Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sojojin kasar Rasha da suka ki shiga yakin Ukraine
- Marubuci, Daga Olesya Gerasimenko da Kateryna Khinkulova
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Wasu daga cikin sojojin Rasha na ƙin komawa fagen daga domin yin yaƙi a Ukraine saboda abubuwan da suka fuskanta a baya a fagen yaki a lokacin kutsen farko da Rasha ta yi wa Ukraine, kamar yadda wani lauya mai kare haƙƙin bil adama na Rasha ya bayyana. BBC ta jima tana tattaunawa da irin waɗannan sojojin waɗanda suka ƙi amincewa su koma fagen daga.
"Ba na so na koma Ukraine domin na kashe ko a kashe ni," in ji Sergey - ba shi ba ne ainahin sunansa ba - wanda ya shafe makonni biyar yana yaƙi a Ukraine a farkon shekarar nan.
Yanzu ya koma gida Rasha, bayan ya samu shawarwari daga lauyoyi domin ya guje wa mayar da shi fagen daga. Sergey na ɗaya daga cikin ɗaruruwan sojoji da aka gano cewa sun ɗauki irin wannan shawara.
Sergey ya ce ya shiga matsananciyar damuwa sakamakon abubuwan da ya fuskanta a Ukraine.
"Ni na ɗauka mu ne sojojin Rasha, waɗanda suka yi fice a duniya," in ji matashin a lokacin da yake bayani a cikin fushi. A maimakon haka, sai ake ganin za su iya yaƙi ba tare da wasu muhimman kayan aiki ba, kamar irin su gilashin gani da dare, in ji shi.
"Mun koma kamar ƴaƴan magen da ba su gani. Mun tsorata da rundunar mu. Ba wasu kuɗi sosai za a kashe ba domin wadata mu da makamai. Me ya sa ba a yi haka ba?"
Sergey ya shiga aikin soja ne bayan an tursasa masa - akasarin matasa na ƙasar Rasha waɗanda ke tsakanin shekaru 18-27 dole ne su yi aikin soja na tilas na shekara guda. Amma bayan watanni ƙalilan da ya soma, sai ya saka hannu kan kwantiragi da zai ba shi dama ya ci gaba da aikin har na tsawon shekara biyu inda kuma zai samu albashi.
A watan Janairu, an tura Sergey kusa da iyakar Rasha da Ukraine inda aka faɗa masa cewa wani atisaye ne za su yi. Bayan wata guda - a ranar 24 ga watan Fabrairu, a ranar da Rasha ta ƙaddamar da yaƙi kan Ukraine - sai aka faɗa masa cewa ya tsallaka iyakar ƙasarsa. Kusan nan take sai aka soma kai wa rundunarsa hari.
A daidai lokacin da suka yada zango da dare a wata gona da ba a nomawa, sai kwamandan su ya ce: "A yanzu irin aikin da kuka yi zuwa yanzu, wannan ba wasa bane."
Sergey ya girigiza matuƙa.
"Abin da na fara tunani shi ne " Dagaske wannan na faruwa da ni?"
An ta kai musu hare-hare da bindiga," in ji shi a lokacin da suke tafiya da kuma lokacin da suka yada zango. A cikin rundunar su mai ɗauke da sojoji 50, an kashe mutum goma an kuma raunata 10. Kusan duka sojojin da ke tare da shi ba su wuce shekara 25 ba.
Ya ji labarin wasu daga cikin sojojin Rasha waɗanda ba su san makamar aiki ba waɗanda ba su san ma yadda za su harba bindiga ba kuma ba su san kan yadda roka take ba, ba su san gaba da bayanta ba".
Ya ce ayarin motocin da suke ciki da ke tafiya tun daga arewacin Ukraine - ya rabu bayan kwana huɗu a yayin da wata gada da za su tsallake bam ya tashi da ita, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar abokan yaƙinsu.
A wata mai kama da haka, Sergey ya bayyana cewa dole ne ya wuce wasu daga cikin abokansa da ke ƙonewa a cikin wata mota da suka maƙale a cikinta.
"Gurneti ne ya tayar da motar. Sai ta kama da wuta kuma akwai sojojin Rasha a ciki. Mun ta tafiya a kusa da ita a lokacin da ake buɗe mana wuta. Ban kalli ko baya ba."
Sai rundunarsa ta ci gaba da tafiya ta gefen iyakar ƙasar, amma a bayyane take akwai ƙarancin dabara a tattare da su, in ji shi. Sojojin da za su taimaka musu sun ƙi isowa kuma ba su da kayan aikin da za su tunkari aikin da ke gabansu na ƙwace babban birni.
"Sai muka ci gaba da aiki ba tare da helikwafta ba - muna tafiya a jere tamkar muna zuwa wurin fareti."
"Sai muka yi sauri muka tafi ba tare da zama da dare ba kuma ba tare da mun je zagaye ba. Ba mu bar kowa a baya ba, idan wani ya yi ƙoƙarin bi ta bayanmu ya kai mana hari babu wanda zai kare mu.
"Ina tunanin kusan duka mutanen mu sun mutu ne saboda da wannan. Da a ce mun tafi a hankali yadda ya kamata, kuma da mun duba kan hanya ko da an dasa nakiyoyi, da an kaurace wa mace-mace."
Kokawar da Sergey ya yi kan batun ƙarancin kayayyakin aiki ta fito ne a yayin wata tattaunawa ta waya wanda ake zargin an yi ta ne tsakanin sojan Rasha da iyalansa, wanda rundunar tsaron Rasha ta yi kutse a cikin kiran wayar kuma ta wallafa tattaunawar da suka yi.
A farkon watan Afrilu, an tura Sergey zuwa kan iyakar ƙasar kuma zuwa wani sansanin Rasha. An janye sojoji daga arewacin Ukraine inda ake ganin suna haɗa kansu domin su ƙaddamar da hare-hare a gabashin ƙasar. Daga baya a cikin watan, sai aka ba shi wani umarni na ya koma Ukraine - inda ya shaida wa kwamandansa cewa bai shirya zuwa ba.
"Sai ya ce haƙƙina ne. Ba su yi ma ƙoƙarin su shawo kaina ba, saboda ba mu bane na farko," kamar yadda Sergey ya shaida wa BBC.
Wani lauya ya shaida wa Sergey tare da wasu mutum biyu da su mayar da makamansu su kuma koma hedikwatar su - inda za su rubuta takarda da za su yi bayani kan cewa sun gaji da wannan aiki kuma ba za su iya ci gaba da yaƙi a Ukraine ba.
An shaida wa Sergey cewa ya koma rundunarsa kuma hakan na da muhimmanci sakamakon idan ya tafi, hakan tamkar ya gudu ne daga filin daga wanda hakan zai iya ja a ɗaure shi tsawon shekara biyu.
Kwamandojin sojoji na yawan ƙoƙarin buɗe ido ga sojoji masu aikin kwantiragi domin su tsaya a rundunonin su, kamar yadda wani lauyan kare haƙƙin bil adama a Rasha Alexei Tabalov ya bayyana.
Sai dai ya bayyana cewa ƙa'idojin aikin soja a Rasha ba su amince da batun mutum ya ƙi yarda ko kuma ya ce ba zai je yaƙi ba idan ba ya so yaje.
Mai kare haƙƙin bil adama Sergei Krivenko ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan wata doka da ke aiki kan waɗanda suka ƙi yarda su koma fagen daga.
Ba hakan na nufin ba a taɓa ƙoƙarin kama wani da laifi ba.