ce harin da sojojin Isra'ila suka kai ya yi tsanani. Sojoji ba su ce komai game da harin ba, bayan sun bayar da umarnin sauyawa al'umma matsuguni ranar Lahadi.

    Dubban mutane sun tsere daga muhallansu. Hukumar Kula da Ayyukan jin kai ta MDD ta yi gargadi, tilastawa mutane barin muhallansu na haifar da koma baya a ƙoƙarin tsaron rayuwar mutane.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce jami'an ta za su ci gaba da zama don kare gine-gine masu muhimmanci.

    Likitoci na cewa an kashe Falasdinawa da dama cikin sa'o'i ƙalilan da suka gabata, ana tunanin mutane 20 na da rai daga mutane 50 da Hamas ke tsare da su har yanzu a zirin Gaza.

  5. Yadda ziyarar Tinubu zuwa Kano ta bar baya da ƙura

    Abba

    Asalin hoton, Ibrahim Adam/Facebook

    A ranar Juma'a da ta gabata ne, shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara zuwa jihar Kano, domin ta'aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan da ya gabata.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a lokacin da aka yi rasuwar Tinubu ba ya ƙasa, amma duk da haka ya aika tawaga ƙarƙashin ministan tsaron ƙasar domin wakiltarsa a wajen jana'izar.

    Sai dai ziyarar tasa ta bar baya da ƙura, saboda rashin zuwa gidan gwamnatin jihar da kuma gidan Sarki.

  6. Faɗowar jirgin sama a makaranta ta kashe mutum 19 a Bangladesh

    Aƙalla mutane 19 sun mutu a Bangladesh sakamakon rikitowar wani jirgin horas da sojin sama a wata makaranta da ke Dhaka babban birnin kasar.

    Daruruwan mutane sun samu raunuka, gwamnati ta ce da dama daga cikin wadanda suka mutu yara ne kanana.

    Ganau sun shaida wa BBC cewar sun ga yadda jirgin ya fada harabar makarantar yana cin wuta.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda wuta da hayaki ke tashi, kuma mutane na ihu da kuka. Hukumar kashe gobara ta Bangledesh ta ce ginin na ɗauke da azuzuwan ɗalibai matasa.

    Da dama daga cikin waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin yanayi. Gwamnati ta sanar da ranar Talata a matsayin ranar makoki,

  7. Ƙasashe 26 sun yi kira da Isra'ila ta dakatar ya yaƙi a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    A wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Burtaniya ta fitar tare da hadin gwiwar Ƙasashe fiye da 20, an buƙaci a dakatar da yaƙin da ake yi a Gaza ba tare da ɓata lokaci ba, inda suka bayyana damuwa game da halin ƙuncin da fararen hula ke ciki.

    Sanarwar ta ce halin da al’ummar Gaza ke ciki ya kai wani mataki mai tayar da hankali, kuma dole ne a kawo ƙarshen wannan bala'i da gaggawa.

    Sanarwar ta zargi gwamnatin Isra’ila da toshe duk wata hanya ta shigar da kayan agaji, wanda hakan ke ƙara dagula lamarin da tauye mutuncin al’ummar Gaza.

    Sanarwar ta ce "fiye da Falasdinawa 800 sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin samun abinci da ruwa."

    Haka kuma ƙasashen sun bayyana taƙaici da yadda Isra’ila ke hana agajin jin kai isa ga fararen hula, wanda suka bayyana a matsayin saɓawa dokokin ƙasashen duniya.

    Ƙasashen sun kuma yi Allah-wadai da cigaba da tsare mutanen da Hamas ta kama tun ranar 7 ga Oktoban 2023, inda suka bukƙaci a sako su ba tare da wani sharaɗi ba.

    Sun ce hanya mafi dacewa don dawo da wadannan mutane gida ita ce ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar tattaunawa.

    Haka kuma, ƙasashen sun buƙaci Isra’ila ta cire duk wata takura da take wa isar da agaji tare da bai wa Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin jin kai damar gudanar da ayyukansu cikin aminci.

  8. Ban ajiye muƙamin da Tinubu naɗa ni ba - Mohammed Babangida

    Babangida

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Ɗan tsohon shugaban gwamntin sojin Najeriya - Janar Ibrahim Badamasi Babangida - Mohammed Babangida ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya ƙi amincewa da muƙamin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa shi.

