Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tanzania: Dalilin da ya sa noman tumatir a ƙasar ke neman gagarar manoma
- Marubuci, Daga Soraya Ali da Sara Adam
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A tsakar rana mai zafi ta Tanzania, Lossim Lazzaro, ya tsaya cikin kaɗuwa yana kallon gonarsa.
A hankali sai ya riƙa zuwa takin dabbobi kan shukokinsa, a yunƙurinsa na ƙarshe domin taya su girma.
Mista Lazzaro yana da kadada biyar ta gona, kuma ya taɓa zama manomin tumatir wanda ya samu alheri daga noman a arewacin yankin Arusha. Sai dai a yanzu, kamar sauran manoma, yana ta gwagwarmaya domin ganin shukokinsa da kasuwancinsa na tafiya daidai ba tare da matsala ba, duk da halin da ake ciki na ƙarancin taki.
"Samun taki a kasuwa ya zama wani abu mai matukar wahala a gare ni," in ji Mista Lazzaro.
Taki - wanda ɗaya ne daga cikin ginshiƙan da ke taimaka wa shuka ta girma - ana cikin ƙarancinsa a faɗin duniya. Farashinsa a fadin duniya ya yi tashin gwauron zabi sakamakon yaƙin Rasha da Ukraine.
"A halin yanzu, irin wannan buhun ya kusan ruɓanya kuɗinsa," in ji shi a yayin da yake nuna buhun.
Adadin takin da ake da shi a faɗin duniya ya ragu da kusan rabi, haka kuma farashin wasu daga cikin nau'in takin ya ninka uku a tsawon shekara guda, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
Wannan abin yana da tasiri matuƙa kan ƙasashe kamar Tanzania inda manoma suka dogara kan takin da aka shigar da shi ƙasar.
"A ƙarshe na ƙare da sayen taki daga wurin wanda ya sarrafa shi cikin gida amma duk da haka sai na bayar da odarsa watanni kafin lokacin saboda ƙarancinsa," in ji Mista Lazzaro.
Wannan lamari yana sanya fargabar ƙarancin abinci a zukatan jama'a.
Nahiyar Afrika, wadda ita ke amfani da mafi ƙarancin taki a duk kadada a faɗin duniya, na cikin hatsari.
Wannan ƙarancin takin zai yi tasiri kan amfanin gona, musamman alkama wadda ke buƙatar taki mai ɗumbin yawa kuma tana da amfani domin miliyoyin mutane ne suke amfani da ita.
Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa ƙarancin taki zai iya jefa ƙarin mutum miliyan bakwai a cikin halin ƙarancin abinci.
Sun bayyana cewa samar da hatsi a 2022 zai ragu da kusan tan miliyan 38 daga abin da aka samu a bara wato tan miliyan 45.
Tanzania, kamar sauran ƙasashen duniya, ta dogara ne kan Rasha da China domin samun taki - waɗanda su ne manyan ƙasashen duniya da ke kan gaba wurin samar da taki.
Rasha, wadda ke ƙarƙashin takunkumin ƙasashen duniya, na samar da adadi mai yawa na potash da ammonia da kuma urea.
Waɗannan su ne ginshiƙai uku da ake buƙata domin samar da takin zamani. Sun taimaka wurin shirin samar da abinci na 1960 wanda ya ninka adadin abincin da ake samarwa a duniya kuma ya taimaka wurin ciyar da miliyoyin mutane abinci.
Rasha na fitar da kusan kashi 20 cikin 100 na taki kuma idan aka haɗa ta da Belarus wadda ita ma aka saka wa takunkumi take fitar da kashi 40 cikin 100 na potassium, kamar yadda bayanai suka nuna.
Farashin takin zamani tuni ya tashi sakamakon tasirin annobar korona. A yanzu, takunkumin da aka saka wa Rasha da Belarus da kuma ƙoƙarin daƙile wasu kayayyakin da ake fitarwa daga China, sun ƙara sakawa abubuwa sun ƙazanta.
Wannan lamari ya ja ƙasashen Afrika da dama waɗanda suka dogara kacokan bisa abubuwan da ake shigar musu da su neman mafita ko ta halin ƙaƙa.
Yadda ake neman takin zamanin da ake yi a cikin gida ya ƙaru.
Ƙananan monama a arewacin Tanzania na mayar da hankali domin dogara ga kamfanonin ƙasar kamar su 'Minjingu Mines and Fertilizer Ltd', ɗaya daga cikin kamfanoni mafi girma da ke samar da takin zamani a Tanzania.
Kamfanin ya ce a halin yanzu ya samu ƙarin buƙatar samar da takin kuma yana ta ƙoƙari domin samar da shi. Sai dai shugabannin kamfanin sun ce ba za su iya ƙari kan adadin da suke samarwa ba saboda yawan haraji.
"Ba mu da damar da masu shigo da kayayyaki suke da ita," in ji Tosky Hans, wanda darakta ne a kamfanin Minjingu Mines and Fertilizer.
"Masu samar da taki a cikin gida suna biyan haraji mai yawa, su kuma masu shigar da shi ba su biya," kamar yadda ya ce.
Kamar sauran ƙasashen duniya, masu zuba jari na ƙasashen waje ana ba su rangwame ko tallafi domin jawo hankalinsu cikin ƙasar, sai dai masu samar da kayayyaki a cikin ƙasar kuma na biyan haraji.
Wata ƙungiya ta Alliance for Green Revolution in Africa, wadda ƙunigiya ce mai zaman kanta ce da ke taimaka wa manoma a fadin nahiyar ta ce wannan dama ce ga manoma su dogara da kansu.
Vianey Rweyendela, wanda manajan ƙungiyar ne a Tanzania, yana ba manoma ƙwarin gwiwa domin su haɗa ƙungiya. Ya ce wannan yunƙurin zai taimaka musu su samu murya ɗaya don daidaita farashi.
"Wannan zai taimaka musu su samu ƙarfin yin ciniki haka kuma a sayar musu taki a farashi mai rahusa," in ji Mista Rweyendela.
Wanda ya fi kowa kuɗi a Afrika Aliko Dangote, ba da daɗewa ba ya ƙaddamar da kamfanin takin zamani a Najeriya wanda ake sa ran zai samar da tan miliyan uku na takin zamani a duk shekara.
Yana da burin ganin cewa wannan kamfain nasa zai kawo sauyi.