Amsar tambaya biyar kan dalar shinkafar da Shugaba Buhari ya kaddamar

    • Marubuci, Umar Mikail & Fauziyya Tukur
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar domin nuna irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu wajen noman shinkafa.

An tattara dala-dalar shinkafar 13 wadda aka yi miliyoyin buhunan shinkafa a dandalin baje-koli na babban birnin kasar a Abuja.

Ga amsar wasu tambayoyi da ƴan Najeriya ke ta yi wa kawunansu dangane da batun dalar shinkafar.

Mece ce gaskiyar hoton dalar katako da ake yaɗawa?

Wani hoto da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta ya nuna dalar shinkafa ɗauke da jerin katakwaye a tsakiya da nufin ita ce dalar da Shugaba Buhari na Najeriya ya ƙaddamar ranar Talata a ABuja.

An yi ta yaɗa hoton musamman a Facebook da WhatsApp da zimmar dakushe bikin ƙaddamar da dalar shinkafar da gwamnati ta ce ita ce mafi girma a duniya da aka taɓa yi.

Gwamnatin Buhari ta ce an tattara buhunan shinkafa fiye da miliyan ɗaya da aka karɓa daga manoma a faɗin jihohin ƙasar da suka samu tallafi ta cikin tsarin Anchor Borrower Programme na Babban Bankin Najeriya CBN.

Sai dai binciken da Sashen Bankaɗo Labaran Ƙarya na BBC ya gudanar ya gano cewa hoton ya fara ɓulla ne a dandalin Nairaland tun watan Janairun 2018, inda aka yi amfani da shi a wurare da dama.

Binciken ya gano cewa an ɗauki hoton ne yayin irin wannan bikin na dalar shinkafa a Jihar Ogun.

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara yaɗa hoton ƙaryar ne don mayar da martani kan wani bidiyo na dalar shinkafar da Lauretta Anochie, wata wata mataimakiya ta musamman ga Shugaba Buhari ta fito tana yabonsa kan ci gaban da ya kawo a harkar noma.

"Lauretta Onochie idan kin gama yaɗa bidiyon farfagandar na dalar shinkafar, sai ki kai Buhari wajen da dalar take ya saya..." kamar yadda wani ya rubuta a jikin ɗaya daga hotunan da ake yaɗawar.

Sashen binciken ƙwaf na BBC ya ce dalar shinkafar da aka yi a Cibiyar Kasuwanci da Masana'antu ta Abuja ba a kan ginin katako aka ɗora su ba, kamar na Ogun, sannan an ɗora buhunhunan shinkafar kan wani abu da ruwa ba zai ratsa ba, ba kamar na hoton da aka yi ta yaɗawan ba.

Sannan buhunhunan da BBC ta gano yau a wajen ƙadddamarwar ba irin na jikin hoton ƙaryar da aka yi ta yaɗawa ba ne.

Sannan dalar shinkafa na hoton Ogun ɗin sun fi ƙaranta idan aka kwatanta da dalar Abuja da shugaban ƙasa ya ƙaddamar a yau.

Kazalika Ms Lauretta a shafinta na Facebook ta kuma wallafa wasu hotuna da bidiyo da ke nuna lokacin da ake tsara dalar shinkafar Abujan. Ba a ga katakwaye a jikin hotunan ba dalar ba.

Sai dai wani bincike da BBC ta ƙara yi ɗin ya gano cewa shinkafar da ke cikin buhunhunan shamfera ce wacce ba a cashe ba, amma dai ba duwatsu da tsakuwa ba kamar yadda wasu ke yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Ta yaya aka tara shinkafar?

An dai noma shinkafar ce a daminar bana a jihohi daban-daban na Najeriya.

Alhaji Aminu Gwaranyo wanda ya gudanar da jawabi a wurin taron, ya faɗa wa manema labarai cewa sun shafe tsawon wata huɗu ana noma ta sannan kuma sun ɗauki tsawon wata uku suna haɗa dalar.

Buhun shinkafa nawa ne?

