'Yan sandan Kano sun kama mai saka sunan mata a Facebook 'don yaudarar mutane'

Asalin hoton, Kano Police/Kiyawa
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta damƙe wani matashi a Kano wanda ake zargi da amfani da shafukan bogi a kafafen sada zumunta domin yaudarar jama'a.
Mai magana da yawun ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce sun samu nasarar kama matashin mai suna Musa Lurwanu mai shekara 26 ne bayan tattara bayanan sirri da kuma bin diddiƙin lamarin.
Ya bayyana cewa tun da farko sun samu ƙorafe-ƙorafe ne tun a watan Afrilun bana kan yadda wani ya yi ƙaurin suna a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da sunayen maza da mata da hotunansu domin buɗe shafuka a Facebook da Twitter da Whatsapp da dai sauransu domin yaudarar mutane.
A cewar ƴan sandan, har sun samu ƙorafi daga wata Zahra Mansur mai shekara 20 wadda ta ce abokanta da ƴan uwa na ta kiranta sakamakon wani na amfani da sunanta da hotonta da bidiyoyi wurin buɗe shafukan Facebook da kuma yaudarar jama'a.
Bayan haka ne kwamishinan yan sandan jihar CP Sama'ila Dikko ya bayar da umarnin kamo duk wanda ke aika hakan wanda a ƙarshe aka kamo Lurwanu Maje da ke ƙauyen Sittti a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano.
Yan sandan sun bayyana cewa sun samu wanda ake zargin da waya samfarin Redmi Note 11 Pro wadda ƙudinta kimanin dubu 200 da kuma wasu abubuwa da matashin ya saya ta wannan hanya.
Haka kuma an same shi da kuɗi naira dubu saba'in haka kuma an same shi da hotunan tsiraicin wasu daga cikin waɗanda ya yaudara a tare da shi.
SP Kiyawa ya bayyana cewa bayan an gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya buɗe wani shafin bogi mai suna Zahra Mansur inda ya rinƙa amfani da hotunanta domin yaudarar mutane, haka kuma ya amsa da cewa ya yaudari mutane da dama inda ya samu hotunan tsiraicinsu da bidiyo inda ya yi musu barazana da su kan cewa su tura masa kuɗi.
Wannan lamari dai yana daga cikin matsalolin da ake fama da su a kafafen sada zumunta a Najeriya inda jama'a da dama ke kokawa kan lamari.











