Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da Buhari ya gaya wa manyan APC gabanin zaben fitar da gwani
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da manyan jiga-jigan jam'iyyar APC, gabannin taronsu na ƙasa domin zaɓen wanda zai tsaya takarar gaje kujerarsa a zaɓen 2023.
Ganawar da aka yi a fadar gwamnati a Abuja, ta samu halarta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da kuma tsofaffin shugabanni jam'iyyar na riƙo da gwamnonin jam'iyyar.
Ana dai gani ganawar a matsayin wani ƙoƙari na cimma daidaituwa kan mutumin da za a mara wa baya a zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar ke somawa ran Litinin 6 ga watan Yuni ta kuma ƙarƙare a jibi Laraba, 8 ga watan Yuni.
Baya ga ganawar jiya Lahadi, an yi ta samun tuntubar juna, kuma sama da mako guda kenan ana zama tsakanin gwamnoni da masu takara domin samar da maslaha gabanni zaɓen fitar da gwamnin.
Me Buhari ya ce a taron?
A wata sanarwar da kakakin shugaban ya fitar, Femi Adesina, na cewa Shugaba Buhari ya yaba da kokarin tuntuɓar juna da aka rinƙa samu tsakanin masu neman kujerarsa ta shugaban Najeriya da kuma yiwuwar cimma matsaya kan mara wa mutum guda baya.
A cewar sanarwar, shugaban ya ce yana da ƙwarin-gwiwar suna kan gaba wajen sake lashe zaɓe a karo na uku jere, ƙarƙashin inuwar jam'iyyarsu ta APC.
Sannan yana son ganin taron ya samar da shugabanci mai ƙarfi da alƙibla a wannan gaɓar da ake ciki, na tunkarar babban zaɓe a 2023.
Ya ce: "Ina da ƙwarin-gwiwar cewa sakamakon wannan tuntuɓa da kwamitin bayar da shawarwari na jam'iyya zai taimaka wajen sake ba mu alƙbila, da taimaka mana wajen cimma manufofinmu na dimokraɗiyya, al'adu da tsare-tsarenmu da dama ake bi a jam'iyyarmu.
"Kuma ana cikin wannan yanayi, na tattauna da gwamnonin jam'iyyarmu, da kuma sauran manyan mambobin jam'iyyarmu da ke neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyarmu a zaɓen 2023.
"Ina farin cikin sanar da ku cewa na samu sakamako mai kyau a ganawar da na rinƙa yi wanda ke nuna irin shirin da jam'iyyarmu ta yi domin sake ɗanne mulki a karo na uku jere tun 2015, a zaɓen shugaban kasa."
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma nuna muhimmancin haɗa-kai da mara wa juna baya a ƙoƙarin sake gina jam'iyyarsa zuwa ga nasararsu a idon duniya baki daya, yana mai cewa kar jam'iyyarsu ta zama ta daban.
Da suwa aka tattauna?
Mutanen da suka halarci zaman jiya da Shugaba Buhari sun haɗa da tsohon shugaban riƙo na farko na jam'iyyar, Cif Bisi Akande da John Odigie-Oyegun.
Akwai kuma shugaban jam'iyyar ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakataren Jam'iyyar, Sanata Iyiola Omisore da wasu gwamnoni.
A cikin gwamnonin akwai na Borno, Babagana Zulum da Simon Lalong na Filato da Bello Matawalle na Zamfara akwai kuma gwamnan Ebonyi, David Umahi.
Ana kuma sa ran a yau Litinin ma Buhari zai sake ganawa da gwamnonin Jam'iyyar APC 22.
Rahotanni na cewa duk da cewa yau Litinin ake soma taron, ba za a soma gudanar da zaɓen ba sai a yammacin Talata daga 6 zuwa 9 na yamma.
Daligete sama da 2,300 da ake sa ran shigar su Abuja domin zaben wanda zai riƙe tikitin kara a APC.