Tun da farko masu gabatarwa a wurin taron sun ce akwai buhu miliyan ɗaya a kowace dala.

Sai dai Aminu Gwaranyo ya tabbatar da cewa akwai saɓani wajen adadin buhunan da aka tara.

"Kamar yadda ka ji, wasu na cewa buhu miliyan ɗaya ne, wasu na cewa miliyan uku, wasu ma na cewa miliyan 10 ne; duka dai babu wanda ya faɗi ƙasa da miliyan ɗaya," in ji shi.

Ya ƙara da cewa suna tattara takardun bayanai na abin da kowace mota ta ɗauko zuwa wurin.

Sai dai shinkafar shamfera ce wacce bayan an cashe ta ba lallai ta kai yawan buhunhunan da suka a yanzu ba.

Don haka a yanzu a iya cewa babu wanda zai bugi ƙirji ya faɗi ainihin yawan buhunhunan shinkafar, wataƙila sai dai a jira sanarwar hukumomi a nan gaba.

Me za a yi da shinkafar da aka tara?

Kamar yadda Aminu Gwaranyo ya bayyana, an tara dala-dalar shinkafar ce da zummar bayyana wa duniya nasarorin da Najeriya ta samu a fannin noma ƙarƙashin gwamnatin SHugaba Buhari.

Bayanai sun nuna cewa shinkafar ta biyan bashi ce da Babban Bankin Najeriya CBN ya karɓa daga hannun manoman da suka karɓi bashin.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce za a sayar wa kamfanoni shinkafar da aka tara domin su gyara da kuma kai ta kasuwa.

Ayyukan noma na kan gaba a cikin alƙawuran da Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya a 2015 lokacin da yake neman su zaɓe shi, kuma an jiyo shi a lokuta daban-daban yana shawartar 'yan ƙasa da su koma gona.

Me Shugaba Buhari ya ce a taron?

Shugaba Buhari da kansa ya je taron ba aike ba, kuma da yake ƙaddamar da dalar wanda aka ce ita ce tarin shinkafa mafi girma da aka taba yi a wuri ɗaya, ya daki ƙirji cewa yawan shinkafar da ƙasar ke samarwa a yanzu a shekara ya kusan ninka wadda take samarwa a daga tsakanin shekarar 1999 da lokacin da ya hau mulki a 2015.

"Kawo yanzu shirin Anchor Borrowers ya tallafa wa ƙananan manoma miliyan 4.8; wajen noma nau'ukan amfanin gona har iri 23 da suka haɗa da shinkafa, da masara da kwakwar manja, da koko, da auduga, da rogo da tumatur da kuma wajen kiwon dabbobi.

"A yau yawan shinkafar da Najeriya ke samarwa ya ƙaru zuwa ton bakwai da rabi a shekara. Kafin ƙaddamar da shi abin da Najeriya ke samarwa a shekara tsakanin 1999 da 2015 bai kai ton huɗu ba a shekara.

Bugu da ƙari kafin ƙaddamar da shirin ana da kamfanonin sarrafa shinkafa 15 ne kawai a duk Najeriya, amma zancen nan da ake muna da cikakkun kamfanonin shinkafa fiye da 50 a ƙasar nan da ke samar da ayyukan yi tare da rage zaman kashe-wando."

Shugaban ya ce wannan nasarar sakamako ne na juye-juyen halin da gwamnatinsa ta ƙaddamar ta fuskar noma domin tabbatar da cewa ƴan Najeriya na iya noma abin da za su ci kuma su ci abin suka noma.

Shugaban dai ya ƙaddamar da dalar ne tara da rakiyar wasu gwamnonin jihohin ƙasar biyar da suka yi fice wajen noman shinkafa, wato na Cross Rivers da Ebonyi da Ekiti da Kebbi da kuma Jigawa.

Abubakar Atiku Bagudu shi ne gwamnan jihar Kebbi inda shugaban ya ƙaddamar da shirin noman shinkafar a 2015 wanda kuma ta zama ta ɗaya a samar da shinkafa a kasar.