Kalaman saɓo a Indiya: 'Masifar da muka shiga bayan rushe gidajenmu mu Musulmai'

Afreen Fatima's house

Asalin hoton, Vivek Singh

Bayanan hoto, Hukumomi sun rusa gidan Javed Mohammad bayan sun kama shi bisa zargin zanga-zangar da aka gudanar kan addini kwanakin baya
    • Marubuci, Daga Zoya Mateen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi

Mene ne gida?

Gidan su Somaiya Fatima, mai shekara 19, launin ɗorawa ne a garin Prayagraj (wato Allahabad a da), wani birni a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya, inda take zaune ita da iyayenta da ƴan uwanta.

Ta ce akwai abubuwan tunawa da dama a gidan mai hawa biyu kamar su wajen cin abincinsu da wajen yin nishaɗinsu ita da ƙannenta musamman a baranda.

Fatima ta ce gidan nasu, waje ne da ya zama mafaka a gare ta, kuma ya zama muhalli na kwana da rayuwa ga ita da iyayenta.

Amma a ranar Lahadin da ta gabata, aka rusa musu jin daɗinsu, bayan da hukumomi suka rushe gidan "ba tare da sanar da su ba", suka bar su da tashin ƙura da ɓaraguzai.

Hukumomin sun ce ba a bi ƙa'ida ba ne wajen gina gidan, zargin da Fatima da iyayenta suka musanta.

Rushe gidajen ya jawo ɓacin rai musamman daga masu suka kan gwamnatin ƙasar ta jam'iyyar BJP mabiya addinin Hinsu, waɗanda suka ce shi ne lamari na baya-bayan nan da aka yi da nufin kai wa Musulmai hari a Indiya.

Tun lokacin da BJP ta karɓi mulki a 2014 a Indiya - take kuma mulkar jihar Uttar Pradesh tun 2017 - ake samun ƙaruwar hare-hare a kan Musulmai da takura musu.

Fatima ta ce ko damar kwashe kayansu ba a bai wa iyayenta damar yi ba. Ta ce tana kallon wani hoton zane da ta taɓa yi wa ƙaninta da take so sosai, amma ba ta iya ɗaukarsa ba.

"A yanzu gidanmu ya zama tarihi, babu abin da muka tsira da shi," ta faɗa cikin kuka.

Afreen Fatima's house in Prayagraj

Asalin hoton, Somaiya Fatima

Bayanan hoto, Ga gidan nasu kafin a rushe shi

An rushe gidansu Fatima ne bayan kama mahaifinta, wanda ɗan siyasa ne a yankin mai suna Javed Mohammad - wanda ƴan sandan Uttar Pradesh ke zargin sa da shirya zanga-zangar da Musulmai suka jagoranta a baya-bayan nan da ta rikiɗe zuwa rikici.

Masu zaga-zangar sun buƙaci a kama Nupur Sharma, wata tsohuwar mai magana da yawun jam'iyyar BJP, wacce ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad a watan da ya gabata. An dakatar da ita daga jam'iyyar.

Mr Mohammad na daga cikin fiye da mutum 300 a Uttar Pradesh kan zanga-zangar.

Ɗaya daga cikin ƴaƴansa Afreen Fatima - fitacciyar Musulma mai gwagwarmaya ce da ta sha shiga bore kan adawa da dokar zama ƴan ƙasa mai cike da ce-ce-ku-ce da kuma ta hana ɗalibai mata Musulmai sanya hijabi a makarantu.

Rubbles of Afreen Fatima's house in Prayagraj

Asalin hoton, Vivek Singh

Bayanan hoto, Fatima ta ce ta ji takaciin rashin ɗaukar komai a gidan musamman wani zane da ta yi tun tana ƙarama

Ƴan jam'iyyar hamayya sun yi tur da rushe gidajen Musulman, suka kuma zargi gwamnatin Uttar Pradesh - wacce wani ɗan addinin Hindu Yogi Adityanath ke jagoranta - kan ƙin bin matakan da suka dace wajen warware matsalar.

Sauran gidajen da ake rushe na wasu Musulmai ne da ake zargi da yin jifa bayan kammala Sallar Juma'a - su ma an rushe su a ƙarshen mako.

Wannan ɗaya ne daga cikin jerin rushe gidajen Musulmai da aka yi a Uttar Pradesh da wasu jihohin da BJP ke mulki sakamakon rikicin addini.

Hukumomi sun ce sun yi rusau ɗin ne saboda ba a kan doka aka gina gidajen ba, amma ƙwararru kan shari'a sun musanta hakan.

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda aka rushe gidajen Musulmai bayan zanga-zangar adawa da ɓatanci ga Annabi
Presentational white space

Ƴan sanda sun zargi Mr Mohammed baban Fatima da hannu a kitsa rikicin. Wani babban ɗan sanda ya shaida wa ƴan jarida cewa ƴar Mr Mohammed Afreen Fatima ma na da hannu cikin shirya irin waɗannan zanga-zanga, kuma ita da babanta tare suke shirya farfagandar. AMma ita ba a kama ta ba.

