'Yan Niger Delta sun kai hari a Lagos

Jami'an tsaro sun yi wa unguwar kawanya
Bayanan hoto, Jami'an tsaro sun yi wa unguwar kawanya

Wasu matasa da ake zargi 'yan yankin Naija Delta ne sun kai hari a wani yanki na birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa matasan sun kai hari ne a unguwar Igando da asubahin ranar Talata, inda suka rika yin harbi kan mai uwa da wabi.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatarwa BBC aukuwar lamarin, kuma ta ce jami'anta sun yi wa unguwar kawanya.

  • <link type="page"><caption> Za mu murƙushe tsagerun Naija Delta — Buhari</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2016/05/160529_buhari_niger_delta" platform="highweb"/></link>
  • <link type="page"><caption> Sojoji sun kama mutane 6 a Niger Delta</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2015/08/150810_nigeria_military_arrest_niger_delta" platform="highweb"/></link>

Sai dai rundunar ta musanta cewa 'yan kungiyar sun kashe jami'anta.

Har yanzu dai mazauna yankin suna cikin fargaba.

A watan jiya ma maharan sun kai farmaki a jihar Ogun da ke makwabtaka da Lagos, inda aka yi zargi sun kashe mutum 20.