Ike Ekweremadu: Yadda aka kama Sanatan Najeriya bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum

An gurfanar da wani dan majalisar dattawan Najeriya a gaban kotu bisa zargin kai wani yaro kasar Birtaniya da zummar cire sannan jikinsa.

Ike Ekweremadu, mai shekara 60, da matarsa Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekara 55, sun gurfana a gaban kotun Majistiret ta yankin Uxbridge a Yammacin London ranar Alhamis.

An mika wa gidan kula da kananan yara yaron, mai shekara 15, da ake zargi an kai London domin cire sassan jikinsa. Rundunar 'yan sandan birnin London ta ce hukumomi suna yin bakin kokarinsu domin kulas da shi.

Kotun ta saurari karar da ke cewa Mr Ekweremadu, wanda dan siyasa ne kuma lauya, ya taba zama mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya.

'Neman izinin Antoni Janar'

An gaya wa kotun cewa mutanen da ake zargi suna zaune a Najeriya sai dai suna da iyali a London. Ana zarginsu da hada baki wajen shigar da yaron cikin Birtaniya da zummar cire sashen jikinsa.

Ma'aikacin kotun ya nemi sanin adireshin mutanen biyu inda suka ce suna zaune a: "Najeriya".

Kotun ta ji cewa za a iya ba za a iya ci gaba da tuhumarsu ba sai an nemi izinin Antoni Janar saboda batun da ya shafi humurin kotun.

Mai shigar da kara Damla Ayas ya shaida wa kotun cewa: "Game da wadannan zarge-zarge da ake yi wa wadannan mutane, ana bukatar izinin Antoni Janar kuma kotun tana bukatar kwana 14 wajen samun wannan izini."

Kotun ta majistiret ta ji cewa an aikata kusan daukacin laifukan da ake zargin Sanata Ekkeremadu da matasa da da su ne a Birtaniya. A halin yanzu dai an tsare Sanatan da mai dakinsa har lokacin da za su sake gurfana a gaban kotu ranar 7 ga watan Yuli.

Tawagar bincike ta musamman

Mr Ekweremadu, wanda a kwanakin baya aka nada shi a matsayin farfesa na wucin-gadi wato visiting professor a Jami'ar Lincoln, sau uku yana rike mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, dag 2007 zuwa 2019.

Dan jam'iyyar hamayya ta People's Democratic Party (PDP) ne, kuma tun shekarar 2003 yake majalisar dattawa a matsayin Sanata.

Tawaga ta musamman ta 'yan sandan birnin London ta gudanar da bincike a kansa ne bayan wani ya tsegunta mata cewa wani mutum yana shirin cire sannan jikin wani yaro.

Ana cire sassan jikin mutum ne domin sayarwa ba tare da izininsa ba.

Wani mai magana da yawun Jami'ar Lincoln ya ce: "Galibin farfesoshin wucin-gadi ba sa zaune a jami'o'in da suke aiki kuma ba a ba su albashi, sannan mukami ne na bayar da shawara kawai.

"Mun yi matukar damuwa game da yanayin zarge-zargen da ake yi masa amma wannan batu ne da ya shafi bincike na 'yan sanda, don haka ba za mu yi tsokaci a kai ba a wannan mataki."