APC ta fada sabon rudani kan batun dan takarar shugaban kasa na maslaha

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fada cikin sabon rudani bayan shugabanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa sun amince da shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Bayanai sun nuna cewa Sanata Adamu ya bayyana haka ne a wurin taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta APC a Abuja ranar Litinin din nan.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Adamu ya shaida wa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta APC matsayarsu ne bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Ya sanar da wannan mataki ne kwana guda kafin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Amma wasu 'yan kwamitin gudanarwar sun ce ba da yawunsa shugaban APC ya dauki matakin ba.

Kazalika jim kadan bayan hakan, gwamnonin Jihohin arewacin Najeriya karkashin jam'iyya sun yi watsi da matsayar shugaban jam'iyyar tasu.

Daya daga cikin gwamnonin ya shaida wa BBC cewa suna nan a kan bakansu na mika mulki ga kudancin kasar a zaben 2023.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar Aso Villa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce Shugaba Buhari ya tabbatar musu cewa bai goyi bayan wani mutum ba cikin mutum 23 da ke son jam'iyyar ta tsayar da su takara.

Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce sun dauki matakin goyon bayan dan takara daga kudancin kasar ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasar.

"Mun yi duba game da daukacin al'amuran kasarmu kuma mun yi amannar cewa jam'iyyar APC da Shugaban kasa sun raba romon dimokuradiyya ga dukkan bangarorin kasar nan... Abin da muke bukata shi ne a bai wa wasu bangarorin kasar dama. Kuma hakan zai kawo zaman lafiya," in ji shi.

Shugaban APC ya sanar da wannan mataki ne kwana biyu bayan gwamnoni 11 na arewacin Najeriya karkashin jam'iyyar sun amince mulki ya koma kudancin kasar bayan mulkin Shugaba Buhari.

Wannan matakin nan nufin sauran masu neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar ta APC ba su samu tubarrakin jam'iyyar tasu ba.

'Ba za a tursasa dan takara ba'

Dambarwar da ake yi kan batun dan takarar shugaban kasar na Najeriya a jam'iyyar APC ta sa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa yana nesanta kansa ga goya wa kowanne dan takara baya.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya aike wa manema labarai ya ambato Shugaba Buhari yana cewa babu wanda ya zaba a matsayin dan takarar APC na shugaban kasa a zaben 2023.

"Shugaba Muhammadu Buhari, ranar Litinin da rana, ya warware zare da abawa game da matsayarsa kan zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, inda ya bayyana a gaban gwamnoni 14 na jihohin arewacin Najeriya na jam'iyyar cewa ba shi da dan takarar da ya zaba," da kuma shafaffe da mai kuma a shirye yake ya tabbatar ba a yi dauki-dora a jam'iyyar ba," in ji sanarwar.