    An dai ta yaɗa wata takarda, wadda a ciki ake cewa Mohammed ya ce ba ya son naɗin da aka masa na shugabantar kwamitin gudanarwa na bankin noma na ƙasar.

    A jawabinsa na ƙaryata batun, Mohammed ya ce, "ban ajiye muƙamin ba aka naɗa ni ba. Takardar da ake yaɗawa ta bogi ce, kuma aikin masu neman tayar da zaune tsaye ne.

    "A shirye nake in yi aiki da shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin noma domin bunƙasa ɓangaren noma da samar da abinci a Najeriya."

    A makon jiya ne dai gwamnatin Najeriya ta sanar da naɗa Mohammed Babangida a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin noma na ƙasar a cikin wasu jerin naɗa-naɗe da gwamnatin ta yi.

  9. Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon rikici

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda yunwa ke kara kamari a arewa maso gabas na Najeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda fiye da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar matsananciyar rashin abinci.

    A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa.

    A Dikwa, manoma na tashi da safe su ratsa tafiya mai tsawo domin yin noma na ‘yan awanni kafin su koma gida.

    Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma, ya ce farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, kuma kudin ɗinki da yake samu da dare bai isansu.

    Modu Umar, wani shugaban al’umma, ya bayyana cewa yunwa tana haddasa cututtuka kamar gudawa a cikin yara da manya saboda rashin abinci da magani.

    "Mutane na fita nesa su tara itace domin samun kudin siyan abinci." in ji shi.

    ICRC dai ta ce ta fara wani shiri na taimakawa noma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga sama da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.

    "Ana kuma shirin rarraba famfunan ban-ruwa masu aiki da hasken rana domin noman rani." in ji ƙungiyar ICRC.

    Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta ce ana fargabar lokacin Ƙarancin abinci daga Yuli zuwa Satumba, inda mutane ke buƘatar sayen abinci, amma Ƙarancin kudi yana hana su cika buƙata.

    Wata uwa mai yara biyar, Bintu Konto, ta ce: “Wasu lokuta muna kwana da yunwa har kwana biyu zuwa uku. Idan Allah ya kawo wani abu, sai mu ci.”

    Ƙungiyar ICRC na aiki a Borno tun 2012 inda take taimakawa al’ummomin da rikici ya shafa da kuma kare martabar fararen hula bisa dokokin Geneva na 1949.

  10. An tuhumi Boniface Mwangi da laifin mallakar makamai a Kenya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An tuhumi mai rajin kare haƙƙin yan Adam a Kenya Boniface Mwangi da laifin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba a wata shari'a da yansanda suka ce na da alaƙa da zanga-zangar ƙyamar gwamnati a watan da ya gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce: Cikin Kotu Nairobi, masu goyon bayansa na rera taken kasar Kenya, an kama Mista Mwangi a karshen mako cikin gidansa kusa da babban birnin kasar.

    An bayar da belinsa bayan ya karyata zargin da ake masa.

    Yansanda sun ce sun samu hayaki mai sa hawaye da harsashai a gidansa ya yinda suke bincike.

    Kungiyar kare hakkin yan Adam ta Amnesty International da kungiyoyin kare hakkin yan Adam na cikin gida sun ce ana yiwa yan adawa cin zarafi irin na siyasa.

  11. Ana gab da cimma yarjejeniya tsakanin Rasha da Ukraine

    Sakataren Tsaron Burtaniya ya yi hasashen an samu damar da za ta tilasta wa Rasha cimma yarjejeniya da Ukraine.

    John Healey na jawabi a taron tsaron ƙungiyar tuntuɓa game da tsaron Ukraine a London, tare da manyan yan siyasa daga ƙasashen da ke goyon bayan Ukraine.

    Wakilin BBC ya ce John Healey ya ce muna da kwanaki hamsin da za mu bai wa Ukraine abin da take buƙata wajen kare kanta.

    Abin da zai yi daidai da kwanaki 50 da Donald Trump ya deɓar wa Rasha ta amince da yarjejeniyar sulhu ko ta fuskanci ƙarii takunkumai masu tsauri.

  12. Somaliya ta rufe bankuna da asusun ajiya da ke da alaƙa da ƙungiyar al-shabab

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Somalia ta rufe bankuna da asusun ajiya sama da 100 tare da rufe layukan waya 575 da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar al-Shabab, a wani mataki na yaƙi da ta’addanci da ya dauki watanni shida.