Somaiya Fatima da ɗan uwanta Mohammad Umam sun yi watsi da zarge-zargen, suna cewa babansu da yayarsu ba su da hannu a lamarin.

Afreen Fatima

Asalin hoton, Somaiya Fatima

Bayanan hoto, Afreen Fatima fitacciyar ƴar gwagwarmaya ce

Fatima cikin raha ta ce babanta Mr Mohammad yana da wasu ɗabi'u masu ban sha'awa, kamar yawan amfani da Facebook da gina makwararar ruwa a wurare daban-daban a cikin gidan, sannan yana ɗaukar lokaci sosai wajen tsara yadda zai bai wa ƴaƴansa kyaututtuka.

Ta ce karamcin mahaifinta bai tsaya kan iyalansa ba kawai. "Abba yana taimakon kowa. Kuma yana da kyakkyawar alaƙa da kowa kama daga kan hukumomi har zuwa kan maƙwabta da baƙi," ta faɗa tana mai karawa da cewa tana matuƙar alfahari da kasancewa ƴarsa.

Ƴaƴan gidan na yawan gaya wa babansu da yayarsu cikin raha cewa "su kan fuskanci matsala" saboda "baram-ɓaramarsu."

"Wasu lokutan ƴan uwana maza kan gargaɗi yayarmu Afreen cewa ta rage kaifin bakinta," in ji Fatima. "Amma ba wanda ya taɓa zaton za mu samu kanmu a irin wannan yanayin."

Javed Mohammad

Asalin hoton, Somaiya Fatima

Bayanan hoto, An zargi Mr Mohammad da tayar da zaune tsaye, amma ƴaƴansa sun musanta

Iyalan Mr Mohammad sun tuhumi hukumomi kan dalilin da ya sa aka rushe musu gida.

Hukumar Kula da Ci gaba Birnin ta Prayagraj ta ce a ranar 10 ga watan Mayu ta aika saƙon cewa za ta rushe gidan saboda an gina shi ba bisa ƙa'ida ba, inda ta nemi ya je gabanta ranar 24 ga watan Mayu.

Amma ɗansa Umam ya ƙaryata hakan, yana mai cewa iyalan ba su samu wata takarda ba har sai da daddare ana ya gobe za a rushe gidan.

"Kuma ma gidan da sunan mahaifiyata aka saye shi - kyauta ce babanta ya ba ta. Duk kuɗaɗen ruwa da wuta da haraji a kan aiko ne da sunanta. Amma sai aka aiko da sanarwar da sunan babana," in ji shi.

BBC ta tuntuɓi wasu jami'ai biyu daga hukumar Prayagraj, waɗada suka ƙi cewa komai.

Afreen Fatima's home

Asalin hoton, Vivek Singh

Bayanan hoto, Rushe gidan Mr Mohammad ya sanya tsoro a zuƙatan maƙwabtansa

Govind Mathur, wani tsohon alkalin alkalan babbar kotun Allahabad, ya shaida wa BBC cewa abin da hukumomin suka yi "rashin adalci ne."

"Ko da a ce ma an yi kuskure a bin ƙa'idojin gina gidan, kamata ya yi hukumomi su sa a biya tara ƙarƙashin dokokin ƙaramar hukuma," a cewarsa.

"Aƙalla ma dai ai sai su bai wa iyalan damar yin bayani."

Mr Ali ya ce ana yin rusau ɗin ne kawai don tsokanar Musulmai.

A bulldozer is being used to demolish the illegal structures of the residence of Javed Ahmed, a local leader who was allegedly involved in the recent violent protests against Bharatiya Janata Party (BJP) former spokeswoman Nupur Sharma's

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu suka sun ce hujjar rusa gidan ba ta isa ba

Rushe gidan ya sanya matuƙar tsoro a zuƙatan maƙwabtan Mr Mohammad.

Kareli, wajen da gidan yake, unguwar mai hada-hada sosai. Kuma mafi yawan mazaunata Musulmai ne, sai tsirarun mabiya Hindu da su ma ke zaune a can.

Yawanci unguwar kan cika da hayaniyar jama'a musamman masu talla da sauran hada-hada.

Amma tun bayan da aka rusa gidajen, sai ko ina ya kasance shiru saboda tsoro da fargaba.

Mazauna unguwar da dama sun ƙi yin magana, sun ce suna tsoron su ma a yi musu hakan idan suka fadi abin da ke ransu.

Da dama kuma suna ma tsoron fitowa daga gida, sai dai ajiyo muryoyinsu ƙasa-ƙasa idan har sun ga gilamawar baƙi.

Wani maƙwabinci Mr Mohammad ya fadi yadda ya dinga yi wa gidan nasa kwaskwarima kwanan nan. Wani ɗan unguwar kuma ya ce shi yana son sanin me ya sa sai gidajen Musulmai ake rusawa.

Ga iyalan Mr Mohammad dai, sun shiga cikin damuwar rushe gidansu da rashin adalcin da suka ce an yi musu.

Ƙarin bayanai daga Vivek Singh a Prayagraj