Boko Haram ta kai hari Kamaru

Sojojin Kamaru yayin farautar 'yan Boko Haram

Asalin hoton, .

Bayanan hoto, Sojojin Kamaru yayin farautar 'yan Boko Haram

Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan kimanin 25 suka jikkata sakamakon wani harin kunar-bakin-wake a garin Mora da ke lardin arewa mai nisa a Kamaru, da safiyar Lahadi.

Rahotanni na cewa wani matashi ne da ba a bayyana adadin shekarunsa ba, ya kwance damarar kayan ababan fashewar da ke dauke da su, a kofar shiga babbar kasuwar garin.

Ana dai bayyana fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu ka iya karuwa bisa rashin samun kai daukin gaggawa ga wadanda harin ya rutsa da su.

Harin na ranar Lahadi dai ya faru ne a dai-dai lokacin da jami'an tsaro na Rundunar Hadin Gwiwa a Tafkin Chadi ke ikirarin samun nasarar karya lagon Boko Haram a yankin.