Neman mafaka a Rwanda: Tsohon dan sandan Iran da ke jin tsoro kasarsa za ta kashe shi

    • Marubuci, Daga Parham Ghobadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian

Wani tsohon dan sandan Iran, da za a kai Rwanda daga Birtaniya karkashin sabuwar dokar nan mai cike da ce-ce-ku-ce, ya ce yana tsoron masu leken asirin kasarsa za su iya kashe shi.

A baya-bayan nan mutumin ya ba da bahasi a gaban wata kungiyar kare hakkin dan adam da ke Birtaniya, da ke bincike kan zargin cin zarafin farar-hula da hukumomin Iran suka yi lokacin zanga-zanga a shekarar 2019.

Ana dai tsare da shi a sansanin da ke kusa da filin jirgin sama na Gatwick, bayan ya shiga Birtaniya daga Turkiyya a watan Mayu.

A ranar Talata ake sa ran za a tasa keyar rukunin farko da suka nemi mafaka zuwa Rwanda.

A can Rwandan za a ci gaba da shirin ba su mafakar, a nan kuma za a taimaka musu da matsuguni. Idan aka yi nasara, za su ci gaba da za a Rwanda har na tsawon shekaru biyar, da samun damar karatu da tallafi.

Sai dai wannan sabon shiri na fuskantar suka ta bangarori daban-daban musamman 'yan siyasa da kungiyoyin agaji, wadanda suka nuna damuwa kan kaurin-sunan da wasu kasashen Afirka suka yi kan take hakkin dan adam.

Kotun soji ta yanke wa tsohon kwamandan, wanda ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na tsaro, daurin shekara biyar a Iran. An kuma rage masa mukami saboda kin harbe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati kan tsadar rayuwa da tashin farashin man fetur.

A wancan lokacin, tsohon kwamandan shi ke bai wa 'yan sanda 60 da ke karkashin ikonsa umarni.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta tattara bayanan maza 304 da mata da kananan yaran da aka zargi jami'an tsaro sun kashe cikin kwanaki biyar, yawanci sanadin harbin bindaga.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce an kashe akalla mutum 1,500 cikin kasa da mako biyu.

A lokacin da aka ba da belin shi bayan daukaka kara, tsohon kwamandan ya tsere zuwa kasar Turkiyya, inda a watan Nuwamba 2021, ya ba da bahasi ta kafar intanet gaban kotun da kungiyoyin kare hakkin dan adam uku suka kafa a birnin Landan.

Ya ce ya shafe watanni 14 ya na boye a Turkiyya, kafin ya samu isa Birtaniya. Duk da cewa ya rufe fuskarsa a lokacin da ya ke ba da shaida, ya ce jami'an tsaron Iran sun gane shi da kuma sanin inda 'yan uwansa suke.

"Iyalina suna Iran cikin ukuba, sannan wannan tasa keyar tawa da za a yi, na nufin duk halin da suka shiga ba shi da wani amfani," in ji shi a lokacin da BBC ta tattauna da shi daga cibiyar da ake tsare da shi wato Brook House.

"Sun takurawa 'iyalina, su na gallaza musu saboda na ji tsoro na koma gida ta haka ne kadai za su iya kama ni," in ji shi.

A ranar 14 ga watan Mayu, ya isa Birtaniya ta kwale-kwale, kuma nan da nan aka tsare shi a cibiyar tsare bakin-haure.

Kwafen takardar wa'adin mayar da shi da sashen BBC Persia ya gani, an ba da ne tun ranar 31 ga watan Mayu, inda aka shaida ma sa za a tasa keyarsa zuwa birnin Kigali na Rwanda ranar 14 ga watan Yuni.

Takardar ta ce ''damar da ya ke da ita na daukaka karaza ta samu ne idan baya cikin Birtaniya".

Tsohon kwamandan ya ce ya na tsoron kar rayuwarsa ta salwanta, idan aka tasa keyarsa zuwa Rwanda, a cewarsa sojin juyin-juya halin Iran su na gudanar da ayyuka a nahiyar Afirka.

Daya daga cikin wadanda suka samar da kotun Aban Tribunal, Shadi Sadr, ta ce tabbas rayuwar mutum tana cikin hatsari saboda sojin juyin-juya halin Iran sun yi kaurin suna wajen sace mutane da garkuwa da su, da kitsa kisa, sannan yawanci su na aiki a kasashen Afirka da dama.

A makon da ya wuce aka fara bai wa tsohon kwamandan, maganin zazzabin cizon sauri, a wani bangare na shirin tasa keysarsa zuwa Rwanda, amma ya ki yadda ya sha.

"Babu inda zan je, sai dai idan gawata za ku kai Rwanda," wannan shi ne abin da ya shaida wa jami'an tsaron.

"Don me za a kai ni Rwanda? Ai gara an kai ni Iran," in ji shi. "Ko ba komai, na san abin da zan tarar a can. Ba zan iya rayuwa cikin tsoro da rashin sanin abin da ka je ya zo ba da kuma tsoro."

Ms Sadr ta ce mutumin na fara da matsananciyar damuwa, kuma ofishin cikin gida na Birtaniya ya tabbatar da yana fama da ciwon zuciya.

Sakatariyar cikin gida a Birtaniya, Priti Patel, ta kare sabon shirin, tare da cewa na hadin gwiwa ne da gwamnatin Rwanda, kuma wani bangare ne na daukar matakai da garanbawul kan dokokin neman mafaka da bata gari ke takewa, da mai da abin tamkar kasuwanci.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida, ya shaida wa sashen BBC Persia cewa ''Za a bai wa wadanda aka tasa keyarsu zuwa Rwanda damar sake gina rayuwarsu".