    Kamfanin dillancin labaran gwamnatin ƙasar, Sonna, ya bayyana cewa wannan mataki ya tarwatsa hanyoyin samun kuɗi da kungiyar ke amfani da su wajen tilasta biyan kuɗi daga mutane da kamfanoni ta hanyar da ba na bisa ƙa'ida ba.

    "Daga 1 ga Janairu zuwa 30 ga Yuni ne gwamnati ta aiwatar da wata dabarar kasa da ta mayar da hankali kan katse hanyoyin samun kudin kungiyoyin ta’addanci, inda hakan ya kai ga rufe bankuna 21 da asusun ajiya 88, da kuma rufe layukan waya 575.

    Haka kuma, hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa ta gargadi jama’a da ‘yan kasuwa da kada su bayar da kuɗi ga ƙungiyoyin ta’addanci da ke fakewa da sunan “zakka”.

    A watan Maris 2024, gwamnatin ƙasar ta ƙwace dala miliyan bakwai, ta kuma rufe layukan waya 675 da rufe asusun ajiya 110 da ake zargin na da alaƙa da al-Shabab.

  13. 'Adadin Falasɗinawan da suka mutu tun fara yaƙin Isra'ila da Hamas ya kai 59,000'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ma’aikatar Lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce adadin Falasɗinawan da suka mutu tun bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-harenta kan Hamas a ranar 7 ga Oktoban 2023 ya kai 59,029

    Ma'aikatar ta kuma ce sama da mutum 142,000 ne suka jikkata tun daga lokacin.

    A cikin sa’o’i 24 da suka gabata kaɗai, kimanin mutum130 ne suka mutu, fiye da 1,000 kuma suka jikkata.

    Ma’aikatar ta ƙara da cewa har yanzu akwai wasu gawawwaki da mutanen da suka jikkata a karkashin gine-gine da kuma kan tituna, amma ba a iya kai musu ɗauki saboda cikas da jami’an agajin gaggawa da na kashe gobara ke fuskanta.

  14. Sudan za ta taƙaita kira ta whatsApp

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar sadarwa ta Sudan ta sanar da cewa za ta fara taƙaita amfani da kiran waya da na bidiyo ta manhajar WhatsApp daga ranar 25 ga Yuli, saboda dalilan tsaro.

    Hukumar ta ce dakatarwar bai shafi sauran ayyuka kamar tura saƙo ta hanyar rubutawa da raba bayanai ba.

    Sun bayyana matakin a matsayin kariya ga tsaron kasa, musamman duba da rikicin da ke tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF, wanda ya lalata cibiyoyin sadarwa a ƙasar.

    Jama'a, musamman a Darfur da Kordofan, na dogaro da WhatsApp domin sadarwa da 'yan uwa da abokai.

  15. Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya - NiMET

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025, inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar.

    A kan haka NiMet ta shawarci al'umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.

    A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.

    Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, za a samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sokoto da Kaduna.

    Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar ƙasar kamar Abuja da Naija da Plateau da Nasarawa da Benue da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.

    Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Niger da Plateau.

    A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sokoto da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.

  16. Majalisar dattawa ta gargaɗi sanata Natasha kan komawa bakin aiki

    ...

    Asalin hoton, X/Natasha

    Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar da komawa bakin aiki, inda ta bayyana cewa ba ta da hurumin komawa har sai an kawo ƙarshen dakatarwar da aka yi mata.

    A wata sanarwa da kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ya fitar ranar Lahadi, ya jaddada cewa babu wani umarnin kotu da ya ce majalisar ta karɓi Sanata Natasha kafin ƙarewar lokacin da aka dakatar da ita.

    An dakatar da sanata Natasha ne tun watan Maris ɗin 2025 sakamakon karya dokokin majalisar bayan ta yi gardama da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio - inda ta zarge shi da cin zarafi ta hanyar lalata, abin da Akpabio ya musanta.

    A kwanakin baya, Natasha, wadda ta dogara da hukuncin da mai shari'a Binta Nyako na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke, ta bayyana niyyarta ta komawa zauren majalisa ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025.

    Sai dai, kakakin majalisar dattawa ya ce hukuncin ba ya ɗauke da wani umarni na doka da ya ce majalisar ta karɓi dawowar sanatar kafin karewar wa'adin dakatarwa da aka yi mata.

  17. Hotuna: Yadda Falasɗinawa ke tserewa Gaza bayan gargaɗin Isra’ila

    ...

