Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Jesus, Bellingham, Ward-Prowse, Eriksen, Gvardiol, Belotti, Danjuma
Dan wasan Manchester City da Brazil, Gabrie Jesus, mai shekara 25, ya amince da kwantiragin kaka biyar da Arsenal a kan £45m. (Guardian)
Liverpool tana da tabbacin za ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund da tawagar Ingila, Jude Bellingham mai shekara 18. (Sun)
West Ham na son daukar dan wasan Southampton da tawagar Ingila, James Ward-Prowse, mai shekara 27, a kakar nan . (Sky Sports)
Dan wasan tawagar Denmark, Christian Eriksen na daf da yanke hukuncin ko zai koma Tottenham sai dai kuma Brentford na fatan tsawaita yarjejeniyar dan kwallon mai shekara 30. (Fabrizio Romano)
Villarreal da West Ham sun tattauna kan batun sayen dan wasan tawagar Netherlands, Arnaut Danjuma, mai shekara 25. (Toni Juanmarti - in Spanish)
Kociyan Manchester United Erik ten Hag zai iya samun fam miliyan 100 daga mahukuntan kungiyar domin sayo sabbin 'yan wasa. (Sun)
Tottenham na binciken farashin dan kwallon RB Leipzig dan kasar Croatia, mai tsaron baya, Josko Gvardiol, 20. (Nabil Djellit)
Atletico Madrid na bibiyar farashin dan wasan Celtic's dan kasar Croatia, mai tsaron baya, Josip Juranovic, 26. (Record)
Monaco na tuntubar dan kwallon Torino da tawagar Italiya, Andrea Belotti, mai shekara 28, AC Milan na son sayen dan kwallon. (Ekrem Konur)
Wakilin Sadio Mane ya musanta batun cewar dan kwallon Senegal mai shekara, 30, ya bar Liverpool zuwa Bayern Munich a kakar nan saboda baya karbar albashi mai tsoka a Anfield. (TVMondo, via Mirror)
Leeds za ta dauki dan wasan RB Leipzig dan Amurka, Tyler Adams, mai shekara 23, da na RB Salzburg dan kasar Mali, Mohamed Camara, mai shekara 22, domin maye gurbin dan kwallon Ingila, Kalvin Phillips, mai shekara 26, wanda ke daf da komawa Manchester City. (Mail)
Angel di Maria, wanda kwantiraginsa zai kare a Paris St-Germain a karshen watan Yuni, na dab da komawa Juventus, duk da cewar Barcelona na son daukar dan kwallo Argentina mai sheiara 34. (Calciomercato - in Italian)
Dan wasan Manchester United da tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya barar da damar komawa kungiyar David Beckham Inter Miami zai ci gaba da taka leda a Old Trafford. (Star)