Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Kamomar Jesus, Bellingham, Pope, Cucurella da Bazunu

Arsenal na gab da kammala sayen dan wasan gaba na Brazil da ke wasa a Manchester City, Gabriel Jesus, mai shekara 25. (Times - subscription required)

Newscastle United na bibiyar mai tsaron gida na England da kuma kungiyar Burnley Nick Pope, mai shekara 30. (Times - subscription required)

Har yanzu Liverpool na nuna sha'awarsu na sayen dan wasan tsakiya na Engila da Borussia Dortmund Jude Bellingham. (Mirror)

AC Milan su ne kan gaba a rige-rigen da take yi da Newcastle wajen sayen mai tsaron baya na Lille Sven Botman. (Football Insider)

Manchester City na shirin taya dan wasan Brighton Marc Cucurella mai shekara 23 da haihuwa. (Guardian)

Kungiyar kwallon kafa ta Leeds United da kuma Southampton dukkaninsu suna son dan wasan Manchester United mai shekara 18 Romeo Lavia. (Athletic - subscription required)

Southampton na gab da sanar da daukan mai tsaron gida na kasar Ireland Gavin Bazunu daga Manchester City a kan kudin da ya kai fan miliyan 15. (Telegraph - subscription required)

Kungiyoyin kwallon kafa na Fulham da Wolves dukkaninsu na nuna sha'awar sayen dan wasan Sporting Lisbon Joao Palhinla mai shekara 26 da haihuwa. (90min)

Mai tsaron baya na Ingila James Tarkowski ya amince ya tafi kungiyar kwallon kafa ta Everton da zarar yarjejeniyarsa da kungiyar Burnley ta kare a wannan shekara. (Sky Sports)