    Asalin hoton, BBC/Reuters

    Yayin da muke ci gaba da ba da rahoto kan hare-hare ta ƙasa da Isra’ila ke kai wa a Deir al-Balah, rundunar sojin Isra’ila (IDF) na ci gaba da far wa sassa daban-daban a Gaza.

    Kamar yadda BBC ta ruwaito, dakarun sojin Isra’ila sun bayar da umarni ga Falasɗinawa da su fice daga Deir al-Balah a jiya, wani yanki da ba su taɓa kai farmakin ƙasa a cikinsa ba tun farkon yaƙinsu da Hamas watanni 21 da suka wuce.

    Rundunar IDF ta bayyana cewa mutane su gaggauta yin hijira zuwa al-Mawasi da ke gefen tekun Bahar Rum.

    Mai magana da yawun rundunar a harshen Larabci, Avichay Adraee, ya ce Isra’ila “na faɗaɗa ayyukanta” a Deir al-Balah, ciki har da “wata sabuwar unguwa da ba ta taɓa shiga ba a baya.”

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda ɗaruruwan mutane suke tserewa dauke da kayayyakin su da kuma hotunan da ke nuna lokacin da wani makami ya faɗo kan wani gini a safiyar yau a birnin Gaza, babban birnin da ke arewacin zirin.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Tsofaffin ƴansandan Najeriya na zanga-zanga a Abuja

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

    Tsofaffin jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun fara gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja da wasu jihohi, domin nuna rashin jin daɗinsu kan tsarin fansho da ake amfani da shi a yanzu.

    Sakamakon hakane, Sufeto Janar na ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci dukkan kwamishinonin ƴansanda a faɗin ƙasar da babban birnin tarayya Abuja (FCT), da su samar da tsaro yayin wannan zanga-zangar.

    Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce an samu yunkurin yaɗa bayanan ƙarya domin ɓata sunan gwamnati da na rundunar ƴansandan.

    Ya ce kiraye-kirayen da tsofaffin jami’an ke yi na fita daga tsarin fansho da ake amfani da shi a yanzu ba sabon abu ba ne, kuma waɗanda suka riƙe muƙamin sufeto Janar a baya sun goyi bayan hakan, amma wasu matsaloli na doka da na kuɗi sun hana ci gaban hakan.

    ...
    ...

    Sufeton ya kuma ja-kunnen masu siyasantar da batun, yana cewa kada a yi amfani da ƙorafin tsofaffin jami’an don cimma manufar siyasa.

    Ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar, musamman a inda ake gudanar da ita bisa ƙa’ida.

    ...
  19. 'Gwamna Radda na cikin ƙoshin lafiya bayan hatsarin mota'

    Dikko Radda

    Gwamnatin jihar Katsina ta ce gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda na cikin koshin lafiya bayan hatsarin mota da ya samu.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Daura, inda wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta, kuma ta faɗa wa motar da gwamnan ke ciki.

    Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, ta ce gwmanan bai samu wasu munanan raunuka ba.

    "Muna godiya da addu'o'i da ake ta yi mana. Allah ya jarabce mu da hatsarin mota amma mun samu sauki, muna nan a asibiti ana ci gaba da duba mu domin samun sauki," kamar yadda gwamna Radda ya bayyana a cikin wani bidiyo.

  20. 'Falasɗinawa 19 sun mutu cikin sa'o'i 24 saboda yunwa a Gaza '

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla Falasɗinawa 19 ne suka mutu sakamakon yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Gaza, a cewar wani jami’i daga ma’aikatar lafiya ta Hamas.

    Mai magana da yawun asibitin al-Aqsa da ke Deir al-Balah, Dr Khalil al-Daqran ya shaida wa BBC cewa halin da asibitocin Gaza ke ciki ya kai wani matsayi na matuƙar haɗari.

    “Mutum goma sha tara, ciki har da yara, sun mutu saboda yunwa,” in ji shi.

    “Ƙarfin mu na samar da abinci ga marasa lafiya ko ma’aikatan asibiti ya ƙare wanda hakan ya sa dayawa daga cikin ma’aikatanmu ba sa iya ci gaba da aiki saboda tsananin yunwa.”

    Ya ƙara da cewa har ma da kayan buƙatu na jarirai kamar madara sun ƙare daga kasuwa.

    “Asibitoci ba za su iya samar da ko kwalban madara guda ɗaya ga yara da ke fama da yunwa ba domin dukkan madarar jarirai sun ƙare daga kasuwa,” in ji shi.