Premier League: Man City za ta ziyarci West Ham, Liverpool da Fulham

Mai rike da kofin Premier League, Manchester City za ta ziyarci West Ham United a wasan farko a kakar 2022-23.

A jadawalin da aka fitar ranar Alhamis za a yi hutu domin buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar tsakanin watan Nuwamba zuwa Disambar 2022.

Saboda haka ba za a buga wasannin Premier League ba a karshen makon ranar 12 zuwa 13 ga watan Nuwamba zuwa 26 ga watan Disamba, saboda gasar kofin duniya.

Za a fara wasan farko a kakar nan ranar Juma'a 5 ga watan Agusta, inda Crystal Palace za ta karbi bakuncin Arsenal.

Liverpool za ta fara wasa da sabuwar kungiyar da ta koma buga Premier League, Fulham, yayin da Nottingham za ta ziyarci Newcastle.

Forest ta koma buga Premier League a karon farko tun bayan 1998-99 rabonta da babbar gasar tamaula ta Ingila.

Za a fara gasar cin kofin duniya a Qatar ranar 21 ga watan Nuwamba har da tawagar Ingila da ta Wales da za su fafata a wasannin.

Za kuma a buga wasan karshe a kofin duniya ranar 18 ga watan Disamba, kwana takwas kafin a ci gaba da wasannin Premier League na kakar da za a fara.

Babu wani babban wasa tsakanin manyan kungiyoyi shida na Ingila a makon ranar 12 zuwa 13 ga watan Nuwamba, hakan zai bai wa fitattun 'yan wasa damar halartar gasar kofin duniya da wuri.

Wasan Premier League makon farko:

Ranar Juma'a 5 ga watan Agusta

  • Crystal Palace da Arsenal

Asabar 6 ga watan Agusta

  • Bournemouth da Aston Villa
  • Everton da Chelsea
  • Fulham da Liverpool
  • Leeds United da Wolverhampton
  • Leicester City da Brentford
  • Newcastle United da Nottingham Forest
  • Tottenham da Southampton

Ranar Lahadi 7 ga watan Agusta

  • Manchester United da Brighton
  • West Ham United da Manchester City