Ana ci gaba da rikici a Syria duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Asalin hoton, Reuters
Ana ci gaba da rikicin ƙabilanci a kudancin Syria duk da sanarwar gaggauta tsagaita wuta da shugaban ƙasar ya yi.
Cikin makonnin da suka gabata mayaƙan al'ummar Druze marasa rinjaye suna fafatawa da mayaƙan Bedouin da ke lardin Suweida, inda kowanne ɓangare ke ɗora wa juna laifin aikata ba daidai ban.
Shugaban Syria na riƙo, Ahmed al-Sharaa ya tura da ƙarin dakaru yankin amma ana zargin dakarun gwamnati da kai hare-hare kan Druze. Mutane fiye da 900 aka bayar da rahoton an kashe a rikicin.
A farkon makon nan Isra'ila ta sanar da goyon bayan ta ga ƙabilar Druze, inda ta kai hare-hare a kan gine-ginen gwamnati da ma'aikatar tsaron ƙasar da ke Damascus.

Sharaa ya sanar da tsagaita wuta a ranar Asabar, kuma ya tura dakarun Syria zuwa Suweida domin kwantar da tarzoma. Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda Isra'ila da Amurka ke gyon baya ta yi tanadin daina kai wa juna hare-hare da kuma tabbatar da kariya ga al'ummar Druze.
Dakarun gwamnatin sun kafa shingayen bincike domin hana ƙarin mutane shiga rikicin, amma duk da haka an riƙa jiyo ƙarar makamai a birnin Suweida a ranar Asabar.
An ga yadda mutane ke ɓalle shaguna suna kwasar kaya da sunan ganima, da kuma cinna masu wuta.
Ministan harkokin wajen Isra'ila ya bayyyana shakku kan sabon alwashin da Syrian ya sha, na bayar da kariya ga ƙananan ƙabilun ƙasar.
Al'ummar Druze da ke Suweida ƙaramar ƙabila ce mai bin addini na daban duk da cewa ta ɓalle ne daga mazhabar shi'a, kuma tana da jama'a a Isra'ila da kuma Lebanon.
Firaministan Ira'ila, Benjamin Netanyahu ya yi alƙawarin kare ƙabilar Druze a Syria saboda alaƙar da suke da ita da ƙasarsa.
Zaman ɗar-ɗar da aka daɗe ana yi tsakanin ƙabilar Druze da Bedouin ya rikiɗe zuwa ƙazamin rikici a ranar Lahadin makon jiya bayan kama wani ɗan kasuwa daga ƙabilar Druze a kan babban titin zuwa Damascus.
Wata ƙungiyar kare ƴancin ɗan Adam ta Birtaniya mai ayyukanta a Syria, Observatory of Human Rights (SOHR), ta ce mutane aƙalla 940 aka kashe tun bayan ɓarkewar rikicin.
Jakadan Amurka na musamman a Syria, Tom Barrack ne ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar Juma'a.














