Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Jesus, Raphinha,a Lukaku, Lewandowski, Spence, De Jong

Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya fara shirin barin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. (La Repubblica)

Arsenal na duba yiwuwar rattaba hannu kan dauko dan wasan Manchester City, asalin Brazil kuma na gaba Gabriel Jesus, mai shekara 25. Gunners na fatan fam miliyan 30 za ta sayo dan wasan, to amma ita City fam miliyan 50 take nema kafin ta saki dan wasan. (Sky Sports)

Watakil Gunners ta sake rattaba hannu domin dauko dan wasan tsakiya na Leicester asalin Belgium, Youri Tielemans, mai shekara 25, duk da ce wa su na shirin kammala yarjejeniyar dauko wani dan wasan tsakiya na Porto, Fabio Vieira, mai shekara 22, da shi ma dan asalin Portugal ne. (Evening Standard)

Arsenal na son dauko dan wasan Leeds asalin Brazilia Raphinha, mai shekara 25, da dan wasan Ajax mai tsaron baya na Argentina Lisandro Martinez, mai shekara 24. (Athletic, subscription needed)

Kociyan Chelsea Thomas Tuchel, na son maye gurbin mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 29 - wanda Inter Milan ke farauta, haka ma mai kai hari na Bayern Munich mai shekara 33 dan Poland Robert Lewandowski, sai dai akwai wata sarkakiya da ke tattare da hakan. (ESPN)

Barcelona na son dauko Lewandowski, tare da cewa dole nan gaba ya bar Bayern, sai dai ba ya son bata alakarsa da kulob din na Jamus ta hanyar tilasta komawa wani. (Express)

Nottingham Forest za su karkare shirin siyo mai tsaron baya na faransa Moussa Niakhate, dan shekara 26. (Football Transfers)

Southampton na duba yiwuwar dauko mai tsaron baya na Bayern Munichkuma dan Amirka Chris Richards, mai shekara 22. (GiveMeSport)