Masana'antar guragu da ke koya wa masu kafa kere-kere a Kano

Bayanan bidiyo, Masana'antar guragu da ke koya wa masu kafa kere-kere a Kano

Danna hoton dake sama domin kallon bidiyon:

Wasu masu bukata ta musamman a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na neman 'yan uwansu masu larura da kuma sauran matasa domin koya musu kere-kere da zummar dogaro da kai.

Wannan na zuwa ne a yayin da mutane da dama a Najeriya ke ci gaba da lalubo mafita kan tsadar rayuwa.

Wannan lamari ne da ya sha bambam da wanda aka saba gani na barace-barace daga masu lalura a kan titunan birnin kano.

Masana'antar da Alhaji Aminu Ahmad Tudun Wada ke jagoranta ta shafe shekara kusan 40 tana aiki.

Yace an samar da ita ne sakamakon kira da masu bukata ta musamman suka yi na samar musu motoci da babura da kuma kekuna wadanda za su rika hawa.

Akwai mutum sama da 30 da ke koyon aiki a masa'antar ta kere-kere.

Alhaji Aminu ya ce akwai masu bukata ta musamman sama da 500 da suka kammala karatu a matakai daban-daban amma ba su samu aiki ba.

Ya kara da cewa irin wadannan dalilan ne ya sa suka kafa masana'antar domin koyawa 'yan uwansu masu lalura sana'o'i da kuma matasa marasa larura aiki domin dogaro da kai.

Shugaban masa'antar na ganin dole ne a kai yara masu bukata ta musamman makaranta kamar yadda ake kai yara marasa larura.

An yaye matasa da dama daga jihohin arewacin Najeriya a masana'antar da ta shafe kusan shekara 40 kuma suna dogaro da kansu a yanzu.

A cewar mallam Aminu ganin yadda sana'ar kere-kere ke rufa musu asiri ne ya sa suke ta yunkurin janyo masu bukata ta musamman dake barace-barace a kan titunan Kano su koya musu sana'ar.