Nigeria: CBN zai ci gaba da sayarwa 'yan canji dala

Asalin hoton, AFP
Lokacin karatu: Minti 1
A cikin wannan mako ne da ke karewa, kungiyar 'yan canji ta Nijeriya ta ce babban bankin kasar ya bayyana aniyar ci gaba da bai wa 'ya'yanta dalar Amurka, don sayarwa ga masu bukata a kasar.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsanancin hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki, sakamakon faduwar darajar Naira.
Daga Kano, wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya je kasuwar 'yan canji ta Wapa, inda ya zanta da Alhaji Al'mustapha Yakubu Kofar Mata, mataimakin shugaban kungiyar 'yan canji ta kasa shiyyar arewa maso yamma.
Kuma ya fara da tambayarsa ko sun fara samun wannan dala daga babban banki?







